Tsakure
Wannan takarda mai taken “Hadakar manufa tsakanin ‘yan fim din Hausa na Arewacin Nijeriya da ‘Yan fim din Inglishi na Kudancin Nijeriya” wani yunkuri ne na yin nazarin samuwar hadakar manufa a tsakanin ‘yan fim. A duniyar fina-finai, hadakar manufa ba bakon al’amari ba ne, Akwai irin wannan Hadaka ta manufa ga ‘yan fim na Amurka da Indiya da Sin, da sauran manyan bangarorin ‘yan fim na duniya. Wannan ne ya sanya aka dukufa don nazarin fina-finan da ake samun wannan hadakar manufa tsakanin ‘yan fin din Hausa na arewacin Nijeriya da ‘yan fim din Inglishi na kudancin Nijeriya. An yi amfani da dabarar tattara bayanai ta hanyar duba littatafi da kallon wasu fina-finan da binciko wasu bayanai a wasu shafuka na giza-gizan sadarwa. Bayan haka, takardar ta lura da cewa, a cikin fina- finan, arewaci da kudancin Nijeriya akwai fina-finai da yawa da aka samu hadakar manufa a cikinsu. Haka kuma, yawancin fina-finan da aka samu wannan Hadaka ta manufa, fina-finai ne na barkwanci, kuma galibin jaruman da suka fito a cikin fina- finan, sun yi fice ne ga fina-finan barkwanci.
1.0 Gabatarwa
Hadakar manufa na nufin haduwar wasu bangarori biyu ko fiye da haka domin su zamo abu daya a kan wata ka’ida ko yarjejeniya don cimma wani buri. Wadannan mutane ya alla ‘yan jam’iyun siyasa ne ko kulob-kulob ne na kwallo ko ‘yan kungiyiyoyi ne ko ‘yan fim ne (Oxford Living Dictionaries, 2018).
Shi kuma wasan kwaikwayo abu ne mai tsohon tarihi a duniya gaba daya, kuma mawuyacin abu ne a duniya wani mutum ko wasu mutane su iya fadin hakikanin rana ko lokacin da ake fara wasan kwaikwayo a duniya, sai dai an san cewa shi dadadden bangare ne na adabi. (‘Yar- Aduwa, 2012:4).
Yayin da fim ya kasance wata hikima ce ta hoto mai motsi da ake dauke da mutane, wato hotunansu maza ko mata, yara ko manya, ko kuma ma wani mutum, wanda aka dauko ta hanyar yin amfani da na’urar daukar hoto ta musamman, yana baiwa mutane (kowanensu) damar tafiyar da wasu ayyuka ta fuskar kwaikwayo ko waninsa, a wani dan lokaci da aka kebe wanda shi wasan kwaikwayon yake dauke da wani sako na musamman kan nishadi da gargadi da wa’azi da soyayya da tarihi, ko wanin haka zuwa ga al’ummar duniya (‘Yar-Aduwa, 2012:30).
Haka kuma, bayan ma’anar fim akwai ire-iren a fina-finai da suka hada da:
- Fim din siyasa
- Fim din soyayya
- Fim din tarihi
- Fim din barkwanci/nishadi
- Fim din addini
- Fim din sarauta
- Fim din tsafi/tsibbu/sihiri
- Fim din batsa
- Fim din jarumta/yaki
- Fim din fadace-fadace
- Fim din damfara
- Fim din hadin kai
- Fim din shashanci
- Fim din bokanci
- Fim din al’ajabi
- Fim din ban tausayi
- Fim din zamantakewar iyali
- Fim din al’amurran yau da kullum (Literary Genres, 2019)
Galibi irin wadannan nau’ukan fina-finai akwai su a fina-finan Hausa.Sannan akwai wani sabon nau’in fim da ke cikin fina-finan Hausa a yanzu shi ne Indiya Hausa.Fim din Indiya ne amma da fassarar Hausa. Sannan a arewacin Nijieriya akwai ‘yan fim da yawa kuma shahararru da suka hada da: Rabilu Musa (Ibro) da Yusuf Haruna Funtuwa (Baban Chinedu) da Ali Nuhu da Adam A. Zango da Hafsat Muhammad Sharada (Mai Aya) da Nafisa Abdullahi da Aisha Aliyu Tsamiya da Rabi’u Rikadawa da Hauwa Maina da Baballe Hayatu da Rahama Sadau da Maryam Booth da Sani Musa (Danja) da sauransu.
A kudancin Nijeriya ma akwai ‘yan fim irin su: Emeka Ike da Uzee Usman Adeyemi Chinedu Ikedieze da Osita Iheme da Paul Sambo Liz Benson da Stephanie Okereke da Edward Tom da John Okafor (Mr. Ibu) Nkem Owoh (Osoufia) da Rita Dominic da Oge Okoye da Tonto Dikeh daUche Jombo da Mercy Johnson da Genebibe Nnaji da sauransu. Kuma da yawa daga cikin wadannan na kudanci da na arewaci suna haduwa su aiwatar da fim a tare, wanda wannan ita ce “hadakar manufa”.
Hadakar manufa tsakanin ‘yan fim na arewacin Nijeriya da ‘yan fim din Ingilishi na kudancin Nijeriya tana taimaka wa ‘yan fim su sami damar isar da sakonsu kuma ya kayatar cikin kankanin lokaci a duk fadin arewaci da kudancin Nijeriya.
Saboda haka, wannan takarda za ta yi tsokaci kan samuwar hadakar manufa a tsakanin ‘yan fim din Hausa na arewacin Nijeriya da ‘yan fim din Ingilishi na kudancin Nijeriya da kuma yin dan takaitaccen sharhi ga wasu fina-finan arewacin da kudancin.
2.0 Ma’anar fim
Fim wani sashe ne daga fasahar kafar sadarwa ta lantarki wadda take samar da gani da ji da motsi, domin amfanin mutane masu yawa, sannan sako ne da kowane mutum ke iya fahimtarsa.
Fim wata hikima ce ta hoto mai motsi da take dauke da mutane, wato hotanansu maza ko mata, yara ko manya, ko kuma ma wanin mutane, wanda aka dauka ta hanyar yin amfani da na’urar daukar hoto ta musamman, tare da bai wa mutane (kowanensu) damar tafiyar da wasu ayyuka ta fuskar kwaikwaiyo ko waninsa, a wani dan lokaci da aka kebe wanda shi wasan kwaikwaiyo yake dauke da wani sako na musamman kan nishadi da gargadi da wa’azi da soyayya da tarihi,ko wanin haka zuwa ga al’ummar duniya.‘Yar-aduwa, (2012:30).
Shi kuwa Yakasai (2004:332) ya bayyana fim a matsayin tantagaryar kimiyya da fasaha ce, kuma rayuwar dan’Adam ce ake nunawa. Fim yana dauke da tarihi da dabi’un jama’a da muhallinsu da abincinsu da kuma suturarsu, musamman bisa harshensu da tsarinsu na rayuwar da hanyoyin tunaninsu da kuma falsafar rayuwar mutanen da ake yin fim din don su. Har ila yau,
Fim hanya ce ta sanarwa da ilimantarwa da jan hankali da nishadantarwa da fadakarwa da yada manufa da tallatawa.
Fim shi ne wasan kwaikwayo na zamani, wanda yake dauke da hoton rayuwar al’umma a kan dukkan al’amurran yau da kullum tare da isar da sako ta sigar hikima kuma a aikace.
A dunkule fim kafa ce daga cikin kafafen yada labarai, sannan kuma hanya ce ta kasuwanci da samar da aikin yi ga al’umma.
3.0 Samuwar fim a duniya
Akwai hasashe mai karfi da ke nuna cewa tarihin samuwar fim a duniya ya faro ne a cikin karni na goma sha tara (19) a shekarar 1824, inda wani likita dan kasar Birtaniya, mai bincike a bangaren ido, wato Peter Mark Rogel, wanda ya fara wani bincike domin samar da wata na’ura mai kamar idon mutum. Daga nan aka ci gaba da bincike-bincike da ya taimaka wajen kirkiro wasu abubuwa da suka shafi na’ura, misali kamar kallo-kallo na yara, wato Zoetrope.
A tsakanin shekarar 1844 zuwa 1918ne wani Bature dan kasar Faransa mai suna Charles Emile Renoad ya samar da wata na’ura mai suna Prodiono Scope. A shekara ta 1861 wani Ba’amurke, wato Coleman Scllers, shi ma ya samar da wata na’ura mai suna Cinema-toscope.Sai kuma a 1872 aka samu wani aikin hadin guiwa a tsakanin wasu Turawan Amurka da Ingilaida suka dauki hotunan dawaki guda 24 suka samar da hoton tafiyar dawaki da motsinsu.
A shekarar 1830, Etiene Jues Marey, mutumin Faransa ya samar da Chronophotgrphe, wato kyamara mai motsi wadda ake iya daukar hoto da ita a takarda. Su George Eastman da Hannibal Williston Goddwin ma a tsakanin 1822-1900 sunsamar da zaren kallo na majigi. (Yakasai 2004:333).
Bayan Thomas Alra Edison ya samar da na’urorin Kenetographe da Kinatoscope, wadanda ya kaddamar da su a bainar jama’a a Amurka (New York), sai kuma ya yi amfani da su ya bude shagunan kallo a Faris da London inda aka ringa kallo a ciki.An samu wani gagarumin aikin hadaka da a karkashin shi ne aka samu na’urar Projector wanda Robert W.Palt da Jean Louas Lumiere da Charles Francis Jenkis suka yi. (Yakasai, 2004:335).
Ana tunanin fim na farko a duniya da aka fara nuna wa mutane an samar da shi ne a tsakanin shekarar 1895-1910 wanda an nuna tsawon fim din bai muce minti daya ba kacal. Sai A shekarar 1912 aka fara yin fim din barkwanci. Sarauniyar Ingila Kueen Elizabeth na cikin wadanda suka shiga harkar fim a lokacin da ta shahara tana cikin yin fim din ne aka bata sarauta. A shekarar 1913 aka yi cikakken fim mai suna “Judith of Behulia”. A 1915 kuma aka yi fim na farko na yaki mai suna “The Birth of Nation”, Daga nan aka yi ta samun ci gaban na’urori da sauran kayayyakin da za su taimaka ga samuwa da ingantuwar fim a duniya. Daga nan bunkasa da yaduwar kasuwar fim ta ci gaba da mamayar duniya (Yakasai, 2004:335).
3.1 Samuwar fim a Nijeriya
Zaren tarihi ya nuna cewa a shekarar 1903 aka fara yin kallo a Legas, a Nijeriya. Fim na farko da aka fara kawowa a Nijeriya aka kalle shi a gidan kallo na Galoria Memorial Hall da ke Legas, shi ne Moral Re-Almament. An nuna shi ne a shekarar 1903, kuma fim ne na tarihi da ya koyar da mutane a yi biyayya ga Nasara a guji Yahudawa.Shi ya sanya aka sanya masa suna Farfado da da’a.
An ci gaba da samun fina-finai jefi-jefi duk da cewa fina-finan shigowa ake da su tun daga 1945 har zuwa samun ‘yancin kai a 1960.Fina-finai ba su samu gatanci sosai ba, duk da ana yin fina-finan a Nijeriya. Sai dai maudu’in da gwamnati ta fi so akan shi ake gudanar da fina- finan a tsakanin shekarar 1980-1981 fim ya bunkasa ya kuma samu gatanci sosai a Nijeriya. Sannan ana kyautata zaton cewa daga tsakanin shekarar 1960-1980 an yi fina-finai da adadinsu ya kai dari da talatin (130) a Nijeriya, a cikin harsuna guda hudu kamar haka:
– 104 da Yarbanci
– 9 da Ingilishi
– 3 da Igbo (Ibonci)
– 2 da Hausa
Haka kuma, akwai tabbacin daga shekarar 1960-1980 akwai gidajen sinima 350 a Nijeriya da ake nuna fina-finai. (Gidan Dabino, 2004:337).
3.2 Samuwar fim din Hausa
Samuwar fina-finan Hausa, abu ne da ya faru a karshen karni na ashirin (20). Amma farkon abin da ya dora tubalin samuwarsa shi ne wasan kwaikwayo. Kuma shi kansa wasan kwaikwaiyo, ya samu ne bayan Turawan mulkin mallaka sun kafu, kuma har sun yi nisa wajen shinfida tsare – tsare da suka shafi ilimi da tsarin mulki da sauransu.Wasan kwaikwaiyo na farko a cikin Adabin zamani na Hausawa an same shi neda ga labaran da Ahmadu Kano, ya ba waniBajamushe mai suna Rudolf Prietze, wato Turbar Kudus 1898, sai kuma a shekarar 1900 a ka samu littafin wasan kwaikwayo na ‘Yan Matan Gaya. A shekarar 1902 an samu littafin wasan kwaikwayo naTurbar Tarabulus. Duk Wadannan littattafan wasanin kwaikwayo da Rudolf Prietze ya rubuta, ya samar da su ne daga labaran Ahmadu Kano ne ya ba shi Malumfashi (2013:166). R.M East ya kirkiri wasan kwaikwayo a rubuce mai suna SidHausa Plays wandakuma hukumar fassara ta farko ta wallafa shi a 1930. A cikin adabin baka na gargaijya akwai wasanin gargajiya masu tarin yawa da suke kunshe da kwikwaiyo na halayyar rayuwar Hausawa da ake gabatar da su lokaci zuwa lokaci don nishadi da ilimantarwa da sauransu. Amma daga baya Hausawa sun bayar da gudummuwar a wannan fanni na adabi (Yar’aduwa, 2013:30).
3.3 Matakan samuwar fina-finan Hausa
Akwai wasu hanyoyi da aka bi da wasu matakai da aka taka kafin a kai ga samar da fina-finan Hausa, Daga cikinsu akwai:
a) Samuwar na’urorin daukar hoto na zamani da Hausawa suke amfani da su a yanzu wajen shiryawa da kuma gabatar da fina-finan Hausa a yau, wato na’urar daukar hoto ta bidiyo da kaset da injin bidiyo da kuma talabijin da faifan (CD) ko disk da memori da sauran kayan sadarwa da yada bayanai na zamani.
b) Kafuwar Kamfanoninkasuwanci masu zaman kansu, na Arewacin Nijeriya, kamar ‘NTC’, wato kamfanin taba.Shi ma ya shirya majigi na Hausa kuma Hausawa ne suka yi, a wajen jan hankali manoman taba da kuma mashayanta. Da fim irin “Musa”da aka shirya kan tallar taba mai- dagi da mai-zobe da taba Target da kamfanin sukari mai iyali (Tale Family Sugar) da suke nuna hotunan majigi suna talla.
c) Kokarin kamfanoni da hukumomi na wallafa litattafai na farko, wato NNPC da NORLA da Hukumar Gaskiya da sauransu, wadanda ayyaukansu shi ne samar da littatafai na ayyanannun labarai da na wasan kwaikwaiyo da niyyar taimakawa ga sashen ilimi. Kuma taimakon ya yi rawar gani wajen zakulo labarai daga adabin Gargajiya da na Larabci da Inglishi, wanda kuma duk sun taimaka wajen samar da fina-finan Hausa. Misali, littafin Shaihu Umar, littafi ne wanda Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa ya samar da shi, kuma yana cikin littattafai na farko na zube wanda asalinsa ayyanannen labari ne wanda aka yi mashi sauye-sauye har kashi biyu (2). Nafarko daga zube zuwa wasan kwaikwaiyo. Nabiyu daga wasan kwaikwaiyo zuwa fim wandaAdamu Halilu ya shirya. Haka ma littafin Kulba na Barna na Umar Danjuma Katsina an baddala shi daga wasan kwakwaiyo zuwa fim wanda Brendon Shehu ya shirya. Littafin Magana Jari CeI-III na Alhaji Abubakar Imam an yi shirin fim din ta (Yar’aduwa, 2007:32).
d) Tasirin fina-finan kasashen waje tun daga na kasar Indiya da na kasar Sin da na kasar Amurka da sauransu. Wannan shi ma ya samar da mafarin wanzuwar fina-finan Hausa. Irin wadannan fina-finan sun samu shekaru fiye da hamsin ana kallonsu a manyan garuruwa na Hausawa, amma tabbas Hausawa sun fi son fina-finan Indiyawa akan na sauran kasashe. Wannan soyayya tana cikin abin da ya haifar da samar da nasu fina- finan.Wasu fina-finan ma sun juyo su ne daga fina-finan Indiya. Akwai fina-finai da dama na Indiya da aka juya zuwa na Hausa,wadanda ake kira da “Hausa-Indiya”. Misali:
HAUSA INDIYA
Izaya – Darcar
Tsumagiya – Suicide Mission
Jalli – Friend of the Family
So – Mohabbatein
Hawayen Zuci – Dhadkhan
Hakuri – Be Wafa Se Wafa
Mujadala – Dillagi
Dijengala – Hum Bade Mein
Jigal – Main Pyre Kiya
Sabani – Dil Kya Kyare
Gagarabadau – Bombay to Goa
Samodara 2 – Bombay to Goa (Sabo, 2004:458-459)
Ko a baya-bayan nan akwai fina-finan Indiya da aka juya su zuwa Hausa.Misali:
HAUSA INDIYA
Auwalu Sani Salisu – Amar Akbar Anthony
Hanzari – Dil Mainken Mata Nahi
Adon Gari – Gajini
Gwaska – Kick
Hanyar Kano – Bombay to Goa
Wadannan da sauran wasu fina-finan masu juyar da su zuwa fina-finan Hausa.
Juyar da littatafai zuwa fina-finai, musamman littattafan Adabin Kasuwar Kano. Ga misalin wasu daga cikinsu:
Ki yarda da ni – Bilkisu Salisu Funtuwa
Sa’adatu Sa’ar Mata – Bilkisu Salisu Funtuwa
Maimunatu – Ibrahim Y. Birniwa
In Da So Da Kauna – Ado Ahmad Gidan Dabino
Naira Da Kobo – Nazir Adam Salih
Kara da kiyashi – Zuwaira Isah Danlami
Alhaki Kuikuyo – Balaraba Ramat Yakubu
Sirrinsu – Maje El-Hajeej Hotoro
Rikicin Duniya – Dan Azumi Baba Chediyar ‘Yan Gurasa
Sakaina – Dan Azumi Baba Chediyar ‘Yan Gurasa
Idaniyar Ruwa – Abdul’aziz Sani Madakin Gini (Adamu, 2004:93)
Hakika wadannan matakai sun taka rawa gaya wajen samuwa da bunkasar fina-finan Hausa, duba da irin misalan da aka kawo na juyar da wasu fina-finan kasashen waje, musamman na kasar Indiya zuwa na Hausa da kuma juyar da wasu littattafan kagaggun labarai na Hausa zuwa fim na Hausa.
3.3.1 Kafuwar kungiyar ‘yan fim din Hausa (Kannywood)
Tarihin kafuwar Kungiyar ‘yan fim na Hausa ya samo asali a shekarar 1990 a lokacin da cikakkun fina-finan Hausa suka fara shiga kasuwa kuma suka samu karbuwa, daga cikin fina- finan da suka samu wannan tagomashi akwai Turmin Danya da Gimbiya Fatima da In da so da Kauna da Munkar da Badakala da Ki Yarda da ni. Kannywood shi ne sunan da ake kiran kungiyar da shi.Ana karfafa samar da sunan ne daga Sunusi Shehu na Mujallar Tauraruwa.Ya samar da sunan ne ta hanyar hada kalmomi guda biyu. “Kanny” da ke nufin Kano, sai kuma “Wood”wadda an cirato ta ne daga sunan babbar cibiyar shirya fina-finai ta Amurka wato “Hoollywood”. Wannan suna ya karbu, kuma an kaddamar da shi a matsayin sunan Kungiyar Masu Shirya Fim din Hausa ta Arewacin Nijeriya wato “Kannywood” a shekarar 1999.
3.3.2 Kafuwar kungiyar ‘yan fim din Ingilishi na Kudancin Nijeriya
A shekara ta 2000 aka fara samun alamun sunan kungiyar ‘yan fim din Ingilishi ta kudancin Nijeriya, amma sakamakon kai-ruwa-rana da aka yi da wasu, sai ba a cimma matsaya ba, kamar yadda Jonathan Haynes ya wallafa a cikin The New York Times. Saboda haka, sai a shekara ta 2002 Nori Mitsu Onishi ya kaddamar da sunan wato, “Noollywood” Ita ma abubuwa biyu su ne tubalin ginin sunanta, wato “Noolly” na nufin ‘yan fim din Ingilishi na Nijeriya, sai kuma “Wood” da aka alakanta da babbbar cibiyar fim ta Amurka. An nuna cewa ban da shirya fim, wannan kungiya tana da ruwa da tsaki akan kowane abu da ya shafi duniyar fina-finai a Nijeriya tun daga fim din Ingilishi da na Ibonci da Hausa da Yarbanci da Iteskiri da Edo da Efik da Ijaw da Urhobo da kowane irin harshe daga cikin harsunan Nijeriya (Wikipedia, 2018).
4.0 Me ce ce hadakar manufa?
Hadakar manufa na nufin haduwar wasu bangarori biyu ko fiye da haka domin su zama abu daya akan wata ka’ida ko yarjejeniya don cimma wani buri. Wadannan mutane ya alla ‘yan jam’iyun siyasa ne ko kulob-kulob ne na kwallo ko ‘yan kungiyoyo ne ko ‘yan fim ne. (Oxford Living Dictionary, 2018).
Hadakar manufa wata dabara ce ta hadin guiwa a tsakanin al’umma, domin tunkarar wani
abu ko wani al’amari a bisa matsaya guda, da zummar samun nasara ga abun ko al’amarin.
Hadakar manufa wata kimiyya ce ta cudar-ni-in-cude-ka,domin yinkurin tabbatar da kudiri da cimma manufa daya.
4.1 Samuwar hadakar manufa a tsakanin ‘yan fim na Hausa na Arewacin Nijeriya da ‘yan fim din Ingilishi na Kudancin Nijeriya.
An fara samun birbishi ko alamun samun hadakar manufa a shekara ta 2007 a cikin wani fim mai suna, “Sitanda” wanda Ali Nuhu ya fito, amma shi kadai ne daga arewacin Nijeriya. Amma a iya cewa cikakkiyar hadakar manufa ta fara faruwa ne a shekara ta 2013 bayan wata tattaunawa da wasu ‘yan kudancin da arewacin suka yi a Abuja.Domin kuwa, a 29 ga Afriluna shekara ta 2013 an samu hadakar manufa a fim din ‘Oga Abuja’ sai 20 ga watan yuli, 2013 a fim din “Dry”.Sai a 6 ga watan Nuwamba 2013 an samu fim din “Confusion Na War”. Haka al’amarin ya ci gaba da gangarowa har zuwa yau.
4.2 Tsokaci akan wasu fina-finai na hadakar manufa
Wannan bangaren za a yi tsokaci ne a kan wasu fina-finai da suke da hadakar manufa a cikinsu kamar yadda takardar ta lalubo su kamar haka:
4.2.1 Fim din “Karangiya”
Labarin wani mutum ne mai suna Alhaji Tanko, wato Rabilu Musa (Ibro),wanda ya kasance mai kudi kuma mai gadara da nuna isa.Yayin da yake auren Hajiya Babba wato Hadiza Muhammad wadda ta kasance mace mai hakuri da ladabi da biyayya ga miji.Wannan ya sanya bai taba sakinta ba duk da bai maida sakin mace a bakin komai ba. A gefe daya kuma ya auri diyar wani Ibo (Baban Chinedu) wanda mutum ne mai tsananin son kudi, wanda shi idan dai za ka bashi kudi duk abin da ka iya ka yi ma shi, amma duk da hakurin Chinyere wato Rahama Hassan sai da Alhaji Tanko ya saketa tun da dabi’ar shi ce auri-saki ko ace auren sha’awa. A karshe dai ta mai da mashi ‘ya’yansa tagwaye a gida bayan ta haihu. Talle (Chinedu Ikedieze) da Mudi(Osita Iheme), bai yi maraba da dawowarsu gidansa ba, ya ringa aibanta sunayensu ya canza masu sunaye daga Uche da Emeka ya maida masu Talle da Mudi.A karshe ya isar da mummunan sako garesu ta fuskar zagi, su kuma suka maido mashi da sakon da ya ba su na zagi.Sai ga shi yana kuka. A karshe suka hada kai da sauran ‘ya’yanshi suka zamar mashi babbar matsala a cikin gida. Sauran ‘yan wasan da ke akwai a cikin fim din “Karangiya” sun hada da: Tijjani Asase wato Sangami da Hadiza Aliyu Gabon a matsayin Raliya da Samira Ahmed a matsayin Salima da Jamila Kaduna a matsayin ‘yan mata da Nasiru Adabko a matsayin Direba sai Danjuma Salisu a matsayin mai gadi.
4.2.2 Fim din “Maja”
Fim din Maja fim ne da ya nuna rayuwar wasu ‘yan uwa wato Nkem Owoh (Osoufia) wato
Ndubisi a cikin fim din wanda ya kasance talakka mai sana’ar tura baro a cikin kasuwa.Ammakuma yana tsananin son kudi sai kuma dan ‘uwansa Sallau, wato Rabilu Musa (Ibro), wanda ya kasance marar ladabi da biyayya ga rashin sanin darajar mutane ga dukiyar gado da mahaifinsa sarkin noma ya mutu ya bar mashi. Dukkansu mahaifiyarsu daya ita ce Mama, wato Hafsat Muhammad Sharada (Mai Aya).Ndubisi shi ne babba domin shi ta fara haihuwa a Jihar Anambara.Daga baya ta rabu da mahaifinsa ta dawo arewa ta auri mahaifin Sallau wato sarkin noma. Ndubisi ya samu labarin mutuwar mijin mahaifiyarshi wurin kanan mahaifiyarshi, Malam Kalla wato Auwal Dare a wani zuwa da ya yi.Daganan Ndubisi ya kwaso kayan shi ya taho arewa dama “iska ya tadda kaba na rawa” saboda suna soyayya da A’isha Aliyu Tsamiya ‘yar gidan Baban Chinedu, har ya yi mata ciki, mahaifinta na nemansa “ruwa a jallo”. Daga nan ya gudu ya dawo wurin mahaifiyarsa. An samu rashin jituwa tsakanin Ndubisi da Sallau, saboda Sallau ya nuna baya son zaman Ndubisi a gidan da kyar dai ya amince amma sai dai Ndubisi ya zauna a dakin mahaifinsa, wato sarkin noma inda ya yi jinya ya rasu.Nan Ndubisi ya yi “gamon katar” da kudin da sarkin noma ya bari, “zakara ya ba shi sa’a”ya kwashe kudin ya dawo Abuja ya fara sabuwar rayuwa. Sallau bai hakura ba da ya tabbatar cewa Ndubisi ya dauke kudin, sai ya fito neman shi, ya yi sa’a sun hadu kuma ya yafe mashi suka hadu suka yi ta cin duniyarsu da tsinke. Kwatsam Bello Muhammad Bello ya bayyana ya yi tuggun da ya karbe kudin a hannun Ndubisi, a karshe Sallau da Ndubisi suka dawo gida. Sauran ‘yan wasan sun hada da: Uzee Usman Ademeyi da Sulaiman Yahaya (Bosho) a matsayin maigari da Rabi’u Daushe da Maryam Gidado diyar mai gari a matsayin matar Sallau da sauransu.
4.2.3 Fim din “Dry”
Fim ne da yake dauke da labarin wata karamar yarinya ‘yar shekara goma sha uku mai suna Halima, wato Zuwaira Ibrahim Fagge, wadda aka yi wa auren wuri da wani tsoho dan shekara sittin wanda bai damu da kula da iyali ba, mai suna Sani (Tijjani Faraga). Tun da Halima ta samu ciki take cikin mawuyacin hali sakamakon rashin kula.Bayan ta haihu ta sha wahala sosai, ba ta samu kulawa daga wurin mijinta ba. Haka daga gidansu wadanda suma talakawa ne na sosai, wanda halin talaucin da suke ciki ya sanya ko makaranta Halima ba ta yi ba. Kowasai ya watsar da ita, bayan ta haihu sannan ga ciwon yoyon fitsari ya kamata. Dakta Zara (Stephanie Okereke) likita ce mai tausayi, da son taimaka wa jama’a karewa da karau ta taba fama da lalura da ciwon yoyon fitsari a lokacin tana yarinya.Wannan shi ya kara sanya mata kaimi ta tsaya tsayin daka ta taimaka wa Halima har ta warke. Fim din ya nuna matsalar cutar yoyon fitsari, wanda galibi hakan na faruwa sakamakon yin auren wuri ga yara kanana. Sauran ‘yan wasan sun hada da: Darwin shaw a matsayin Dr. Aled da William Menamara a matsayin Dr. Brown sai Liz Benson a matsayin Matron sai Olu Jacobs a matsayin Speaker da Hauwa Maina a matsayin Hadiza da
Rahama Hassan da ta fito a matsayin Fatima, sai kuma Rakiya Attah a matsayin Uwar Sani da Kilnt D. Drunk a matsayin Muttaka sai Hakeem Hassan a matsayin Honourable Musa da Paul Sambo.
4.2.4 Fim din “Oga Abuja”
Oga Abuja fim ne na barkwanci da yake dauke da labarin rayuwar wasu ma’aikatan gidan soja Ali (Ali Nuhu), wanda kuma kowanensu yana da alaka da gidan, saboda kuwa mai gadin gidan wato Ibro kanin mahaifin mai gidan da yake gadi ne wato Ali. Yayin da John wanda aikin shi dafa abinci a gidan, shi ma kani ne ga mahaifiyar matar sojan Saira, wato Aina’u Ade. Ibro da John sun zama abokai kasantuwarsu cikin gida daya, suna aiki a tare duk da cewa ayyukansu daban-daban ne kuma kowa na bugun gaban cewa ya isa ya yi abin da yake so ya yi a gidan kasantuwar yana da dan uwa a gidan. Ibro mai dabi’ar wauta, da John mai dabi’ar rashin wayau sun hade sun zama cikakkun abokai da suka ringa yin komai a tare. Tun daga yin karya ga ‘yan mata da satar kudin mai gidansu domin su yi bushasha. Ali kuma ya kasance mai son ya taimaka wa dan uwansa da ma na matarsa wannan ya sanya ya hakuri da sokanci na John da wauta ta Ibro amma dai duk da haka har sai da halayensu suka gallabe shi. A karshe aka nemo ‘yar aiki, wato Daso, da ta kasance masifaffiya mai fada da cika-baki da son nuna iko da isa.Wannan ya sanya Ali da matarsa Saira suka fawwala lamarin kula da gidangaba daya a hannun Daso, wanda hatta Ibro da John a karkashinta suke.Itake da ikon ba su umurni dangane da kome za su yi a gidan. Kasantuwar Ibro da John ba su yi karatu ba Daso ta fahimci jahilci na cikin dalilan da suke sanya Ibro da John suke yin abin da suke yi. Ta bude masu makaranta a cikin gida ta fara masu karatu, amma kuma sai suka hada kai suka bijiro mata da soyayya. Wai kowannensu ya nuna yana sonta a matsayinta na malamarsu. Da ma dai dabi’arsu ce yi wa juna kage da sharri idan suna neman wani abu a tare. Saboda haka a wurin takarar da suke yi don nuna wa malamarsu soyayya, wato Daso, nan ma haka suka yi ta yi. Da yake “duk yadda ka yi da jaki sai ya ci kara”, sai da suka yi laifin da aka kore su daga gidan. Bayan sun bar gidan sun tafi neman aiki an daukesu John ya yi barna aka koresu, suka yi ta buge-buge don samun abinci.A karshe daisuka tafi gidan abokinsu Haruna.Wanna shi ya zamo silar komawarsu makaranta suka fara tun daga karamin aji har suka kammala Sakandire. Hasken karatu da suka samu ya sanya suka natsu suka bar duk shiriritun da suke yi.A karshe, sun dawo gidan Ali a matsayin natsattsun mutane kuma kamilai.Hakika gemu ba ya hana ilimi. Sauran ‘yan wasan sun hada da Maryam CTB da Yakubu Muhammad da Likita wato Auwal Dare da Baby, wato Fati Musa, da Alhaji wato Sani Ibrahim (Dan gwari) da Uzee Usman Adeyemi da Fadila Ibrahim da sauransu.
4.2.5 Fim din “Sons of the Caliphate”
Fim ne da yake dauke da labarin wasu hamshakan mutane guda uku da suke a Jihar Kowa Umar
Loko, wato Patrik Doyle babban dan siyasa ne mai cike da izza, wanda abin da duk yake so a siyasance shi yake yi. Gefe daya akwai wani kasaitaccen mai gadara da takama da arziki wanda ba a yi mashi gardama idan ya yi magana, shi ne Sani Bula, wato Edward Tom. Sai kuma Sarki da ya kasance mai kyawon hali da son kamantawa.
A gefe daya kuwa, wasu matasa da suka zama duwatsun murhu da suka kasance tsararrakin juna, kuma kowa yana ji da kansa saboda akwai abin daya taka. Dikko Loko, wato Yakubu Muhammad, da ne ga babban dan siyasar nan na garin Kowa yayin da Nuhu Bula, wato Mofe Duncan, ya kasance da ga hamshakin dan kasuwar nan. Sai kuma Khalifa mai yaki, wato Paul Sambo, da ya kasance da ga Sarkin Kowa kuma Yarima mai jiran gado. Bayan wadannan matasa masu kamar duwatsun murhu akwai wata matashiyar yarinya mai kissa da hila wacce ta kware wajen salon jan hankalin duk wani namiji, wato Rahama Sadau, da ta fito a matsayin Binta Kutigi, wacce ta zama silar faruwar wata sarkakkiyar soyayya a tsakanin abokai masu ji da kansu kuma makusantan juna, wato Dikko da Nuhu. Sauran ‘yan wasan sun hada da: Kulan Kallamu, wato Maryam Booth, da Jidda Attah, wato Jinjiri, da Rakiya Atttah a matsayin Hajiya Ummi da Mila Mohammed a matsayin Nafisa Loko da Adunni Adewale a matsayin Morina Bola sai kuma Mickey Odeh a matsayin Hamza da Mama Tey a matsayin Hajiya Safiya da Alhasan.Haka kuma Ibrahim a matsayin Agent Hogan da Ibrahim Nasir da ya fito matsayin Magaji da Magaji Mijin yawa da ya kasance a matsayin Waziri da Jasmine Wright a matsayin Ayiko da Auwalu Salisu da ya fito a matsayin Justice Kallamu, sai Tijjjani Faraga a matsayin Gobernor Kallamu sai Sophia Mohammed da Rabi’u Rikadawa. Fim din “Sons of the Chaliphate fim ne mai dogon zango (Season Film) wanda har yanzu ana cikin yinsa ba a gama ba, an fara yin shi a shekara ta 2016.
5.0 Kammalawa
Wannan takarda ta yi tsokaci ne a kan hadakar manufa da ke akwai tsakanin ‘yan fim din Ingilishi na kudancin Nijeriya da ‘yan fim din Hausa na arewacin Nijeriya. Wannan yana nuna ke nan masu shirya fina-finai suna haduwa don su gabatar da fina-finai da hadakar manufa. Hasali ma, akwai fina-finai da yawa da aka yi da wannan sigar kamar Hajiya Babba da Har da Mijina da Taurarin Zamani da Hasana da Hausaina da Doya da Manja da Tsintsiya da The light will come da Accidental Spy da Midnight sun da Wabes da Banana Island GhostdaAjuwaya da Ojokokoro da Boss of All Bosses da Confusion na war da last flight to Abuja da Blood and Henna da sauransu. Sannan wannan takarda ta gano cewa an samu cakuduwar al’adu tsakanin ‘yan arewacin Nijeriya da ‘yan kudancin Nijeriya, kuma ana amfani da wannan turba ta hadakar manufar fina-finai a samar da hadin kai da zaman lafiya a kasa.
Manazarta
Adamu U, (2004) Hausa Home Videos Technology, Economy & Society. Kano: Gidan Dabino Publishers
Dangambo, A. (2008) Rabe-raben Adabin Hausa Sabon Tsari. Kano: K.D.G. Publishers
English Oxford Living Dictionaries (2018) at htpp:/www.odforddictionaries.com
Hausa Language Cinema (2018) htpp//:en.wikipedia.org.
Kannywood News in Hausa (2018) at htpp:/www.bbc.com/hausa/topic.
Literacy Genres (2019) at htpp//:www.google.com/serach
Malumfashi, I. A. (2013) Wanne Ne Ra’ayi Kwakkwara Tsakanin Ra’ayi “Ibrahimiyya ” Da Ummariyya” Kan Samuwar Rubutaccen Wasan Kwaikwayon Hausa. A cikin Himma: journal of Contemporary Hausa Studies, Katsina, Department of Nigerian Languages and Linguistics, Ummaru Musa Yar’aduwa Unibersity.
Nollywood Films (2019) htpp//:buzznigeria.com
Sabo, M.A (2004). Furodusa da Ayyukansa: Nazari a kan Fina-finanKannywood, a Cikin Hausa Home Videos: Technology, Economy, And Society, Kano: Gidan Dabino Publishers
Yakasai, M.B da Waninsa (2004). Matsaloli da Nasarorin Masu shirya fina-finan Hausa Musamman Na Kano, a cikin Hausa Home Bideos: Technology, Economy And Society, Kano: Gidan Dabino Publishers
Yar’Aduwa, M.T (2007) Wasan Kwaikwaiyo Na Hausa Nau’o’insa Da Sigoginsa. Kano:Usman Al’amin Publishing Company.
Yar’Aduwa, M.T (2001). Wasan Kwaikwaiyo: Sigoginsa Da Jigoginsa, a cikinAlgaita Journal of Current Research In Hausa Studies. Vol 1 No 1. Kano: Department of Nigeria Languages, Bayero University, Kano
Allah ya kara taimako da jagoranci
Amin, muna godiya.