Skip to content

Hausa audio books da karbuwarsu a arewacin Najeriya

Hausa audio books sun kewaye saƙo da lungu na Arewacin Nijeriya fiye da yadda ake zato ko tsammani. Abu ne da yake gogayya da zamani, kamar yadda aka sani shi kuma zamani abokin tafiya ne. A halin yanzu, a wurare da dama mutane sun fi mayar da hankali ga sauraren audio books fiye da littafan da za su karanta a cikin wayar salula ko kwamfuta ko ma ta hanyar bugaggen littafi. Tun-tuni sun ɗauki ɗabi’ar saurare wadda ta fi sauƙi sakamakon dalilai na uzurorin rayuwa ko kuma na ƙashin kai.

Kafin in hau dokin gwala-gwalan hujjojina in yi sukuwa da zamiya akwai buƙatar in feɗe maku biri har a wutsiya game da waɗannan kalmomin masu zuwa domin fahimtar inda muka dosa:

Hausa audio books: Littattafan Hausa ne da aka sauya daga rubutu zuwa sauti, domin mutane su saurara maimakon karatu.

Arewacin Nijeriya: Yanki ne a Najeriya da yake arewacin ƙasar, mai tarihi da al’adu na gargajiya, inda Hausawa da masu magana da Hausa suka fi rinjaye a tsakanin mazauna yankin.

Ba na ƙwaina sai da zakara! Tun da mun ji wannan, ku biyo ni cikin jerin gwanon hujjojina inda zan warware maku zare da abawa ta yadda aka yi audio books ya samu karɓuwa a arewacin Nijeriya, har ma da misalai masu tarin yawa:

1. Zamani abokin tafiya

A halin yanzu duk wani cigaba da zamani ya zo da shi mutane sukan haɗa kafaɗa da shi su jera don tafiya tare kuma su tsira tare. Wannan ya sa ko da ɓullowar Hausa audio books ya zo wa arewacin Nijeriya, sai nan-da-nan mutanen yankin suka rungume shi da hannu bibbiyu ba tare da sun yi bori da sanyin jiki ba, kasancewar shi abu ne da yake sauƙaƙa wa masu kwaɗayin karatun littaffan Hausa waɗanda wasu uzurorin rayuwa suka yi masu shamaki ga muradansu.

2. Karuwar hidimomin rayuwa

Ayyukan rayuwa sun yi wa makaranta da dama katutu ta yadda duk soyayyarsu ga labaran Hausa sai gani sai hange daga nesa, amma bayyanar audio books ya share masu hawayensu, don yanzu mutum yana aiki tare da sauraren labarai duk a lokaci guda kuma har ya fa’idantu da saƙon da ake son isarwa. Wannan ma yana cikin manyan dalillan da suka ďabbaka karɓuwar shi a arewacin Nijeriya.

3. Sawun giwa ya take na rakumi

Karatun littafai a gidajen rediyo da kafafen sardawa tare da manhajoji ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa sauraren audio books a arewacin Nijeriya, musamman ma yanzu da mutum zai iya sauraren littafi guda cikin kwanaki ƙalilan ba kamar shekarun baya ba, da za a kwashe lokaci mai tsayi ana bibiya a gidajen rediyo. Wannan ‘yancin da Hausawa suka samu na saurare da kansu, a kuma duk lokacin da suke da dama yana ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka saka audio books ƙara yawaita a faɗin arewacin Nijeriya.

4. Rashin na’urar karatu

Mutane da dama suna muradin karatu da kuma son a faɗakar da su ta silar littattafan Hausa, sai dai rashin babbar wayar da za su yi karatu ya ci karo da kudirinsu. Shi kuma littafin a tsarin sauti ko babu waya akan iya jin shi ta hanyar saka memory card a rediyo a saurara. Masu ƙaramar waya kuwa tuni kakarsu ta yanke saƙa, domin kuwa sukan turo audio daidai ƙarfinsu su saurara yadda suke so har ma su tura wa waɗanda suke so.

5. Rashin dama ko juriyar karatun littafi

Akwai mutane da dama da suka shiga sahun gaba na waɗanda suka asassa karɓuwar audio books a arewacin Nijeriya. Su ne waɗanda karatu yake zamar masu cikas ko yake wahalar da su, da kuma ire-iren waɗanda hasken salula ko na kwamfuta yake takura masu, sai suka mayar da sauraren audio a matsayin hanyar nishaɗinsu. Ire-iren su suna nan birjik a birni da ƙauyen arewacin Nijeriya waɗanda suka zama wani tsani na sake ƙarɓuwar audio books.

6. Rashin lafiya ko ido don karatu

Akwai waɗanda ba su gani, ma’ana, masu buƙata ta musamman, su kan so bibiyar labaran Hausa, sai dai babu halin haka sakamakon rashin idon da za su gani. Lokaci guda kayansu suka tsinke bakin kaba a dalilin zamanantar da littafi daga rubutu zuwa sauti. Gudun barin su a baya sai suka fara sauraren shi sosai, har ma suna haɗa kafaɗa da kafaɗa da masu ganin a fagen sauraren audio. Wannan ma wani muhimmin abu ne da ya saka Audio Books sake haɓɓaka a arewacin Nijeriya.

7. Salon karatun audio books

Salon masu karanta labarai daga rubutu zuwa tsarin sauti ya bambanta da yadda mutum zai yi idan yana karantawa a littafi ko a wayar salula da kansa. Masu karantawa suna amfani da salon jan hankali da kuma bayyana duk wani motsi da aka yi a cikin labarin ta hanyar sautin lafazi ko motsin murya kwatankwacin yadda aka wassafa a labarin. Misali idan muryar yara ce sukan yi kwatankwacin irin ta, idan ta tsoho ce ma haka, idan an yi tsawa su yi ko an yi tsaki har ma da guɗa duk sukan ayyana shi a cikin karatun nasu. Wannan ma wata babbar hujja ce da ta saka audio books bunƙasa domin mutanenmu Hausawa suna da kwaɗayin jin muryar taurari daga wurin masu karatu da kuma yadda aka bayyana su. Wannan ma wani babban dalili ne na karɓuwar littattafai audio domin yana ƙara wa masu bibiyar karsashin saurare da ɗokin bibiya.

8. Yiwuwar hada saurare da wasu ayyukan

Mutane sukan iya tuƙin mota, girki, shara, wanki, wanke-wanke, tafiya a ƙafa da sauran wasu ayyukan yau da kullum suna sauraren Audio ba tare da sun katse ayyukansu ba. Idan muka yi duba na tsanaki za mu fahimci wannan sauƙaƙkawar tana ɗaya daga cikin abin da ya ƙara bunƙasa audio domin abu ne da ba sai an sha wahala ba a idan ana yi, kuma ma masu tafiya ko aiki ba su ganin nisan tafiyar tasu, su kam masu aiki yakan rage masu wahalar aikin nasu idan suna saurare. Shi ma wani dalili ne da ya saka shi sake karɓuwa a wurin mutane.

9. Sauki samu

9. Daga ko’ina mutum yake a arewacin Nijeriya in har yana buƙatar sauraren labarin da yake so cikin salon sauti zai shiga Youtube ko wasu kafafen yaɗa labaran da ake wallafa audio books tare da rubuta sunan labarin da yake so, ko na mawallafi. Babu ɓata lokaci kwalliya za ta biya kuɗin sabulu domin kuwa zai samu abin da yake so har ma da ƙarin waɗanda bai je nema ba. Wannan ma wani babban cigaba ne da yake ƙara bunƙasa sauraren audio domin idan littafi ne kafin ya same shi zai wahala matuƙar ba shi da lambar mawallafin, amma audio ba ya wahalar nema, kamar sha da magani ne lokaci guda. Wannan dalilin ma ya sake bunƙasa bibiyar audio tare da karɓar shi a wurin mutane.

10. Rashin iya karatu

A arewacin Nijeriya akwai mutane da dama waɗanda suke ƙaunar bibiyar labaran ‘yan’uwansu Hausawa, amma ba su iya karatu ba ballantana rubutu ta yadda ba za su kai ga tabbatuwar burikansu ba. Amma shigowar audio ya taka muhimmiyar rawa wajen cikar muradansu har ta saka waɗanda ba su da ilmin karatu suna gogayya da masu ilmin wurin sauraren audio. Shi ya sa za a tarar da mutane sun yin dafifi a wurin masu sana’ar tura fina-finai ko makamancin su don a turo masu audio. Ba kamar zamanin baya ba, idan mutanen da ba su iya karatu ba kwaɗayin jin labarai ya cije su, sai dai su ajiye mutum guda a gefe wanda yake karanta masu littafi a gida ko a wasu wurare na daban. Tuni zamani ya shafe wancaan lamarin yanzu kowa zai iya saurara da kansa ba tare da damuwar komai ba shi ya sa ma suka sake karbar shi.

11. Karuwar samun kudin shiga ga marubuta

11. Mawallafan da ake karanta labaransu sun taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa harkar audio domin sun mayar da shi sana’a har ma suke taka tudu biyu, domin bayan sun gama cin kasuwar littafi a takarda sai su sayar wa masu tashoshin Youtube nan ma su ƙara samun wani togamashi. Sanin kanmu ne abu ne na ƙaruwa, kuma duk abin da za a samu cigaba ba zai zama saniyar ware ba. Wannan ma wata babbar hujja ce da ta sa aka karɓi audio books, musamman ma da kasuwar marubutan ta sake samun karɓuwar a arewacin Nijeriya.

12. Sauƙin kudi

Audio yana samuwa da kuɗi ƙalilan, ma’ana dai sayen shi ya fi arha fiye da littafi kwantankwacin farashin kwanon shinkafa da dussar marasa. Dalilin arhar nan da aka samu sai mutane suka mayar da shi abin ɗebe masu kewa. To duk wani abu da za a samu da sauki matuƙar yana da amfani yakan yawaita fiye da yadda ake zato.

Karkarewa

Hausa audio books yana ɗaya daga cikin ababen da suka samu ƙarɓuwa sosai a arewacin Nijeriya kasancewar shi wani babban cigaba da zamani da ya zo da shi ta fuskoki da dama. Duk wani abu da zamani ya zo da shi yakan samu karɓuwa a wurin mutane matuƙar mai amfani ne ga al’umma, kamar dai yadda tasirin audio a arewacin Nijeriya ya bunƙasa har ya tumbatsa. Da wannan nake sake tabbatar mana cewar mutane sun karɓi audio ɗari bisa ɗari a arewacin Nijeriya duba da gwala-gwalan hujjojin da na gabatar.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page