Skip to content

Manyan Kura-Kurai 10 da marubuta ke yi da yadda za su kauce musu

Kamar kowacce irin sana’a, rubutu yana da wasu matakai ko tsari da lallai ne mutum yana buƙatar ya bi su kuma ya ƙware akansu matuƙar yana son ya isar da saƙonsa ga waɗanda suka dace. Bai yiwuwa haka kawai mutum ta fara rubutu ba tare da sanin abubuwan da rubutun ya ƙunsa ba kuma ya sa ran cewa zai ci nasara. Ba ma wannan kaɗai ba, hatta waɗanda suka ci nasara ko suka yi shura a harkar rubutu ba su fi ƙarfin su yi kuskure ba. Ballantana kuma wanda shi yanzu ma zai fara. To, ko da kai sabon marubuci ne ko kuma wanda ya daɗe yana yi, tabbas ya wajaba akanka ka kiyaye waɗannan kura-kuran waɗanda aikata su na iya rage kimar rubutunka. Fahimtar matsala rabin maganin matsala ce. Sanin kura-kuran da ya kamata ka kiyaye tare da fahimtar hanyoyin kauce musu na iya taimakawa sosai wajen ingantanwa tare da haɓaka naka rubutun. Manufar wannan maƙala ita ce ta fahimtar da kai waɗannan kurakurai tare da kawo mafita.

1. Kuskure: Rashin Tsari

Ɗaya daga cikin manyan kura-kuran da mafi yawancin marubuta ke aikatawa shi ne rashin tsari. Sau da dama sai ga ka marubuci ya hau rubutu haka kawai kai tsaye ba tare da ya yi wani tsari na yin wannan rubutun ba, ba kuma tare da takamaiman bigire da yake son kaiwa gare shi da rubutun ba. Sau da dama irin waɗannan marubutan su ne waɗanda sai sun yi nisa sai su kasa motsawa daga inda suka tsaya. Saboda dama can basu da wata tsayayyar manufa game da rubutun, kawai dai suna yi ne. Misali, mutum ne zai rubuta labari, amma bai san farko, tsakiya da kuma ƙarshen labarin ba. Don haka sai ya yi ta ɗanwaken zagaye yana neman yadda zai kamo bakin zaren labarin amma ya kasa. Daga ƙarshe ya ɓata wa kansa da masu rubutu lokaci, kuma da kasu sharhi za su caccake shi sai ya fara cewa hassada suke yi mishi.

Mafita:

Ka ɗauki lokaci ka bi aikinka a hankali ka tsara shi yadda ya kamata. Ka zana jadawalin yadda al’amura za su tafi a cikin labarin naka. Daga mataki kaza sai kaza, daga nan sai can. Daga wannan babi sai wancan. Tauraro kaza yana da alaƙa da tauraro kaza. Ɓangare kaza na labarin shi zai haɗe da ɓangare kaza domin fitar da asalin jigon labarin. Idan ka yi irin wannan tsarin, shi ne zai taimaka maka ko da ka maƙale a hanya ka san ina ya kamata ka bi. Kuma masu yin irin wannan tsarin aikinsu ya fi kyau kuma ya fi fita musu cikin sauƙi.

2. Kuskure: Zuzutawa

Zuzutawa kan faru ne yayin da marubuci ya ƙuƙe wurin faɗaɗa bayani game da wani abu fiye da ƙa’ida, ko kuma ta hanyar maimaita magana ɗaya ko kuma kawo wasu bayanai na babu-gaita-babu-dalili a cikin labarinsa. Irin wannan kuskure ne ke sa masu karatu su kasa yarda da labarinsa ko ma su ji ya fitar musu a ka. Sau da dama ma sai ka ji wasu na cewa ‘ai marubuci wane ƙaryarsa ta shahara.’ Ka ga batun ma labarin ya yi tasiri a zukatansu ko ma ya kai ga wanzar da canji bai taso ba. Mafi yawancin irin wannan kuskuren na faruwa ne a tsakanin sabbin marubuta waɗanda ke ganin kamar yawan labari ko girman littafi shi ne iya rubutu.

Mafita:

A Koyi yadda ake taƙaita magana a yayin rubutu. A kuma tabbatar an tace rubutu sosai tare da rage duk wani bayanin da bai da wani muhimmanci a cikin rubutun ta yadda za a ɗaure labarin zam ya zamana ya riƙe tunanin mai karatu. Ka tambayi kanka, shin wannan jumlar tana da wani muhimmanci a cikin wannan labarin? In har ba ta da shi, to cire ta kawai. Sannan karanta rubutunka kafin ka fitar da shi zai taimaka ƙwarai waje ba ka damar rage abubuwan da suka kamata a cire.

3. Kuskure: Nuna halin ko in kula ga masu karatu

Yin rubutu haka kawai ba tare da halarto da waɗanda ka ke yin rubutun domin su a daidai lokacin da ka ke yin rubutun ba na iya sa wa saƙon da ka ke son isarwa ya kasa zuwa inda ya kamata ya je. Misali: yin amfani da kalmomi masu tsauri ko kuma manya-manyan karin magana a cikin littafin da ka rubuta domin yara, ko kuma nuna son iyawa da gwanintar iya sarrafa harshe a cikin littafin da aka rubuta domin ‘yan makaranta na iya sa masu karatu su ƙauracewa rubutunka gaba ɗaya.

Mafita:.

Kafin ka fara rubutu, ka san su wa kake yin rubutun domin su. Idan ka fahimci wannan, sai ka yi rubutun a harshe, da sauti, da murya irin wadda za su iya fahimta. Ka kuma yi amfani da jigo da salo irin wanda ya dace da su.

4. Kuskure: Ƙin tace rubutu

Marbut da dama suna aikata wannan kuskuren. Wasu da sun yi rubutu haka kawai za su tura wa masu karatu ba tare da sun sake bibiyar wannan rubutu sun duba ko akwai gyaran da ya kamata su yi ba. Rashin komawa a duba aiki yadda ya kamata ke sa kai ta ganin kurakurai a cikin rubutun da shaɓa iri-iri a cikin littafin.

Mafita:

Komai ka gani yana son gyara sai dai in bai samu ba. Ba gazawa bace ba rauni bane kuma ba rashin iya bane ke sa mutum ya koma ya duba aikinsa ko kuma ya ba wani ya duba mishi. Face sai don son ganin an fitar da aiki managarci. Ka duba aikinka da kyau ka yi gyaran da dace ya fi akan a ce sai ya fita tukunna a yi ta surutu game da gyaran da bai taka kara ya karya ba.

5. Kuskure: Tsaron rashin nasara

Tsoron rashin nasara na iya jawo cutar farfaɗiya ta kama alƙalamin marubuci. Hakan ke sa wasu marubutan su ma kasa rubuta labarin ko kuma su kasa kammala wanda suka fara. Sau da dama irin wannan tsoron kan samo asali ne daga rashin yarda da kai, tunanin sai an yi abu tsaf-tsaf ko kuma takura wa kai wajen ganin an cimma wani gaci na tsammani.

Mafita:

Rashin nasara ba baƙon abu bane a wurin kowa. Ba lallai ne don kayi nasara yau ya zama kullum kuma kai mai nasara bane. Kamar yadda rashin nasara a yau baya nufin rashinta har abada. Ita rashin nasara ma wani ɓangare ne na ƙara girma da samun damar gyara abubuwa da dama a gaba. Manyan marubuta irin su J. K Rowling da Stephen King ma sun fuskanci ƙalubale iri-iri amma hakan bai hana su zama abinda suka zama ba a duniyar rubutu.

6. Dogaro da gana-garin magana/jigo

Amfani da gama-garin magana, karin magana, jigo ko yankin magana na iya sa masu karatu su ji ai sun saba jin ire-iren su. Don haka sai su kasa ɗaukar marubuci da muhimmanci. Misali; kiran tauraron labari da ‘ƙaƙƙarfa kamar zaki’ ba baƙon abu bane, kuma ba zai wani burge masu karatu ba.

Mafita:

Amma ko da za ka ɗauki jigo wanda yake gama-gari ne, to sai ka canza salo. Yi ƙoƙari ka ƙirƙiro wani abu sabo maimakon ka dogara da gama-garin abin da mafi yawancin mutane ke amfani da shi. Ka nemo sabbin hanyoyin da za ka iya bayyana abinda ke ranka ta hanyar amfani da salo na daban a rubutunka. Misali: maimakon ka ce ‘lokaci na gudu’ kana iya cewa ‘kamar da wasa haka awoyi daga cikin ranakun rayuwarmu ke wucewa ta tsakankanin yatsunmu amma ba mu ankara ba’ da dai sauransu.

7. Kuskure: Rashin gina taurari yadda ya dace

Taurari su ne zuciyar kowane labari. Amma duk da haka wasu marubutan ba sa maida hankali wajen ganin sun ƙirƙiro taurarin da za su shiga zukatan masu karatu. Sai ka ga tauraro da ɗabi’a iri kaza a babi kaza, ana shiga wani babin kuma ka ganshi da wata. Sannan wasu taurarin ba a basu lokacin da ya dace balle su girma daga inda suke tun a farkon labarin har zuwa ƙarshe.

Mafita:

Kana iya fitar wa da taurarin labarinka jadawali na musamman mai ɗauke da bayanan duk da suka dace game da su. Yin hakan zai ba ka damar komawa kana dubawa akai-akai saboda kar ka sauka daga kan layi. Misali; abu ne mai wahala ace ga tauraro mai kunya da ƙarancin magana ya tashi ya yi wani abu gatsal haka irin wanda bai saba ba sai dai in wani abu ne ya faru da shi da har ya sauya daga inda ya ke. To in ba ka bayyana wannan abin da ya kawo canjin ba masu karatu sai su gundura da irin wannan hawan-ƙawarar da ake yi musu kuma su kasa yarda da labarin naka.

8. Kuskure: Sauri ko nawa

Wasu marubutan saboda gaggawar ganin sun gama rubuta labari sai su yanke wani ɓangare na labarin kawai su dira a wani. Wannan ba ƙaramin kuskure bane. Domin yana hana mai karatu jin cewa lallai abinda ya faru a ƙarshen labarin ya dace da ya faru. Akwai wadu kuma da ke jan labari su yi ta yaƙwanƙwana shi haka kawai suna ja wa masu karatu rai fiye da kima har ta kai ga suna tsallake shafuka zuwa shafi na gaba. Dukkan waɗannan kuskure ne da bai kamata a samu marubucin ƙwarai na aikata su ba.

Mafita:

A yi ƙoƙarin daidaita aiki da kuma sakamakon aikin. A yi amfani da rubutun sauri wajen da ya dace, a kuma tafi a hankali a wurin da ya dace. Hanya mafi sauƙi da za a iya gane wane irin salo masu karatu suka fi so shi ne ta hanyar jin ra’ayin masu karatu.

9. Kuskure: Ƙin ɗaukar shawara

Wasu marubutan sam ba sa ɗaukar shawara. Musamman idan masu karanta labarin nasu ne. Sau da yawa sukan yi tunanin cewa ai aikinsu ya fi ƙarfin kuskure ko kuma sun fi ƙarfin a yi musu gyara. Irin wannan halin ke sa marubuci ya kasa ci gaba.

Mafita:

Kamata ya yi marubuci ya kasance mai sauraron ƙorafin masu karatu tare da ɗaukar shawararsu. Haka kuma marubuci ya kasance mai karɓar ƙorafi ko suka da buɗaɗɗiyar zuciya. Hakan shi zai ba ka damar sanin inda ya kamata a yi gyara.

10. Kuskure: saurin karaya

Rubutu ƙalubale ne mai zaman kansa, kuma sau da dama rubutu na buƙatar kaɗaici. Wannan dalili ne ke sa wasu marubutan ke karaya har ma su ajiye wani aikin nasu tun kafin ya ginu saboda rashin samun ƙwarin gwiwa, fushi ko kuma tsoron faɗuwa.

Mafita:

Marubuci ya zama mai haƙuri da juriya tare da kafewa akan muradunsa. Ka zagaye kanka da mutanen da kuke da ra’ayi iri ɗaya waɗanda za su ke ƙarfafa maka gwiwa. Idan kuma in ka tashi yin wani abu mai muhimmanci, to ka fara da abubuwa masu sauƙi na ƙasa kafin ka je ga manya na sama.

Shi rubutu wata irin tafiya ce wadda ke cike da ƙalubale iri-iri. To amma duk da haka, kauce wa irin waɗannan kurakuran na taimakawa wajen tsallake irin waɗannan ƙalubalen. Musamman tsara aikinka kafin ka fara da kuma komawa ka duba inda gyara ka yi.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page