Skip to content

Nazari kan rikidar wakar Jarumar Mata ta Hamisu Yusuf (Breaker) ta fuskar jigo

Abstract

The paper entitled “Madubi Daya Fuska Hudi: Nazari Kan Rikidar Wakar Jarumar Mata Ta Hamisu Yusuf Bureka (Breaker) Ta Fuskar Jigo” This paper is aimed to analyse the changes or adaptation that occurred from the popular poem “Woman Heroine (Jarumar Mata) which is written and sang by famous Hausa poet in modern time Hamisu A Yusuf Dorayi who is well known as Hamisu Breaker, which later other poets like Ummi M. Dart, Yusuf Mai Waka, Auwalu Iguda (Dankwairon Ma’aiki) and Musa Abubakar Sadik derived the poem Jarumar Mata (Woman Horeine) completely to reproduce their song in different format. Moreover, close reading theory is used as a theoretical framework for the research analysis. Also, both written and oral (literature) songs for the purpose of the study were gathered on social media platform especially Facebook and YouTube. The research finds out that after the first poem which its central theme is “Soyayya” (Love) the other poets used the poem in different way and create other themes such as “Kudi” (Money), “Madahu” (Praise), “Ilimi” (Knowledge) and “Soyayya” (Love).

1.0 Gabatarwa

Waka tsohuwar hanya ce ta isar da sako ta sigar hikima da azanci da gwanintar harshe, ta hanyar amfani da zababbun kalmomi kuma bisa wata tsararriyar ka’ida, sanannan abu ne tun daga da har zuwa yanzu duk al’ummun duniyasuna amfani da waka a cikin kowane irin al’amari nasu da ya shafi yau da kullum ba wai Hausawa kadai ba. Kuma a iskan da ke kadawa a halin yanzu fasaha ko hikimar waka ta ratsa kowane al’amari na rayuwar dan Adam.

Masana sun bayyana waka a matsayin babbar ‘ya daga cikin ‘ya’yan adabi guda uku, kuma it ace mafi shaharar cikinsu. (Dumfawa, 2019; Yakawada 2019).

Sannan akwai wakar baka akwai kuma rubutacciya, sannan rubutacciyar waka ta ratso zanguna da yawa kama tun daga karni na 15 wanda daga nan ne aka fara samun birbishi na rubutacciyar waka. An ci gaba da samun rubutattun wakoki a karni na 17-18 amma basu yawaita ba, sai dai kakar wakoki ta yanke saka ne a karni na 19 a lokacin Jihadin Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo, kuma duk wakokin da aka samu a wadannan karnuka wakoki ne da suka shafi fadakarwa da sanin ilimin addini da tauhidi da abin da ya kunshi lahira ko tashin kiyama da yabo ko begen Annabi Muhammadu (SAW) da Sahabbai ko Salihan bayi abin da a takaice ake kira “Faru’a / Madahu” (Dangambo, 2008; Dumfawa, 2019 & Yakawada, 2019).

A Karshen karni na 19 aka samu wakoki masu jigon duniya, wadanda ake kira “wakokin Hululu” abin da ya gangaro har zuwa karni na 20 wanda kofar wakoki masu jigon duniya suka bude, wanda hakan ya kai kololuwa a karni na 21 (Yanzu) wanda aka samu wakokin zamani, so ko soyayya na cikin manyan jigogin da suka mamaye wakoki zamani a karni na 21.

1.1 Waiwaye dangane da wakar Jarumar Mata

Wakar Jarumar Mata Ta Hamisu Bureka tana cikin wakokin zamani wadda jigonta soyayya ne. Waka ca ta zamani da ta yi tasiri ta kuma samun tagomashi a tsakanin matasa maza da mata, musamman ma ‘yan mata da matan aure, waka ce da mawakin ya yi ya saki a watan Janairu na shekarar 2020, amma ba ta shahara ba  sai a watan Yuni na shekarar 2020 daidai lokacin da ake bikin shagalin karamar sallah (Sallar Azumi), hakan ya biyo bayan sanya wata gasa da A’isha Falke Shugabar Kamfanin Northern Habiscus ta sanya, wato gasar rawa a gaban miji, wannan gasa ta samu karbuwa ga matan aure da yawa, musamman masu hali, kuma a lokacin guda ta samu yabo da suka daga bangarorin mutane daban-daban yayin da bidiyoyin gasar suka ringa kai-komo a kafafen sadarwa na zamani irin su Fesbuk da Wassaf da Yutub da kuma Instagiram. Da yawa daga cikin wadanda suka yi bidiyon rawar matan aure ne suka yi wa mazajensu, sai dai an samu wasu mazan da suka yi wa matan su, yayin da wasu ‘ya’ya suka yi wa iyayensu abin da ya ci gaba da yaduwa, sannan wakar ta ci gaba da rikida, domin an samu wasu samari wani ya yi wa akuya wani ya yi wa katifar kwanciyawani ya yi wa naira dubu, sannan sojoji guda biyu kowa ya yi wa bindigarsa haka shi ma dan sanda ya yi wa bindigarsa sai kuma wani da ya yi wa naman sallah (Ragon layya). Kasantuwar wakar babu amshi kuma namiji ne Hamisu Breaker yake rera wakar ga mace (Jaruma) wato Momi Gombe, ba tare da ta amsa ba, ko ta rera wani baiti, sai dai rawa da suke tare. Haka su ma wadanda suka kwaikwayi wakar idan mace ce ke yi wa mijin, shi mijin bai amsawa sai dai rawa, wasu ma zaune kawai suke a wuri daya, haka idan miji ke yi wa matarsa, matar ba ta amsawa sai dai rawa ko dariya da ke nuna annashuwa da shaukin soyayya. Duk bidiyon da aka yi na kwaikwayon wakar bai wuce tsawon dakika talatin ba, sannan duk wadanda suka dauki wakar suka kwaikwayi  wani abu sun dauka ne daga baiti na 1-5 ko 6. Misali

  1. Ashe da rai nake sonki,

Jaruma ba da zuciyata ba.

2. Komai ruwa da iska a kanki,

Ba zana dena kewa ba.

3. Idan na samu zarrar samunki,

Ba zana tanka kowa ba.

4. Ni banga mai harara ba,

Bare na waiwaya ahh.

5. In dai a kanki ne zana jure,

Wahalar zuwa garin nisa.

6. Da an tabaki a jirani don ko,

Tilas na zo na dau fansa.

Wadannan su ne baitocin da wadanda suka kwaikwayi wakar suka yi wa wani abu suka ringa rerawa, kuma yadda suke ga asalin wakar haka suka ringa rera su suna nuna abin da suke yi wa wakar. Sai dai akwai wadanda suka yi amfani da karin wakar suka baddala wakar ko suka rikidar da wakar suka yi wani abu daban ta hanyar bin tsarin wakar da karinta tun daga farkon wakar har zuwa karshe. Daga ciki akwai Ummi M. Dart da ta yi wa saurayinta wadda madadin Jaruma ta maida wakarta Jarumi, sai Yusuf Mai waka da ya yi wa kudi, sai Auwalu Iguda da ya yi wa Ma’aiki (SAW) wato Begen Rasulu sai kuma Musa Abubakar Sadik da ya yi wa ilimi, wanda wadannan wakoki ne za a kalle su ta fuskar jigo sakamakon rikidar wakar ta jaruma da take a matsayin asalin madubi su kuma sauran wakokin a matsayin fuskoki, abin da ya sanya aka ambaci madubi daya amma da fuskoki guda hudu.

2.0 Ma’anar madubi

Bargery (1934:740) a kamus dinsa, ya bayyana ma’anar madubi da cewa “kalma ce da nuni ko nufin “magani, madibi, mahangi”

Madubi shi ne abin tsinkaye ko hange ko kallo wanda aka yi da karau na gilashi da ke bayyanar da sura ko inuwa ko hoto idan an nuna ko an kara shi ga abu.

3.0 Ma’anar fuska

Fuska kalma ce ta Hausa da ke cikin sunayen jinsin ta mace da ke dauke da ma’anar “gaba dake bangaren kai ta gaba da ta kunshi baki da idanuwa da hanci, wato ita ce maganin dan Adam. Sannan a wani kaulin fuska na nufin bangare ko rukuni ko yanayi ko kauda kai ko nuna halin ko-in-kula.

4.0 Ma’anar waka

Waka tsararriyar maganar hikima ce da ake rerawa ba fada kurum ba, wadda ke kunshe da wani  s sako a cikin zababbun kalmomi wadanda aka auna domin furucinsu ya yiwu ba tare da tuntube ba (Yahya 1997).

Waka wani sako ne da aka gina shi kan tsararriyar ka’ida ta baiti, dango, rerawa, kari(bahari) amsa-amo (kafiya), da sauran ka’idojin da suka shafi daidaita kalmomi, zabensu da amfani da su cikin sigogin da ba lallai ne haka suke a maganar baka ba. (Dan Gambo 2008).

Ta lura da wadannan bayanai za a ce waka sako ne dunkule cikin hikima da amfani da tsararriyar ka’ida.

4.1 Ra’ayin masana dangane da wakar zamani

Kasantuwar an samu canje-canje dangane da rubutattun wakoki sakamakon tasirin zamananci musamman ta fuskar budewa da rufewa da jigo da sauransu abin da ya yi hannun riga da yadda wakokin karni na 19 suke, musamman a karshen karni na 20 inda tasirin bakin al’adu ya mamaye rubutattun wakoki da aka ringa yi wa kida da nau’ukan abun kida na zamani irin su Jita da Fiyano da sauransu. Wanda hakan shi ne ruhin wakokin karni na 21,wakar jarumar mata ma ba a barta a baya ba wurin bin sawun sauran wakokin zamani takwarorinta.

Wannan ci gaba na zamani da rubutattun wakokin Hausa suka samo kansu a ciki har aka kira su da wakokin zamani, ya haifar da muhawara dangane da matsayi ko gurbin da za a aje wadannan wakoki, abin da ya samar da ra’ayoyin masana kamar haka:

Gusau: yana ganin  wakoki ne na baka, tun da an hada su da kida.

Yakawada: yana yi masu ganin rubutattun wakoki ne. Illa cewa ci gaban zamani ne ya zo da su, kamar yadda muke samun canje-canje a suturunmu.

Dangambo: yana da fahimtar cewa a kira su da wakokin zamani.

Usman: ya kira su da sunan “wakoki masu ruwa biyu” wato sun debo nan sun debo can.

Muhammad: yana ganin cewa wadannan wakoki ya fi dacewa a kira su da sunan “wakoki Jemagu”. Domin sun sabawa tsarin wakar baka ta asali, haka nan kuma waka rubutacciya. Amma idan aka samu wata waka a cikin irin wadannan wakoki ta cika dukkan sharuddan rubutacciyar waka, illa cewa ana kida ana rawa, ana iya sanya ta a cikin rubutattun wakoki. (Muhammad, 2019:5)

5.0 Ma’anar jigo

Jigo a fagen waka yana nufin sako ko manufa ko bayani ko ruhin da waka ta kunsa wanda kuma shi ne abin da wakar ke son isarwa ga mai sauraro ko karatu ko nazarinta (Yahya, 1997:75)

“Abin da ake nufi da jigo shi ne sako, manufa ko abin da waka ta kunsa, wato abin da take magana a kai. A takaice jigo yana nufin dunkulalliyar manufa” (Dangambo, 2008:12)

A takaice dai jigo shi ne gundarin manufa ko sakon da waka ta kunsa, wanda mai sauraro ko karatu ko nazari zai iya fitarwa daga cikin waka a fahimtarsa ya alla tun daga farkon wakar ko karshe ko gaba daya.

6.0 Madubi daya

Madubi daya a wannan nazari shi ne wakar Jarmar Mata, wato asalin wakar, wannan waka ce ta soyayya da ke bayyana tsananin son da shi masoyi(Hamis Breaker) yake yi wa masoyiyarsa wato Jaruma. Jigon wannan waka ya fito a cikin baitoci da yawa. Misali

                        B1. Ashe da rai nake sonki,

                              Jaruma ba da zuciyata ba.

Wannan baiti ya nuna karfin son da Bureka ke yi wa jaruma, wato da gaba daya yake sonta da dukkan ransa ba wai cikin zuciya sonta ya tsaya ba, wanda hakan ke nuna son ya kai matuka.

                        Haka B.5-6

                                                In dai a kanki ne zana jure,

                                                Wahalar zuwa garin nisa.

                                                Da an tabaki a jirani don ko,

                                                Tilas na zo na dau fansa

                                                (Jaruma: Hamisu Bureka)

Wadannan baitoci suna kara fito da jigon wakar wato soyayya, wanda shi masoyin ke nuna zai iya jura duk wahala komai nisan gari domin zuwa ganin masoyiyar tasa, kuma duk wanda ya taba ta babu shan ruwa babu ketare hanya sai ya zo ya daukar mata fansa a baiti na

B 8.

                                    Sirrin na rayuwata ke ce kawai,

                                    Da kin kira da na amsa.

                                    (Jaruma: Hamisu Bureka)

Ya nuna cewa ita ce sirrin rayuwarsa, a nan ma yana sake jaddada jigon wakar.

                        B.12

                                    Sam ba batun na fasa ko za a ce,

                                    Mani in bada rai fansa.

                                    (Jaruma: Hamisu Bureka)

Hamisu ya nuna a batun soyayyar jaruma babu gudu babu ja da baya, har ransa zai iya sadaukarwa, wato ransa fansa ne ga masoyiyarsa.

                        B.21

                                    Idan babu ke ina ne zan,

                                    Saka zuciyata ta bar yawan kuna.

                                    (Jaruma:Hamisu Bureka)

Mawakin ya nuna ita ce mahadin rayuwarsa idan babu ita to rayuwarsa na cikin garari.

B.25

             Ina ji ina gani yadda nake,

            Sonki ya fi karfina.

B.14

            Ina ji kamar mafarki ne,

            Ina son ki so mataki ne.

                                    (Jaruma: Hamisu Bureka)

Wadannan baitoci suna fayyace jigon wannan waka, wato yadda son da yake yi wa jaruma har ma son ya fi karfinsa.

Masoyi yana da rana ne

                                    Masoyi yana da rana ne

Masoyi yana da rana neee

                                    (Jaruma:Hamisu Bureka)

A nan yana bayyana matsayi ko muhimmanci da masoyi yake da shi.

6.1 Fuska ta daya

Fuska ta daya a nan na nufin yadda Ummi M. Dart ta rikidar da wakar ta yi wa jarumi kamar yadda Bureka ya yi wa jaruma, duk yadda Bureka ya yi wakarsa haka Ummi ta yi, sai dai ta juya lamirin zuwa ga namiji wato jarumi. Ita ma jigon wakar kan soyayya ne. Ga misali daga baitocin.

            B.1

                        Ashe da rai nake sonka,

                        Jarumi ba da zuciyata ba

                        (Jarumi: Ummi M. Dart)

Ummi ita ma ta bayyana yadda take son jaruminta da dukkan ilahirin ranta.

                        B. 5-6

                                    In dai a kanka ne zana jure,

                                    Wahalar zuwa garin nisa.

                                    Da an tabaka a jirani don ko,

                                    Tilas na zo na dau fansa.

                        (Jarumi: Ummi M. Dart)

Wadannan baitoci sun kara fito da jigon wakar, kamar yadda a baya irin su suka fito da jigo a wakar jaruma.

                        B.8

                                    Sirri na rayuwa kai ne kadai,

                                    Da ka kirani na amsa

B.12   

                                    Sam ba batun na fasa ko za a ce,

                                    Min in bada rai fansa.

                        B.14

                                    Ina jin kamar mafarki ne,     

                                    Ina son ka so mataki ne.

                        B.21

                                    Idan babu kai ina ne zan

                                    Saka zuciya ta bar yawan kuna.

                        B.25

                                    Ina ji ina gani yadda nake,

                                    Sonka ya fi karfina.

                                    (Jarumi:Ummi M. Dart)

Wadannan suna cikin baitocin da suka warware jigon wannan waka wato soyayya. Soyayyar da Ummi M. Dart ke yi wa jaruminta.

                                    Masoyi yana da rana ne

                                    Masoyi yana da rana ne

                                    Masoyi yana da rana neee

                                    (Jarumi: Ummi M. Dart)

A nan ita ma tana bayyana matsayi ko muhimmancin masoyi

6.2 Fuska ta biyu

Fuska ta biyu a nan na nufin yadda Yusuf Mai waka ya juyar ko rikidar da wakar jaruma ya yi wa kudi, wadda jigonta a kan kudi ne, wato matsayin kudi da tasirinsu. Misali

                        B.1

                                    Ashe da rai nake son,

                                    Kudi ashe ba da zuciyata ba.

                                    (Kudi: Yusuf Mai waka)

Ya bayyana jigon wakar cewa yana tsananin son kudi da dukkan ransa.

            Haka a wadannan baitoci ya warware jigon wakar cewa kudi ya yi wa wakar sakamakon muhimmanci da tasirin da kudi suke da su. Ga abin da yake cewa:

                        B.8

                                    Sirri na rayuwata kudi,

                                    Da sun man kira da na amsa.

                        B.5

                                    In dai a kansu ne zana jure,

                                    Wahalar zuwa garin nesa.

                        B.6

                                    Da an tabasu a jirani don ko,

                                    Tilas na zo na dau fansa.

                        B.12

                                    Sam ba batun na fasa ko za a ce,

                                    Mini na ba da rai fansa.

                        B.14

                                    Ina ji kamar mafarki ne,

                                    Ina son kudi mataki ne.

                        B.21

                                    Idan babu su ina ne zan,

                                    Saka zuciya ta bar yawan kuna.

                        B.25

                                    Ina ji ina gani yadda nake,

                                    Son su ya fi karfina.

                                    (Kudi: Yusuf Mai waka)

                                    Kudade suna da rana ne

                                    Kudade suna da rana ne

                                    Kudade suna da ranaaa ne

                                    (Kudi: Yusuf mai waka)

Shi ma ya rufe wakar da bayyana muhimmanci da matsayin kudi.

6.3 Fuska ta uku

Fuska ta uku a nan ita ce yadda Musa Abubakar Sadik ya juya wakar ya yi wa ilimi. Misali

B.1

                                    Ashe da rai nake son ilimi,

                                    Ashe ba da zuciyata ba.

                                    (Ilimi:Musa Abubakar Sadik)

A nan Musa ya nuna son da yake yi wa Ilimi da daukacin ransa ne ba iya zuciya ba kadai.

                        B.5

                                    In dai a kansa ne zana jure,

                                    Zuwa garin nisa.

                        B.6

                                    Da an taba shi a jirani dan kwa,

                                    Tilas na zo na dau fansa.

                        B.8

                                    Sirri na rayuwata ilimi ne,

                                    Dan ya min kira kuma na amsa.

                        B.12

                                    Sam ba batun na fasa ko da,

                                    Za a ce na ba da rai fansa.

                        B.14

                                    Ni ban da damuwa in har,

 zan bude ‘yan idanuna.

                        B.15

                                    In ganni gani dab da ilimi,

Shi ne cikar muradaina.

                        B.22

                                    Ina ji ina gani yadda nake,

                                    Son ilimi ya fi karfina.

                                    (Ilimi: Musa Abubakar Sadik)

Wadannan baitoci duk sun taimaka wurin warwarar da kara fito da jigo.

 Ilimi yana da  rana ne

 Ilimi yana da rana nee

Shi ma ya rufe wakar da bayyana matsayi da muhimmancin ilimi.

6.4 Fuska ta hudu

Fuska ta hudu a nan na nufin yadda Auwalu Iguda (Dankwairon Ma’aiki) ya juya ko ya rikidar da wakar Jarumar Mata ta Hamisu Bureka ta koma wakar Bege ta Manzon Allah (SAW), jigonta ya zama a kan madahu ne. Ga misali jigon wakar daga wasu baitoci

                        B.1

                                    Alhamdu godiyata ga Rabbu,

                                    Sarkin da yai ni bawansa.

                        B.2

                                    Ikonsa ne ya sani nake,

                                    Yabon shugaban halittarsa.

                        B.3

                                    In dai da rai da Kaunar Rasulu,

                                    Bege ba za mu daina ba.

                        B.4

                                    Komai ruwa da iska da zafi,

                                    Sanyi ba zamu daina ba.

                                    (Begen Rasulu: Auwalu Iguda)

A wadannan baitoci Auwalu Iguda yana fadar cewa ba abin da ya sanya gaba duniya sai yabon Manzon Allah (SAW) wanda duk rintsi sai ya yi bege matukar dai yana da rai, wanda wadannan baitoci 1-4 sun bayyana jigon wakar kan bege ne.

                        B.7

                                    In har an gayyatan zana jure,

                                    Wahalar zuwa garin nisa.

                        B.8

                                    In an tabani a waya na zo,

                                    Na Bege Rasulu ba wasa.

                                    (Begen Rasulu: Auwalu Iguda)

A wannan baitoci mawakin yana nuna yadda yake begen Annabi (SAW) kuma komai nisa da wahalar gari, idan an kira shi ya zo ya yi begen Annabi, zai zo babu wasa babu bata lokaci.

                        B.13

                                    Tilas a so shi tilas a bishi,

                                    Bege ga Daha mun nisa.

                        B.14

                                    Don ba batun mu fasa yabonsa,

                                    Ko za mu ba da rai fansa.

(Begen Rasulu: Auwalu Iguda)

A wadannan baitoci mawakin na kara warware jigon wakar wato bege (Madahu)

                        B.23

                                    Idan babu Daha lahira in,

                                    An je jiki fa zai kuna.

                        B.24

                                    Kowa ya kama Daha ni kam,

                                    Shi ne cikar muradaina.

                        B.25

                                    Ko da ina ruwa kusa da,

                                    Kada zan kirayi manzona.

                        B.26

                                    Zai bani mafita in sarrafa,

                                    Dabbar da zata min barna.

                        B.27

                                    Ina ji ina gani yarda,

                                    Masoya suke fa kallona.

                        B.28

                                    Tamkar ina ganin manzo,

                                    Kullum cikin fa baccina.

                                    (Begen Rasulu: Auwalu Iguda)

Wadannan baitoci su ma suna kara jaddadawa da fayyace jigon wannan waka.

                                         Masoya Rasulu kun gane

                                         Masoya Rasulu kun gane

                                         Masoya Rasulu kun gane

                                         Masoya Rasulu kun gane

                                    (Begen Rasulu: Auwalu Iguda)

Shi ma ya rufe wakar da tsarin yadda aka rufe sauran wakokin tare da jaddada matsayin begen Annabi (SAW) ga masu saurare.

7.0 Kammalawa

Wannan takarda ta yi waiwaye kan samuwar wakar Jarumar mata da wanda ya yita, da yadda aka sanya gasar rawa gaban miji da wakar abin da ya sanya ta samu tagomashi, har wasu mawaka suka yi amfani da tsarin wakar da karin suka samar da nasu wakokin kan wasu jigogin kamar ilimi da kudi da madahu da soyayya. Sannan takardar ta gano cewa wakar tun daga ta farko har zuwa sauran babu amshi babu karbi, sai dai zubin rufewa wakokin duk iri daya ne. Sannan da wakar Jaruma da wakar Jarumi da Begen Rasulu da Kudi dukkansu na sauraro ne ta Ilimi ce kadai rubutacciya. Sannan wakar jaruma tsawonta mintina uku da dakika sha bakwai ce (03:17) ta jarumi mintuna uku ce da dakika sha hudu  (03:14) ta kudi kuwa mintuna uku da dakika sha biyar ce (03:15), ita kuwa Begen Rasulu mintuna uku ce da dakika sha hudu (03:14) kuma ita kadai ce bata da kida.

Manazarta

Bargery, G. P. (1934). A Hausa- English Dictionary and English-Hausa Bocabulary, Zaria: Bugu na Biyu. Ahmadu Bello University Press Limited

Dangambo, A. (2008) Daurayar Gadon Fede Waka (Sabon Tsari) Kano: KDG Publishers

Dumfawa, A. A. (2019). Laccar Kwas Din Hau 815 Ajin Masta Kaduna: Jami’ar Jihar Kaduna

Gusau, S. M. (2015). Mazhabobin Ra’i Da Tarke A Adabi Da Al’adu Na Hausa Kano: Century Research and Publishing Ltd.

Muhammad, S. S. (2019). Matakan Nazarin Rubutacciyar Wakar Hausa. Zaria: Ahmadu Bello   Unibersity Press And Publishers.

Yahya, A. B. (1997). Jigon Nazarin Waka.Fisbas Media Serbices

Yakawada, M. T. (2019). Laccar Kwas Din Hau 813 Ajin Masta Kaduna: Jami’ar Jihar Kaduna

To cite this paper:

Kabir, J. and Aliyu, U. I. (2022) Madubi Daya Fuska Hudi: Nazari Kan Rikidar Wakar Jarumar Mata Ta Hamisu Yusuf Bureka (Breaker) Ta Fuskar Jigo. Bakandamiya Hikaya

2 thoughts on “Nazari kan rikidar wakar Jarumar Mata ta Hamisu Yusuf (Breaker) ta fuskar jigo”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page