Kusan akasarin shafukan labaraina da na dora a Bakandamiya sun cika ka’idojin da ake bukata, kuma Bakandamiya ta biya ni.
Sunana Lubna Sufyan, daya daga cikin marubutan da suka saka littafinsu a taskar Bakandamiya, wannan kuma sune hanyoyi ko in ce dabarun da nake bi wajen samun views, comments da kuma ratings bayan na dora labarina.
Wanne ka’idoji ne Bakandamiya suke bukata?
- Marubuci ya dora labarinsa a Bakandamiya Hikaya
- Shafi guda na labarin kada ya gaza kalmomi 2500
- Marubuci na iya samun N2000 a duk shafin shi daya da ya samu:
- 500 views
- 10 comments (Banda reply na marubuci)
- 20 rating stars
A ina kake saka labarinka?
In har marubuci ne kai, kuma online, inda kake saka rubutunka na kyauta ba zai wuce
- Wattpad
Idan ka kula, dole a cikin guda ukun nan ne, mabiyan littafinka suka fi yawa. Kuma ina da tabbacin kana da groups, naka na kanka, da kuma wasu a manhajar WhatsApp inda a cikin kowanne akwai mabiyan duk wani rubutu naka.
Ni da kai mu hadu mu yi wani lissafi, daga Wattpad, Facebook har kuma Whatsapp, idan ka hada yawan mabiyanka babu yanda za’ayi su gaza 500.
Idan kuma littafinka na saidawa ne fa? Cinikinka idan har a online ne ba zai wuce a Okadabooks ba da kuma WhatsApp.
Ni da kai duka munsan kalubalen da yake tattare da cinikayyar littafi a duka manhajojin biyu, idan ka cire kason da Okadabooks suke dauka, suma akwai ka’idar sai kudinka ya kai dubu goma kafin ka iya cirewa, sannan mabiyan littafin Hausa da yawa suna korafin wahalar da take tattare da sayen littafi a manhajar, inda yake barin da yawa a cikinmu da zabin da baya wuce siyar da littafin a manhajar WhatsApp ta hanyar kayadde wani kudi, a biya mu tara su a group mu dinga turawa, inda ranar farko muke farawa da kwasar takaicin yan jiran bati, daga zarar munyi update wani zai yi copy ko yayi forwarding inda zaita yawo group-group yana dakile cinikin mu.
Atakaice dai gaba kura ne, baya damisa.
Dabarun da ake bi domin cika ka’idojin Bakandamiya
Idan muka koma batun yanda zaka samu views, ratings da kuma comments da Bakandamiya Hikaya suka ka’idance kafin su biyaka akan kowanne shafi na littafinka. Daga nesa wannan ka’idojin za su yi maka kama da abu mai wahala, kana kuma da tambayoyi irin yaushe zan samu wannan views din?
To ga hanyoyin da ake bi, kuma da yardar Allah in ka bi su zaka iya samu cikin sauki.
Da farko dai idan ka dora labarinka a Bakandamiya Hikaya kyauta makarantanka za su karanta, kuma tabbas za su yi farin ciki, za su ji dadi.
Yanzun mu koma hanyoyin da zaka bi ka samu wannan views, comments da kuma ratings din.
Samun views
1. Sakin wasu shafuka a duk wata manhaja da kake saka littafinka a matsayin dandano
2. A kasan shafin karshe na dandanon, ka yi musu bayanin yanda za su samu littafin a kyauta, amman zaka mayar da posting dinshi a Bakandamiya Hikaya ne kawai, kana bukatar goyon bayan su kamar ko da yaushe. Ka kara jaddada musu kyauta ne, amman Bakandamiya Hikaya za su biya ka tare da taimakon su ta hanyar yi maka comment a karshen kowace chapter, sai kuma su danna maka tauraron da suke tunanin ya dace da shafin labarin wanda dashine zaka samu wannan rating din da ake Magana.
3. Daga kayi posting sai ka dauki link din wannan chapter din daka rigaya ka buga a Bakandamiya Hikaya, sai ka hadata da wani waje mai jan hankali a kacokan din labarin ko kuma ita chapter din. Ga misali daga labarin Yelwa.
“Ku saka mata Munawwara, ku kira ta da Madina. Watakila albarkacin sunayen biyu rayuwar da bata da zabi a kanta ta zo mata da sauki ko yaya ne. Zan so kaina a karo na biyu, ku fada mata mahaifiyarta ta sota a watanni taran zamanta a cikinta, ko ba zata yarda ba Daada ki fada mata ta yafe mun, ki bata hakuri na yanda zata kare sauran kwanakin ta a duniya tana biyan zunuban mahaifanta. Kuma ku fada mata sunan babanta Kabiru, yanayin haihuwar ta ba zai canza cewa ita din jinin shi bace ko da bata da gadon shi. Ke ma ki yafe mun, ki yi mun addu’a ko da rayuwa ba zata sake hada fuskokin mu ba.”
Bayan wannan tsakuren dandano sai a saka link na shafin ta yadda makaranta zasu iya latsawa su ci gaba da karatun a Bakandamiya Hikaya.
4. Sai ka dage da sharing, a duka groups din da kake ciki na Whatsapp, status din ka, da kuma duk wani waje da kake saka sauran litattafanka.
5. Ace cikin kaso dari na shafin littafin, zaka iya kowanne shafi daka saka a Bakandamiya, saika dibi kaso ashirin a ciki ka hada da link din a kasa ka yi sharing din shi, idan baka yanko wani waje mai jan hankali a ciki ba, ta yanda duk wanda ya karanta wannan dan tsakuren to zai ji yana son cigaba da karatun, kaga zai danna link din, idan ya danna kuma ka samu view din shi.
Samun comments da ratings
Wadannan su suka fi views wahalar samu, saboda mu duka mun san ko a Wattpad muna samun wannan matsalar, da yawan makaranta sunfi jin dadin yin comment dinsu a Whatsapp group inda za’a hadu a tafka muhawara, hasashe da kuma tattauna abubuwan da littafi ya kunsa. Duk da haka, ka sani a cikin mabiyanka ba zaka rasa wadanda kuka saba dasu ba, wadanda zasu bika ko’ina, su kuma taimaka maka wajen samun wannan comments din da kuma ratings. Irin wadannan su zaka bi daya bayan daya ka yi musu bayanin muhimmancin wannan comments din nasu, koda kuwa fatan alheri ne, da kuma star din da zasu danna maka, ka sanar dasu cewar sai ka cika wadannan ka’idojin ne za’a biya ka.
Ina da tabbacin idan zaka dauki lokaci ka yi wadannan abubuwa, zaka sha mamakin comments da views da ratings da zaka samu.
Na dora labarina na Rai da Kaddara akalla shafuka sama da talatin wadanda suka cika duka ka’idojin da ake bukata, kuma Bakandamiya sun biyani kudin duka shafukan, bayan nayi payment request. Sukan biya ne idan akalla chapter biyar suka cika ka’idojin, kuma zasu biyaka ne a karshen watan da ka nemi kudin, misali ka nema a tsakiyar wata wato shabiyar, to za’a biyaka ne a karshen watan idan ya cika kwanaki talatin.
Duk mai son dora labarinsa ya latsa nan don cikakken Karin bayani.
Allah ya bawa mai rabo sa’a.