Tun da muka dawo gida nake aikin kuka, abinci ma kasa ci na yi, ina jin zafin mutuwar dog, musamman da ya kasance kashe shi aka yi. Ko waye ya yi mishi haka Allah Ya saka mishi.
Ban tuna abin da na gani da daren jiya ba, sai da na kwanta bacci, ido a bude ko a rufe sai in ga mutanen nan tsaye suna wanka tsirara.
Haka nai ta addu’o’i har zuwa kiran sallahr asuba. Bayan na yi sallah na lallaba kitchen ina ciki Aunty ta shigo, na gaishe ta, haka muka rika aiki kowa shiru, har mu ka kammala.
Na dauki fruit din Monkey na fita zuwa cage din nasu.
Tun da na tunkari cage din hawaye ke zubar min, tun ba da na hango wurin zaman dog da kwanciyarshi ba. Idan da ace yana nan da tuni ya nufi kofar cage din yana kallo na tare da jiran isowa ta.
Monkey man duk kuzarinshi ya ragu, da alama ya yi kewar ɗan’uwanshi.
Na isa cikin cage din kamar mara lafiya, dukewa na yi wurin da Dog ke cin abinci na saka kaina a tsakanin cinyoyina na fara kuka a hankali.
Monkey ya rika zagaya ne da hawa jikina yana yar kararshi tare da kokarin lalubo fuskata
Yadda na ga ya matsa da son ganin fuskar tawa ne ya sanya ni zama dirshan, sai ko ya haye kan cinyata yana kallo na da yanayin damuwa, wani lokacin kuma hannunshi yake sanyawa a kan fuskata yana dauke min hawaye kamar yadda ya ga ina yi.
Ban san ko tsawon minti nawa muka kwashe a haka ba.
Sai da murya Aunty ta katse ni ta hanyar kiran sunana
Na juyo fuska jagab da hawaye ina kallon ta, monkey ma kallon ta yake yi daga inda yake zaune a kan kafata.
Kejin ta shigo sosai tana fadin “zo nan Maryam!” cikin tattausar murya ta yi maganar
Monkey na dauke daga kan kafata, sannu a hankali na tako inda take.
Jikinta ta janyo tare da rungume ni, ta shiga bubbuga bayana tare da fadin “Ki yi hak’uri kin ji, na san kina jin zafin mutuwar karen nan, saboda yanayin shakuwar da kuka yi. Ki yi hak’uri kin ji, in Sha Allah kina da tarin lada mai yawa na kiwon da kika yi mishi”
Cikin shesshekar kuka nake gyada kaina da yake kwance a kan kirjinta.
Maganganu masu kwantar da hankali ta rika fada min, har zuciyata ta fara sanyi.
Tare da ita mu ka ba monkey abinci, sannan muka fita tare.
Ita ce ta rarrasheni na taɓa abinci kadan sannan na koma dakina na kwanta
Saboda sosai ban lafiya, zuwa karfe sha daya zazzabi mai zafi ya rufe ni.
Aunty ce ta yi treating dina har da saka drip.
Zuwa yamma na dan ji sauki kadan, sai dai rashin kwarin jiki.
Cikin dare na ji kamar ana tashina, bude idona ke da wuya na ga wasu mutane tsirara sun cika dakina suna ta yin wani abu da ni ban san shi ba, amma kuma tsoro yake ba ni.
Na rufe ido gam tare da juya baya ina karanta duk wata addu’a da ta zo bakina.
Yau ma dai ban runtsa ba har gari ya waye, ido bude ko rufe wadannan mutanen nake kallo.
Aunty ce ta yi komai na gidan, ta kuma duba ni tare da ba ni magunguna, sannan ta wuce wurin aiki, bayan na tabbatar mata zan iya zama gidan ni kadai.
Na fada mata haka ne kawai don ta samu kwarin gwiwa ba wai don ba na jin tsoron ba
Idan akwai abin da ban so ko nake jin tsoro yanzu bai wuce dare da kuma zama ni kadai ba
Shi ya sa ma bayan fitar ta na fito waje kan entrance na zauna, bayan na kwanto monkey na sake shi a tsakar gidan.
Duk wani motsi na shi a kan idona, saboda shi yana da ɓarna ba kamar dog ba.
Idona a kanshi lokacin da yake tsakanin fulowoyin da suka kawata katangar gidan, daga wajen da nake dai ba zan iya sanin me yake ba, amma yadda ya yi concentrating ya tabbatar min da koma menene yake yi ya dauki hankalinsa.
Ni ma sai na tattara hankalina kaf a kanshi, har zuwa lokacin da ya dago yana kallona.
Na yi amfani da hannuna na dama na yafito shi alamun ya zo
Tun ban aje hannuna ba ya sheko da gudu, sai da ya kusa zuwa wajena ya juya da gudu wurin da ya baro.
Ina ta kallon shi har zuwa lokacin da ya dakko wata katuwar kwalba green irin ta da din nan da ake gwada mai.
Hankalina sosai na tattara a kan shi har zuwa lokacin da ya karaso hade da mika min kwalbar.
Na karɓa ina juya ta hade da kare ma abin da ke cikinta kallo.
Wata kurmusheshiyar laya ce wacce daga kasa ta cika kwalbar tab.
Daga cikin abin da ke ba ni mamaki tare da layar har da yadda aka yi aka sanyata a cikin kwalbar.
Saboda bakin kwalbar ya yi kadan wajen wucewar layar, kuma babu inda aka fasa kwalbar bare in ce ko sai da aka fasa kwalbar sannan aka saka layar.
Ban gama mamakin ba, na ji horn din mota daga wajen gate.
Bayan Hammawa ya bude gate motar Ya Azeez ta shigo.
Ban dauke idona ba, har ya fito sanye cikin shirt coffee color da farin wando, kafarsa sanye da farin cambas.
Ya nufo mu hannunsa rike da wani katon abu, an yi wrapping din Shi da wrapping paper mai kyan gaske.
Monkey ya nufe shi cikin dokin ganinshi, ni kuma na yi saurin boye kwalbar da ke hannuna.
Ban janye idona a kanshi ba har ya karaso inda nake “Auntyn na nan?” ya fara tambayata lokacin da ya karaso kusa da ni sosai
Na girgiza kai alamar a’a.
“Biyo ni.” ya yi maganar hade da murɗa handle din kofar ya shiga.
Da sauri na saka kwalbar da Monke ya ba ni cikin fulwoyin da ke jikin ginin Aunty kafin na bi bayan shi
Kai tsaye dakinsa na nufi saboda baya cikin falo.
Monkey zaune a kan center table da ke gaban tangamemen gadon Ya Azeez, shi kuma Ya Azeez din zaune a gefen gado yana taba wayarshi
Shigowa ta ce ta sanya shi dagowa yana kallo na har na shigo cikin dakin sosai
“Ba ki da lafiya ne?” ya fara tambaya ta
Na jijjiga kai alamar eh.
“Me yake damun ki?” ya kara tambaya ta, “zazzabi ne.” na amsa shi.
Bai ce komai ba, illa taɓa wayar shi da yake yi. Kamar 2mns ya ce “Zo ki bude min wannan?”
Ya nuna min abun nan na lullube da ya shigo da shi
“Ko ba ki iya wa?” ya yi tambayar lokacin da nake takowa a hankali zuwa inda yake
“Zan iya” na, tabbatar mishi.
Na shiga yaye wrapping sheet din a hankali, har zuwa lokacin da wani hoto ta bayyana.
Na zubawa hoton ido ina kallo, cike da mamakin kwarewar mai zanen, saboda a kallo daya mutum ba zai dauka zane ba, sai ya jima yana kallo sannan.
Ban san lokacin da murmushi ya subuce min ba, wani farin ciki mara misultuwa ya ziyarci zuciyata, na zame kasa sosai na zauna ina shafa zanen dog din, da aka zana shi yana zaune, zama irin na karnuka, ya fitar da harshen shi, kamar a kira sunan shi ya taho.
Na dago kai ina kallon Ya Azeez shi ma ni din yake kallo, na mayar da kallona kan zanen dog, na kara kai hannuna ina shafawa a hankali. Yayin da zuciyata ta yi laushi, hawaye masu dumi suka rika gangaro min. Ni kadai na san yadda nake ji gami da mutuwar dog, musamman idan na tuna kashe shi aka yi da karfi ba mutuwar Allah ba
Na janye frame din zanen dog din gefe daya, ina kallon hoton da ke kasan shi.
Shi kuma zanen hotona ne, hannuna rike da sarkar wuyan dog, yayin da nake shanye da riga da wandon da ban san ma ina dasu ba, kila ko don me zanen his favorite dress is English wears I don’t know.
But Ni kaina na san sabbin kayan da ya sanya min din sun yi min kyau, musamman wani camvas dan ubansu da ya dora min, ga wata facing cap ta mata da ta karawa kwalliyar tawa kyau.
Cike da burgewa nake kallon zanen, na kuma dago kai ina kallon Ya, Azeez, still ni yake kallo.
Wani murmushi na saki mai dauke da siraran hawaye ina fadin “, sun yi kyau zanen sosai”
Bai amsa min ba, wannan ya sa na kuma janye shi gefe ina kallon zane na uku kuma na karshe.
Wanda ni da Ya Azeez muka zanta dog a tsakiya, a, wannan karon ma English wears din aka sanya min.
Na rika kallon hoton zanen yadda ya fita radau, muma muka fita kamar wasu turawa.
Ya Azeez na da baiwa sosai, musamman ta zane ina ma zai muhimmantar da ita, da ba karamin alkairi zai samu ba.
“Sun yi kyau?” ya katse min tunanina da tambayarshi.
Kai a rika jinjinawa fuskata dauke da murmushi ina kallon zanen tare da fadin “Sosai ma. Har sun gaji da kyau ma. Kai ne ka yi ko?”
Ya mike tsaye yana murmushin jin dadin yabawar da na yi wa zanen na shi amma bai ce komai ba
Na mike zuwa wurin monkey na aje mishi zanen dog ina fadin “Yo miss him?”
Yay ta kallon hoto tare da kai hannu yana tabawa, idan ya shafa sai ya dago kai ya kalle ni.
Na yi dariyar wawanci da yake sannan na ce “Don Allah Ya Azeez saura Monkey”
Ganin bai amsa ba, na kuma cewa “Don Allah!” a shagwabe na yi maganar
Daga inda yake tsaye ya ce “Wannan ke kika sanya na yi?”
Kai na girgiza alamar a’a, kafin na ce
“Wadannan zanen nawa ne?”
Ya daga min kai alamar eh, kafin ya ce “ki boye kar Aunty ta yi fada”
“a falonta ma zan sanya, na dog ne kawai zan kai dakina” na yi maganar cikin zallar farin ciki.
A haka na kwashi zanen na yi falo.
Kasancewar dama falo babu wasu hotuna, sai na Hammah guda daya
Bangon da ke kallon kofar shigowa na kafe hoton da muka sanya dog tsakiya. Saboda Ni a bangarena ya fi ko wane hoto kyau.
Wanda kuma nake tare da Dog Sai na sanya shi a bangon Tv, na yi tsaye ina kallon yadda aka kawata zanen.
“Ɗan baiwa!” na fada a hankali, har zuwa lokacin idanuna na kan zanen.
Monkey ne ya dawo da ni cikin hankalina, na mike ina fadin “Mu je waje, kar Aunty ta dawo ta same ka a falonta, ni da kai, da Ya Azeez din duk mu ci kaniyarmu.”
Bayan na saka shi cikin cage din ne na dawo falo, wani irin karfi nake ji, ji nake babu inda ke min ciwo, wannan ya sa na shiga kitchen don yin abincin rana.
Aunty ba ta dawo gidan ba sai karfe hudu na yamma zuwa lokacin Ya Azeez ya bar gidan.
Ni ce na taro ta, sosai nake son ganin reaction din ta bayan ta ga zanen da Ya Azeez ya yi.
Abin da nake fata shi ne ya faru, saka kafarta cikin falon ya yi daidai da dora idonta a kan hoton zanen
Baki bude ta ce “Waye ya kawo wannan?”
Na rika dariya kasa-kasa ba tare da na ce komai ba
Ta isa wurin hoto sosai tana kallo
“Ya yi kyau ko?” na tambaye ta.
Ta jinjina kai alamar eh, sannan ta dora da “Ya yi kyau sosai, amma ba za a aje min wannan abun a falo ba”
Cikin dariya nake kokarin ba ta amsa, shigowar da aka yi cikin falon ta dakatar da ni
Hammah ne, idonun shi a kan abin da muke kallo, sai da ya iso inda muke ne ya ce “Wow! Azeez ko? Kai zanen ya yi kyau.”
Cikin jin dadin maganar da ya yi na shiga gaishe shi, ya rika amsawa idanunsa a kan zanen yana ta yabawa.
Ni kuma dakina na koma, na basu wuri.
Ban jima da zama ba na jiyo Hammah yana fadin.
“Da safe na so mu yi magana Aisha, sai kuma fitar gaggawa ta same ni. Dama Ina son fada miki ne na Bandi kanen Adama yarinyar nan Maryam.”
A nawa bangaren ƙamewa na yi, yayin da a can waje na ji Aunty ta ce
“Bandi kuma! Yaushe suka fara nema da Maryam kuma?”
“Ai ya jima yana fada min yana sonta”
“Hammah!” Aunty ta fada cikin yanayin da ke nuna mamakin jin maganar shi.
“Yana da matsala ne Aisha, me ye matsalar Bandi din?”
“Ni ban san ko yana da matsala ko babu ba, amma wane irin baiko ne haka, yaushe rabon ma Bandi da garin nan ba ma gidan nan ba”
“Ku mata matsalarku kenan, ai kin san dai aiki ne ya rike shi a inda yake ba zaman banza yake yi ba. Kuma me ye maganar sai ya zo wurin ta, ke kam na je wurin ki ne na aure ki?”
“Wancan zamanin daban Hammah wannan kuma daban.”
“Duk daya ne Aisha” ya fada a fusace yana nufar kofa
“To karatun nata fa?”
Aunty ta kuma tambaya ganin yana niyyar fita.
“I don’t know! Kawai ina son ta yi aure nan da bayan sallah shi kenan”