Skip to content
Part 42 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Cike da mamakin maganar cikina na koma, in kalli kaina a madubi in tambayi kaina wai ina da ciki? Ko in shafa cikina in ce wai ina da ciki irin na haihuwa. Abun mamaki yake ba ni.

Sai kuma in tuna wai Ya Azeez zai zama Baba iko sai Allah.

Bai dawo gidan ba sai 8:30pm.

Shi ne yake fada min shirye-shiryen bude Plaza Hammah ta yi nisa, kuma sunan shi aka sanyawa Plazan DON A. Z kuma shi aka ba manager, Wai amma ba zai iya ba.

Sai a lokacin ne na gyara zama sosai ina fuskantarshi na ce “don me?”

“Ina son gyara exams din da na fadi ne, in karbi results din, Saboda inda na samu aiki sun ce min 1 year kawai suka ba ni in kawo result dina, kuma akwai albishir mai kyau bayan na kawo result din.”

“Wane irin albishir?” na kara tambaya hankalina a kanshi

“Za a kara min girma, sannan akwai scholarships na masters kyauta”

Kai na shiga jinjinawa kafin na ce “Duk da haka za ka iya”

Yadda yake kallo na ne ya sa na ce “Makarantar kam ba sai lokacin exam za ka na zuwa ba, sannan shi kanshi aikin Ya Azeez ai akwai lokacin tashi”

“Bar wannan maganar don Allah, ni fa ban san dorawa kaina sirgulla”

Dariya na yi mai sauti ba tare da na ce komai ba.

Tun da Ya Azeez ya dawo bai zauna ba, idan ya fita tun safe sai magriba yake dawowa, ba shi makaranta ba shi wurin aiki.

Ni ko irin ƴar shagwaɓar nan ta masu laulayi ba na yi, to ba ma ta ni yake yi ba, ina jin yana mantawa ma ina da ciki.

Da weekend ne kawai yake ɗan samun zama har mu fita ya koya min tuƙi, amma duk da hakan duk bayan kwana daya zai ce min Aunty na gaishe ni, alamun dai ya je wurin ta.

Don ni ba zuwa nake yi ba, Sai dai waya ko video call.

Yau asabar da misalin karfe biyar na yamma muka dawo daga wurin da yake koya min tuƙi, ni ce nake jan motar a hankali irin dai na ƴan koyon nan.

Tun da muka shigo layin gidanmu na hango motar Aunty, cike da tsokana ya ce “Yau kam ga Aunty ya za a yi kenan”

Fuska na kyaɓe kamar zan yi kuka hankalina kuma a kan tuƙin da nake yi.

Daga bayan motarta na yi parking, muka fito a tare da Ya Azeez.

Cike da sha’awa take kallonmu, na karasa kusa da ita ina murmushi lokaci daya kuma na mikawa Abdallah hannu.

Ga mamakina sai ya ƙi zuwa, amma da Ya Azeez ya miƙa mishi hannu sai ya je

Cike da mamaki na ce “Aunty har ya fara ƙiwa wai?”

“Ga alamu ma, bai san ki ba”

Murmushi na yi tare da fadin “Sosai ya yi girma Aunty ya kuma kara kyau”

“Ke ma ai kin yi girman kin kuma kara kyan”

Tafukan hannuna na sanya hade rufe fuskata ina dariya.

Daidai lokacin ne kuma Ya Azeez ya bude mana kofa, mu ka shiga Aunty na fadin “Biko na zo, Maryam almost wata hudu ba ki je inda nake ba, ko laifi na yi miki?”

Cikin sauri nake girgiza kai kafin na ce “Aunty me za ki yi min da zai hana ni zuwa wurin ki?”

Caraf Ya Azeez ya ce “Aunty in fada miki gaskiya?”

Na yi saurin mayar da kallo na zuwa kanshi, ina yi mishi alamun roko da idona

Aunty kuma ta ce “Fada min, ina jin ka”

Daidai lokacin muka shiga main falo

“Fada min na ce.” Aunty ta kuma fada tana kallon shi

Kamar zan yi kuka na ce “Aunty babu komai fa, shi ne idan na ce ya kai ni, Sai ya ce aiki ya yi mishi yawa.”

“Ga ki kuma ba ki san hanya ba?” Aunty ta tambaya idanunta a kaina

“Atoh!” cewar Ya Azeez cikin Salon tsokana

Na kuma marairaicewa ina ta neman abin da zan kare kaina, Aunty kuma na fadin ba ta yarda ba

Ya Azeez ya ce “Ki kalle ta tsab Aunty me kika gani?”
Ya yi maganar lokacin da yake cire hannun Abdallah a bakin shi

“Tun da na iso na gani ai” Aunty ta amsa cikin dariya

Shi ma gajeruwar dariya ya yi, wacce ke nuna yana cikin nishadi.

Aunty kuma ta ce “Wato kai ne mara kunya ko? Allah Ya shirye ka Azeez”

Ni dai tuni na yi gum da bakina, jin sun saki waccan maganar ne ya sa na gaishe ta, na kuma tambayi Hammah ta amsa min yana lafiya.

Abun taɓawa na kawo mata gami da ruwa, ruwan kaɗai ta sha, ta ce ya ishe ta.

Kafin mu ka shiga hira, bayan Ya Azeez ya bamu wuri ne ta ce “Babu dai wata matsala ko?”

Na jijjiga kai alamar eh.

“Ina ke miki ciwo yanzu?”

Na ɗan yi shiru kafin na ce “Babu ko ina”

“Ma Sha Allah! Ki rika yin komai cikin nutsuwa kuma a hankali saboda tsautsayi”

Kan na kuma dagawa alamun na fahimta.

Ya Azeez kuma ya ɗora Abdallah a kan cinyata ya juya zuwa dakin shi

“Ki ce hannu ya fara fadawa, har kina iya tuƙawa da kanki”

Cike da jin dadi na amsa mata, kafin na dora mata irin challenges din da nake fuskanta wajen tukin, da kuma abin da yake ba ni wuya, ita kuma tana kara min haske

Sai da ta yi sallahr magariba sannan ta tafi.

Zuwanta Sai ya ba ni wani Nishadi na musamman, na rinka jin zuciyata fari ƙal.

Cikin wata uku Hammah ya bude plazan shi, gini ne na zamani mai dauke da kayan duk da kake so, kayan zaƙi, na sanyi, juice, atamfofi, takalma, yadika, shadda har kayan kitchen.

Ya zuba ma’aikata shi ke zama da rana Ya Azeez kuma da yamma zuwa dare.

Yanzu kam komai ya canja babu shiririta, saboda babu lokacin yin ta, ko wane lokaci yana da abun yi, safe aiki ko makaranta idan yana da paper, yamma kuma kasuwa.

Dakwai bambancin rayuwa ta wajen ci ma, da kayan sanyawa, yanzu kam sai manage, saboda hanyar samun kudin ta bambanta da ta baya.

Yanzu idan aka ce za a yi waccan rayuwar karyar to komai sai ya lalace, ciki har da plazar da kusan mu dukkanmu da ita mu ka dogara.

Cikina na kai wa wata takwas na koma wajen Aunty, inda ita ma take fama da laulayi, ita kam laulayi ba ya yi mata da wasa, sosai take ficewa hankalinta, duk da tsohon cikina haka nan nake fama da hidimar gidan.

Kamar yanzu ma da agogo ya nuna karfe biyar daidai na yamma, zaune nake a farfajiyar gidan a kan tabarma, ina kallon Abdallah da yake wasa da monkey a tsakar gidan, lokaci zuwa lokaci wasan nasu ya kan sanya ni nishadi

Sannan in rinka jin ina ma ace Abdallah yarona ne, ni ce na haife shi yake ta wasan shi haka

Sosai yaron ke burge ni, fari tas kyakkyawa, komai na Abdallah mai kyau ne, musamman gashin kanshi da yake kwance baƙiƙƙirin kamar an fenta.

Idanuna na dauke zuwa gate inda nake jin horn, ko ba a fada min ba na san Ya Azeez ne, ban dauke idonun ba har motar ta shigo, bayan ya gama parking Hammah ne ya fara fitowa, Abdallah kam ya ruga da gudu zuwa wajen shi ya makale shi

Yadda suke ta dariya ni ma sai na tsinci kaina ina darawar.

“Sannu da dawowa Hammah” na fada lokacin da suka zo saitina

Ya amsa hade da fadin “Ba wuta ne?”

“Akwai, kawai dai iskar wajen nake so”
Zuwa lokacin tuni ya kusa hawa kan entrance, lokacin ne kuma Ya Azeez ya iso inda nake

Plastic chair din kusa da ni ya zauna yana fadin “Na gaji”

“Na gani” na fada cike da kulawa kafin na dora da “Sannu Allah Ya albarkaci nema”

“Amin” ya amsa kafin ya ce “Aunty fa?”

Dama na yi mamakin yadda har ya zauna ba tare da ya tambaye ta ba, tun da Allah Ya sa na dawo, kuma zai shigo gidan bai gammu tare da Aunty ba sai ya ce tana ina.

Akwai wata soyayya mai karfi da shakuwa a tsakaninsu, duk da basu shan inuwa daya, saboda na tabbata idan zai shiga yanzu sai sun yi fada.

Na katse tunanina da fadin “tana ciki”

Baki ya tabe kafin ya ce “Aunty dai ba za ta hak’ura da cikin nan ba ko, tsakani ga Allah kina haihuwa tana haihuwa, Allah ba na jin dadi”

Murmushi na yi kafin na ce “Ita kuma tana son abun ta, Hammah ma yana so, daga kai sai Abdallah kawai kun isa, ai mu ma muna son ƴar mace”

“Ba sai ki haifar mata ba”

“Da namu ai gara da nawu”

“Ke ce ke zuga ta kenan?”

Dariya na yi mai sauti kafin na ce “A’a”

File din da ke hannunshi ya bude haɗe da fiddo wata takarda ya mika min

Ido na fitar baki a washe bayan na gama fahimtar wace irin takarda ce na ce “Kai Ma Sha Allah. Gaskiya na taya ka murna, after all struggles result dai ya zo hannu.”

Murmushi ya yi yana fadin “Gaskiya kam na ci wuya, amma dai bukata ta biya, yanzu haka har na tura result din wurin directornmu”

Na waro ido tare da fadin “Ba dai wanda ka ce idan result naka ya zo hannu ka tura mishi ba, wannan na Kasar wajen, ya ma sunan Kasar?”

“Germany!” ya yi saurin tarar numfashina

“Ba Aunty ta ce ba ta so ba?”

“Ba ta ce ni kadai take gani ba? Yanzu ga Abdallah nan, ga kuma wani a ciki”

Shiru na yi ba tare da na ce komai ba, saboda ni kaina ba na son abin da zai daga ni da garina.

Ya miƙe tsaye hade da mika hannu ya kamo nawa hannun, na mike dakyar, ya sake hannun nawa kafin muka jera, yana kara fada min irin farin cikin da yake ciki gami da karɓar result din, a haka muka karasa cikin falo, daidai lokacin da Hammah da Aunty suke sakkowa.

“Aunty!” Ya kira sunan ta cikin murna

Ita ma cike da farin ciki ta ce “Ba sai ka fada min ba, an ri ga ka, kuma Ina taya murna, Allah Ya albarkaci abin da aka karanta” ta karasa maganar tare da karbar result din

Bayan ta duba ne ta ce “Anya Azeez ba cin hanci ka bayar ba, second class upper”

Hammah ya fashe da dariya yana fadin “Azeez ai yana da kokari Aisha, ki bar shi dai da shiririta”

“To Allah Ya sa albarka”

“Amin.” ya amsa sannan ya dora da “Na tura document nawa Germany din fa”

“Dama kana jira ne?”

“Aunty scholarship in yi degree ga aiki, ga wurin zama, ta ya zan yi wasa da wannan damar. Ai na yi hankali na daina wasa da dama ta”.

“Idan akwai wurin zaman Maryam Allah Ya kiyaye hanya, amma fa idan babu wurin ta, gaskiya ba za ka je ba”.

“Aisha sarkin son kai” Hammah ya fada cike da tsokana, kafin ya nufi kofar fita, ita kuma ta bi bayan shi tana fadin “Ni gaskiya nake fada fa, amma sai ku ce na faye rigima”

Ni kuma bayan Ya Azeez na bi zuwa ɗakinshi. Kayan jikinshi ya fara ragewa, sannan ya zauna kusa da ni hade da karɓe result dinshi da yake hannuna ya ce”Ba kya gajiya da kallo ne? “

“Imagining nake Ina ma nawa ne? Ko yaushe ni ma zan rike nawa haka oho?”

“I don’t know, but may be soon, Ni fa karatun mace bai wani dame ni ba, na fi son zamanta a gida”

“Ya Azeez da bakinka kake fadin haka, ba ka ga amfanin ilmi a kan Aunty ba” na yi saurin fada

“Na ga ma rashin amfaninshi a kan Aunty Adama”

“Haba wannan ai ya wuce”

Ya mike tsaye tare da fadin “Bai wuce ba gaskiya kullum ina takaicin yadda na ɓata lokacina can baya a banza. Duk set dina sun yi min nisa”. Yadda ya yi maganar ne ya sanya ni fahimtar yana jin zafin abun.

A tausashe na ce “kana hanyar taras dasu, ina jin a jikina ma za ka iya wuce wasu su.”

“Na ji ba na son haɗa mata biyu sam, saboda kar a lalata min rayuwar yarana ni ma”.

Karon farko da na ji ya yi wata magana da ta shafi abun da ke cikina kai tsaye.

Ba wai ba ya son cikin ba ne, bai taɓa nuna min hakan ba, komai yana yi, amma idan ban ce ba, ko Aunty ba ta ce ba bai yi. Ba ruwanshi, shi kamar bai damu da yara ba. Abdallah ma don yana shige mishi ne, amma ina lura da shi idan zai shigo gidan kafa goma bai ga Abdallah ba ya tambayar yana ina. Amma idan Aunty ce bai gani ba, ya yi ta tambaya kenan wata kan wata.

Yadda nake kafe da idanu ne ya sa ya ce “Me ya faru wai”

“Ji na yi ka ce yaranka, ashe kana son yara?”

Cikin rashin muhimmantar da maganar ya ce “I don’t know yet” Daga haka ya wuce toilet.

Watana ɗaya da ƴankwanaki ni ma na sako Baby boy dina kamar Ya Azeez bayan matsakaiciyar naƙuda, Aunty ce ta karɓi haihuwar a gida, har mu ka gama ba ta fadawa su Hammah ba, wai za ta yi musu bazata.

Misalin karfe shidda na yamma kuwa Ya Azeez ya shigo gidan, ina jin Aunty na tambayarshi ina ya baro Hammah, ya amsa ta da ya baro shi tare da baƙi.

Bai hauro saman Aunty ba sai bayan minti arba’in da da dawowarshi da alama sai da ya yi sallahr magariba, hannunshi riƙe da Abdallah ya turo kofar

Ya sake hannun Abdallah cike da mamaki yake kallo na lokacin da na ke ba Baby nono.

Tsawon lokaci bakinshi a bude ba tare da ya ce komai ba, ni da Aunty ne kawai muke murmushi.

“Ta haihu ne?” Cike da mamaki ya yi tambayar

“Ga zahiri ma” Aunty ta amsa shi

“Haihuwar ba wuya ne Aunty?” Ya yi tambayar a lokacin da yake karasa shigowa cikin dakin sosai.

Ya ɗora da “Abdallah yana ta son fada min, amma ban gane ba, ban iya yaren shi ba”

Ya kai karshen maganar a lokacin da nake mika mishi baby, ya yi saurin ja baya yana fadin “Ban iya dauka ba”.

Aunty ta zaro ido cike da mamaki tare da fadin “Au! Wai har yanzu ba ka iya ɗaukar Babyn ba, ina ta jira zuwanka na ce wannan kam ai ka dauka”.

Fuskarshi cike da farin ciki ya ce “Allah ban iya dauka ba.” Wayar hannunshi ya miko min yana fadin “Yi wa Babyn picture, mace ne wai ko namiji”.

Dariya Aunty ta yi kafin ta ce “Wannan yaro ya mori uba, Allah Ya raya” ta kai karshen maganar hade da ficewa daga dakin

Shi kuma ya dauko sosai ya sumbaci goshina yana fadin “Sannu, babu inda yake miki ciwo?”

Kai kawai na daga ba tare da na ce komai ba.

Gefena ya zauna yana fadin “Ɗan bude min fuskar shi sosai”

Na yi kamar yadda ya ce, ido ya zuba mishi kafin ya ce “Ikon Allah! Yau ni Abdul’azeez, DON A-Z nake da yaro na kaina. Ban taɓa wannan tunanin ba, kafin wannan lokacin, Alhamdulillah Allah Ya raya shi bisa sunnah. Hammah ya samu takwara”.

Jin ban ce komai ba, ya ce “ɗaukar min hotonshi, su Nasir zan turamawa ko sa kara nutsuwa saboda yanzu mun girma”.

Hotuna masu kyau na yi mishi, shi kuma ya sauka zuwa ƙasa, Sai a lokacin ne Aunty ta yi ta kiran mutane tana fada musu, ni ma na kira Maman Comfort.

Hammah kam ba ƙaramin murna ya yi ba, shi ya yi wa yaro hudu ba da Muhammad.

Su Aunty Huzaima sai kira suke yi cike da farin ciki suna barka, wanshekare da safe mu ka fara karɓar baƙi ƴan barka, ciki har da Maman Comfort, ƙawayen Aunty da ƴan cikin unguwa da ake kirki.

Misalin karfe shadaya Ya Anwar, Mubarak da Ya Nasir suka zo ganin Baby dauke da akwati biyu cike da kayan sanyawa na yara masu kyau.

Hotuna kam da videos ranar sun sha shi, don har sai da suka taso Ya Azeez daga wurin aiki, wai ya zo za su yi hotuna.

Aunty tai ta tsokanarsu wai abu ya zo ga ma’iya kukan aure da sallallami.

Ni kam dama tun da muka gaisa na koma dakin Aunty.

Bayan sun gama hotunan ne suka shiga dakin Ya Azeez.

Anwar ne ya fara cewa “Har yanzu ban gama mamakin wai Azeez ya yi aure ba, Sai ga shi matar har ta haihu. A cikinku waye ya yi tunanin Azeez zai riga mu aure ne, mutumin da ko tsayayyar budurwa ba shi da”.

Mubarak ya yi caraf da fadin “Ni abun da ya fi ban mamaki har yanzu shi ne wai Maryam ce matar”.

“Kai ko ni, ɗan iska ya, yi min kutse” Nasir ya fada yana kallon Azeez.

“Kai ma sai ka kutsa ma wani ai”.

“Yo wa? Ni yanzu aure zan yi wlh, don Allah idan akwai mai hankali a cikin danginku kamar Maryam ina so”.

Azeez ya bude ido alamun mamaki tare da fadin “duk ƴanmatanka.”

“Kai share da batun ƴanmatan nan, duk ƴan iska ne”.

“Ai idan za ka kakkaɓe zuciyarka ka yi aure kawai malam ka kakkaɓe, saboda zina bashi ce, idan har ka yi da ƙanwar wani, yayar wani, ƴar wani, matar wani, uwar wani dole kai ma sai an yi da taka. Ya fi sauki ma ayi da matarka a kan ƴarka abun zai fi zafi” Cewar Anwar.

“To kai kuma yaushe ka koma wa’azi?” Mubarak ya tambaya yana kallon Anwar

“Tun da na fara jin wani labari, a wata YouTube channel”

“Labari kuma? ” Nasir ya tambaye shi shi ma, kafin ya amsa kuma Azeez ya ce “Yaushe kuma ka fara sauraron labari?”

“Ranar ne na shiga YouTube, na ci karo da wani labari wai KAMATUDDEEN na fara sauraro, yanzu dai har jira nake yi su yi update, kuma tun da na ji wannan labarin na yi alkawarin ba zan kara aikata zina ba”.

“Ya labarin yake?” Cewar Nasir

“Labarin cike yake da sarkakiya, amma jigon labarin dai a kan zina ne, da yadda zunubin ta yake naso har ta kai ga wanda ya aikata shi. Na rasa wane ɓangare ne ya fi taɓa ni ma a labarin. Bangare daya dai akwai wata yarinya ko ya ma sunanta, to diyar malamai ce irin na zauren nan basu fita ko ina, ko hira irin na saurayi da budurwa basu yi. Amma a haka aka yi wa yarinyar nan ciki har ta haihu, ashe kaddarar ta faru da ita ne saboda mijin da za ta aura ya taɓa aikata zina da wata matar aure. Ita ma matar auren abun ya faru da ita ne saboda mahaifinta ya taba kusantar zina da wasu matan. Sannan kuma mijin da za ta aura a gaba shi ma ya taɓa aikata zina. Kuma abun mamaki ku san a gaban shi aka aikata zina da matar, ya kuma ji a duniya babu wacce yake so sai ita, ba karamin kudi ya kashe ba wajen nemanta”.

“Ɗan wahala” Nasir ya fada cikin taɓe baki.

“Jarabawa kawai, ya yi da ƴaƴan wasu, shi ma an yi da matar shi, kuma duk da ya sani hakan bai hana shi wahala a kanta ba”.

“Ba ka iya bayar da labari ba da Allah. A ina zan samu labarin?” Mubarak ya fada yana kallon Anwar

“Application na Bakandamiya Hikaya ko you tube channel nasu”.

“Zan nema” ya fada hade da mikewa, su ma, duk sai suka mike zuwa kofar fita.

Tun ana gobe suna gidanmu ya fara cika, ƴan Minchika da ƴan Gembu ga kuma su Aunty Karima da yaransu

Ni kaina sai nake ji na cikin Nishadi, Ranar suna kam na samu gifts wasu ma ni ban san su ba, fans din su Ya Azeez ne, aka yi taron suna lafiya aka gama lafiya.

Washegarin suna Ƴanminchika suka wuce gida, saura su Aunty Karima wadanda sai da aka kara yin zumunci sannan suka tafi.

Gida ya koma kamar da Aunty za ta fita aikinta, Ya Azeez da Hammah kasuwa Abdallah makaranta. Sai ya kasance ni kadai da Muhammad (haka ake kiran shi, saboda Hammah ya ce bai so a ɓoye)

Na haihu da wata daya uppern Ya Azeez ta fito, amma zuwa Canada saɓanin Germany da mu ka yi expecting, kuma wata biyu kacal suka ba shi ya tattara duk abin da suka rubuto suna bukata ya taho dasu

Addu’ata Allah Ya sa Aunty ta haihu kafin lokacin.

Ya Azeez ya shiga busyn tattara takardu, Aunty har tsokanarshi take yi ta ce “Azeez idan an fada min za ka rage gayu zuwa haka zan ce karya ne”

Murmushi yake yi kafin ya ce “Ina kokarin neman abun gayun ne Aunty.”

Cikin sati biyu ya hada duk abin da ake bukata, ya zauna zaman jiran lokaci.

Lokacin da na yi arba’in saura sati biyu tafiyarmu, shi ya sa ma, ban koma gidana ba, kawai na yi zamana a dakin Ya Azeez.

Shi kuma dama mace ba wani damuwarshi ta yi ba, zai iya yin sati biyu ba tare da ya bukaci mace ba, Sai dai idan ke ce kika kawo kanki. Bare yanzu ma da hankalinshi kaf yana a tafiyar nan, ina jin yana kosawa gari ya waye, sannan wuni yana yi mishi kadan saboda hidimomin shi.

Yau ma sai 10pm ya shigo gidan, lokacin zaune nake ina ba Muhammad nono da ya ƙi bacci.

Bayan na yi mishi sannu da zuwa ne ya ce “Wai shi dama baya bacci, haka kuke fama da kina kwana a dakin Aunty?”

“Watarana yana yi”

Ya duko kamar zai dauke shi, wannan ya sa na mika mishi shi, ya yi saurin ja baya yana fadin “Sai ya kara girma”

“Wai don Allah me kake jin tsoro ne?” Na fada cike da jin haushi, saboda abun ya fara damuna, tun da aka haifi yaron bai taba daukar shi ba, Sai dai ya leka fuskarshi

“Ya yi taushi da yawa, wannan taushin ne ba na so”. Haɓa na rike alamun mamaki ba tare da na ce komai ba.

Ya aje fasfo din tafiyarmu a gefena yana fadin “Fasfo din nan ya tsayar da ni”.

Na shiga jujjuyashi saboda ni dai ban gane komai ba, bayan na gama kallo na ajiye shi a gefe.

Daidai lokacin ya fito toilet.

“Kana bukatar wani abu ne?” Na tambaye shi idanuna a kanshi.

“Only tea” Ya amsa min.

Na tashi na hada mishi tea din, yana sha ne ya ce “Yau aka yi baikon Mubarak.”

“Ma Sha Allah, Allah Ya tabbatar da alkairi, saura su Ya Anwar”

“Soon in Sha Allah”

“Allahu Ya sha.” Na amsa mishi

Hira kadan muka taɓa kowa ya yi bacci.

Ana saura kwana uku mu tafi Aunty ta haihu, wannan karon ma namiji, har ga Allah na so ace mace ta haifa, amma a hakan ma na yi farin ciki, saboda fatan d nake yi kenan ta haihu kafin mu tafi, kuma Allah Ya karɓi addu’ata.

Sai na koma addu’ar Allah Ya sa a daga tafiyar nan sai an yi suna, duk da dai ta ce ba taron sunan da za a yi, amma dai ina son a yi bakwai din a kan idona kuma a gabana

Sai dai addu’ata ba ta karɓu ba, ranar Laraba da misalin karfe 2 na rana aka yi mana rakiya zuwa airport inda jirginmu zai tashi 2:30pm

Duk yadda na so da daurewa kar in yi kuka, hakan bai faru ba, lokacin da jirginmu ya tsaya kuma aka fara kiran passengers jikin Aunty na fada hade fashewa da kuka, ta shiga bubbuga bayana tana fadin “In Sha Allah tafiyar nan Maryam alkairi ce, na san ba za ki ji dadi ba, ni ma nan ba na jin dadin to kar ki kara kashe min jiki. A duk inda kike ki ji tsoron Allah, kada shiga cikin wasu mutane ya sa ki canja dabi’un ki, a can dai ba ki da kowa sai Allah sai Azeez, to ki yi kokarin samar da zaman lafiya a tsakaninku, daga lokacin da kika ga ba daidai ba ki sanar da ni, idan daidai din ba ta samu ba, zan tura miki kudi ko nawa ne ki taho gida. Mun yi magana da Azeez a kan karatunki, kuma ya ce Sha Allah zai bincika makarantar da ta dace da ke, mu da shi zamu hada hannu wajen ganin kin yi karatu kin ji ko”

Na jijjiga kai ina dauke hawayena, Hammah ma nasiha ya shiga yi min, har zuwa lokacin da aka kira sunanmu, zuwa lokacin kam kuka na kara fashewa da shi, Sai da Ya Azeez ya kama hannuna kafadarshi saɓe da Muhammad muka rika haura matakalar shiga cikin jirgin

Yadda Abdallah ke dago min hannu sai ya kara narkar min da zuciya, har jirgin ya tashi kuka nake yi.

Bayan ya daidaita cikin sararin samaniya ne Ya Azeez ya janyo ni zuwa jikinsa a hankali ya ce “Aunty tana sonki Maryam, Allah Ya sani karfinta mu ka fi ni da Hammah har dauke ki zuwa wata ƙasa. Na yi mata alkawarin zan kula da ke fiye da yadda take son a kula da ke. Ki taya ni addu’ar yin hakan. Na san ban iya soyayya ba, amma zan sanya ki farin ciki ta yadda ba za ki yi kewar gida sosai ba. “

Hawayena na dauke a hankali kafin na ce” Ni ma ina son Aunty, zan iya fansar da rayuwa ta saboda ita, ita din ta yi min abin da dukkan uwa za ta yi wa ƴarta, ina fatan ranar da ni ma zan yi mata wani abu, da zai sanyata farin ciki “

“Za ki yi mata sha Allah “

“Allah Ya sa “

“Amin ” Ya amsa hade da kara kwantar da kaina bisa gefen kirjinshi

Alhamdulillah!!!

Karshe.

<< Da Magana 41

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×