Skip to content
Part 1 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Bismillahir-Rahmanir-Raheem

Garin Sandamu, Daura

Kangiwa junction, Fatima ce tsaye hannayenta rungume da atamfofin da ta karbo a gidan kawar mamanta. Sosai hankalinta yake a tashe, musamman idan ta daga kai ta kalli hadarin da ya hadu ya yi bakikkirin, a ko wane lokaci zai iya sakko da ruwa. Ganin ba ta samu mashin ba, ya sa ta fara takowa da kafa, har zuwa kan hanyar da ta fi Katsayal. Amma dai har zuwa lokacin ba ta samu abun hawa ba, ga ruwa ya fara sakkowa.

Ba ta da zabi da ya wuce kodai ta ci gaba da tafiya, ko kuma ta shiga wani gida ta fake har zuwa daukewar ruwan saman. Ta waiga dama da hagunta, babu wani abun hawa a kusa, hakan ya sa ta tsallake hanyar cikin sauri, ta gangara zuwa kan santar da za ta sada ta gidansu da ke kofar yamma. Lokacin da take kokarin shiga wani gida ne, motar Jamil ta gangaro a hankali.

Fatima ta lumshe ido cike da jin dadi, don ta san wahalarta ma ta zo karshe. Amma abun mamaki, gani ta yi Jamil din ya wuce ba tare da ya tsaya ba, duk da hada idon da suka yi. Ta bi motar da kallo cike da kunar zuciya, wani hawayen bakin ciki da bacin rai ya gangaro mata. Matse zannuwan ta yi a kirjinta, ta ci gaba da tafiya, ba tare da ta damu da ruwan da yake sauka kamar da bakin kwarya ba. Lokaci zuwa lokaci ta kan kai hannunta kan fuskarta, tare dauke hawayen da ke bin kuncinta.

Tafiyar mintuna goma ne ta kawo ta gida, zuwa wannan lokacin ta jike sharkaf ita da kayan da ke hannunta. Motarshi a kofar gida ya lullubeta tamkar sabuwar amaryar da ke jiran sayen baki. Kallo daya Fatima ta yi wa motar hade da kau da kai gefe, wani kululu ya tsaya mata a zuciya, ji take kamar ta cinna wa motar wuta in ya so kowa ma ya rasa.

Shigowarta ya tsayar da Mama da ta ke juye ruwan saman da ta tara cikin randa, fuskarta cike da mamaki ta ce, “Yanzu a cikin ruwannan kika taho Fati, ba kya iya samun wani guri ki fake sai ya dauke sannan ki taho?”

Fatima ba ta yi magana ba, wucewa kawai ta yi cikin daki, hade da jibge kayan hannunta a kan kujera, lokaci daya kuma ita ma ta yi wa kanta mazauni.

“To wai kukan na mene ne?” Mama ta tambaya tana kallon Fatiman.

“Yaya Jamil ne.” Ta ba ta amsa cikin muryar kuka.

“Ya yi me?” Mama ta kuma tambaya.

“Yana fa kallona ruwan sama yana dukana, ko ya tsaya ya dauke ni, ni kuma kawai sai na taho cikin ruwa, ya ga ko zan mutu” Cewar Fatima tana goge hawayen fuskarta

“Mtsww!” Mama ta ja tsaki sannan ta ce

 “Aikin banza wankin tifa. To yanzu wa kika yi ma wa? ” ba ta jira amsarta ba ta dora

“Ni da ke, kin dama mun salalar tsiya, zannuwa sabbi kin jike mun su jagab da ruwa. Yanzu ta ina zan fara? Zan warwaresu in shanya su bushe ko ya zan yi?”

Shiru Fatima ba ta yi magana ba, idan ka dauke fuskarta da ta yi kicin- kicin da ita.

“Ke ba ‘yar fari ba, amma sokancinki ya fi na ‘ya’yan farin ma. Da bai tsaya ya dauke ki ba ki shiga wani gidan ki fa…” Shigowar Jamil din ce ta katseta

“Me ya sa ka wuce Fatima a hanya kana ganinta ba ka dauke ta ba?” Mama ta jefe shi da tambayar hade da kallon fuskarshi.

“Amma dai ba wannan Fatin ba ko? Idan ita ce, to ni dai ban ganta ba, wane abu daya zan yi, tuki ko kalle-kalle? Ita da ta ganni me ya hana ta tsayar da ni?”

“Yaushe za ta tsayar da kai tana ji da girman kai. Ai ga shi nan ni ta jawo mun asara.”

“Wallahi-Wallahi Mama ya ganni ai har hada ido mu ka yi da shi.” Cewar Fatima tana kumbura baki.

“An fada miki da ido ake gani? Hankali ne ke gani idan ba ki sani ba.”

“Mama sam ba kya son laifin Yaya Jamil, amma wallahi ni na san ya ganni.”

“Mama, kyaleta, na ganta ko banganta ba ya rage nata.” Cewar Jamil yana kallon Maman.

“Ai ni dama na san kana kallona ka wuce.” Murya kasa-kasa ta yi maganar hade da murguda baki.

Mama ce ta kaiwa bakin duka, cikin rashin sa’a ba ta samu Fatiman ba. Hakan ya sa Fatiman saurin tashi hade da bangaje Jamil da yake tsaye ta fice da gudu.

“Ka ga waccan yarinyar me tsawo kamar ramar rani, watarana uku zan karyata saboda rashin kunyarta. Ita gani take yanzu daidai take da kowa.”

“Ki daina bata ranki da ita, kuruciya ce ke da munta.” Cewar Jamil a lokacin da yake kokarin zama.

Fatima kuwa daki ta shige ta fada kan katifa, hade da fashewa da kuka.

Kiri-kiri Mama ke fifita Jamil a kan kowa a gidan, abin da yake so shi za’a yi ga shi sam baya laifi.

Ta yi saurin mikewa tsaye hade da tattara kayanta tana cusawa cikin akwati. “Gara in bar masu gidan ma kawai.” Ta fada a zahiri.

Har ta fita gidan janye da akwatinta ba wanda ya ganta.

Ba ta damu da yayyafin ruwan da ke sauka ba, don dama a jike take, kokari kawai take ta isa gidan hakimi inda Auntynta Hauwa ke aure.

Aunty Hauwa ita ce diya ta fari a gidansu Fatima, inda take auran Hakimin Sandamu, tana da yara tare abokiyar zamanta da suke zaune lafiya ba tashin hankali.

Auntyn Hauwa zaune a falo tana sanyawa yara kayan sanyi, Fatima ta shigo janye da akwatinta tana digar ruwa.

Aunty Hauwa ta zubawa Fatima ido cike da mamaki, daga bisani kuma ta tuntsire da dariya hade da yiwa Fatiman kirarinta.

“Birji- birji sallah kura ba ki gama ba kin kai rida, kura kyaci da gashi, Fatitti ana ba guri kina kafa daki, tunkiya uwar tambele ba ki san gari ba ke ce a gaba, shege- shegen bako ana so ka zo ana so ka tafi, Fatitti jikar Malam mai sayem fada da kudinta. Fatitti sissikar barkono ko an sissika ba a sheke ba. Kaza kanki da motsi yar gidam Alhaji Musa ko kudi kuna buga naku.”

Duk da ran Fati a bace yake, sai da ta wangale baki hade da rufe fuskata ta kuma ci gaba da kyalkyata dariya.

“Kada dama ruwa, kin dama can kin dawo nan kenan?”

“Hmmm! Mama ce da dan gaban goshinta, kin san ba ta son laifinshi. Wallahi yana kallona ruwan sama na dukana ya ki tsayawa ya dauke ni. Amma Mama sai ta dora mun laifi har tana niyyar dukana.” Cewar Fatima da ke tsaye hannunta rike da akwatinta.

Fitowar Hajiya A’i abokiyar zaman Aunty Hauwa ya hana ta Magana.

“A’ah Fati yar London yar secondary goyon gwamna, ana dambun nama Auntynta tana dambun naira, ranar auranki daga me jirgi sai mai mota ‘yan acaba duk ‘yan aike ne. Fati yar gidan Aunty Hauwa yanzu kike mutum yanzu ba mutum ba. Fatitti ba’a gayyarku biki, ko an ganyace ku a koro ku, saboda halin naku. Don halin da ba’a so shi za kui, ku doki uban mutum ku zo ku fada mai, idan yay gardama…”

“Bar ni haka Aunty, kar ki tayar mun da tsumi na.” Cewar Fati cikin dariya.

Su din ma dariyar suke yi.

“Me ya faru cikin ruwan nan?” Aunty A’i ta tambaya.

“Sai an zauna Aunty” cewar Fatima a lokacin da take jan akwatinta zuwa dakin Zainab.

Zainab kwance a kan katifa tana bacci, ba ta san duk abin da ke faruwa ba, har zuwa lokacin da Fatima ta cire kayanta hade da janyo zanen Zainab da ke kan kofa ta daura.

Daga bisani ta fita da kayan nata ta shanya. Har zuwa lokacin kuwa ana yayyafi kadan-kadan.

Shiga toilet din dakin ta yi, ta yi alwalla, sallaya ta hau don gabatar da sallahr la’asar.

Bayan ta idar ne ta dakawa Zainab duka hade da fadin, “Ke tashi ki yi sallah.”

Zainab ta bude ido cikin yanayin bacci, tana kallon Fati, ba ta yi magana ba, sai dai ta mike ita ma ta dauro alwalla hade da fara sallah.

“Goggo Fati yaushe kika zo?”

Zainab ta yi tambayar hade da kallon Fatima bayan ta idar da sallah.

“Ban sani ba yar rainin hankali, ai na fada miki bana son Goggon nan ki kira ni da sunana mana. Amma Goggo kamar wata tsohuwa.” Cewar Fatima fuskarta a daure.

“Allah ya ba ki hakuri. Kin ga litattafai na aro mana, dama ina son kai miki ruwa ya sakko.” Zainab ta fada lokaci daya kuma tana daga kafitar da ke yashe a tsakar daki. Kwaso littattafan ta yi hade da mikawa Fati da ke zaune tana kallonta.

“Bankada, Rumaisa, Rayuwar Raihana.” Ta ambaci sunayen littafan, lokaci daya kuma tana jujjuyasu a hannunta.

” Wanne zan fara karantawa? Da alama duk zasu hadu, alkalamin manya ne ya yi aiki.”
Fati ta yi maganar hankalinta a kan Zainab.

“Ko wanne, ki zaba kawai.” Cewar Zainab lokacin da take gyara shimfidar katifa.

“Na dauki RUMAISA.”

“Ok to ni ba ni BANKADAR.” In ji Zaibab da take kokarin zama.

“Kin ga hankaklinmu kwance, yau an yi ruwa ba islamiya, mu sha karatunmu more.” Cewar Fati lokacin da take kallon Zainab.

Suka tuntsire da dariya, lokaci daya kuma suka haye kan katifar kowa ya fara karanta na shi.

*****

A can gidansu Fatima kuwa, ganin shiru Fatiman ba ta leko ba har Magriba, ya sa Mama lekowa dakin.

Kaya ne baja-baja a cikin dakin ta yamutsa komai, kuma ba’a akwatinta. Hakan ne ya nunawa Mama Fatima ta bar gidan.

“Oho! Ina zaune za ki dawo ki taras da ni, tulu ai shi ke yawo. Kuma mai madi ke talla, me zuma yana gida zaune. Yadda kika bar dakin haka za ki dawo ki same shi. Kyalle ba zan daga ba.” Mama ta fada hade da janyo kofar ta fita.

*****

Da misalin karfe hudu na yamma Fatima ce da Zainab sanye da kayan islamiya masu ruwan toka, doguwar riga da kuma dogon hijabi.

Tattaunawa suke akan littafin Rumaisa, wanda Fatima jikinta ya mutu likis da rayuwar Rumaisa a gidan aure.

“Wai ni kam Zainab, haka aure yake ne, kowa sai ki ji yana da matsala? Ni fa wani lokaci ina jin kamar kar in yi.” Cewar Fatima tana kallon Zainab.

“Mtsww! Da Allah ni kyale ni da wannan zancen Allah ya zaba mana ma fi alkairi, ni fa ban son tun kafin in yi abu a kashe mun jiki a kanshi. Kin ganni shi ya sa kawai abin da yake gabana shi nake yi ba ruwana da hangen nesa.”

Fatima ta yi shiru ganin sun iso kofar ajin nasu.

Suka duka tare da hada baki

“Malam ina wuni?”

Malam Mustafa da yake tsaye gabon allo sanye da doguwar riga irin ta maza (jallabiya) kanshi sanye da hula (taba ni ka ji hadisi) ya kare masu kallo kafin ya ce,

“Kullum sai kun makara ne?’

Caraf Fatima ta ce, ” Ba dai kullum ba Malam, sau nawa nake baro ka gidanmu ko gidan Aunty Hauwa in taho makarantar.”

Ya juyo sosai suna fuskantar juna ba tare da ya ce komai ba, ya yi masu alamar su je su zauna.

Ya san halin Fatima sarai, tana iya ba shi kunya cikin dalibanshi.

Bayan ya gama yi masu darasin Nah’wu “akwai mai tambaya?” Ya yi tambayar yana kallon ‘yan ajin.

Shiru ya ratsa, zuwa can kuma Maryam ta daga hannu.

“Malam wai ba kyau mace ta yi sallah da wando?”

“Eh musamman idan ana ganin surar jikinta…”

Daga hannun da Zainab ta yi ne ya dakatar da shi daga bayar da amsar.

“To malam mu da muke boarding school ai wando muke sanyawa, kuma malamanmu sun ce ba komai laluri ne.”

“To zo ki zauna ki bayar da fatawar mana.”

Cewar Malam Mustafa yana kallon Zainab.

Shiru ya kuma ratsa ajin, har zuwa lokacin da Fatima ta daga hannu.

“Ina jin ki.”

“Misali mutum ya mayar da irin rigar jikinka wando, shi ma din dai baya sallah?”

Duka ‘yan ajin suka kwashe da dariya, idan ban da Malam Mustafa da ya bata rai yana kallon Fatima.

“Fatima ke da Zainab, ku fita mun a aji na kore ku tsawon sati biyu.”

Fatima ta zaro ido kafin ta ce,

“Malam da gaske nake fa, Zainab ce ta mayar da irin rigar wando.”

Ya daga bulalar hannunshi ya tsala mata cikin sa’a kuwa ya same ta, hakan ya sa ya ci gaba da dukanta, har zuwa lokacin da ta fita daga ajin a guje, ko jakarta ba ta dauka ba.

Zainab da tuni ta yi waje tun lokacin da taga irin dukan da Malam Mustafa ke yi wa Fatima, ta tsaya can nesa tana jiran isowarta.

Allah ya isan da Fatima ta yi ya fi cikin kondo kafin su isa gida.

Ganin lokacin tashi bai yi ba, ya sa Aunty Hauwa tambayar,

“Har an tashi daga islamiyar?”

Sai a lokacin Zainab ta tuntsire da dariya, tana kalllon Fatima. Dariya take yi sosai wadda har ta kasa amsa tambayar Aunty Hauwa. Haushi ne ya sa Fatima diddirkawa Zainab lafiyayyun dunduna tana fadin,

“Wallahi Zainab zan yi miki rashin mutumci yar rainin wayau kawai.”

Ganin basu da niyyar amsa tambayarta sai kawai ta shiga harkokinta ta kyalesu.

*****

Bayan sallahr isha’i Fatima ce kwance a babban falon gidan hannunta rike da littafin ‘Rayuwar Raihana’ tana karantawa. Tana jin sallamarshi amma ba ta amsa ba haka ba ta motsa ba. Shi ma kallo daya ya yi mata, a daidai lokacin da yake neman gurin zama. Shiru ya ratsa falon har zuwa lokacin da Hajiya A’i ta fito.

“Mustafa, yaushe ka shigo? Sallah nake yi ban ji shigowarka ba sam wallahi. Kai Abdullahi!”

Ta kwada wa daya daga cikin yaranta kira, ya amsa ta umurce shi da ya kawo wa Mustafa abinci.

“Dazu su Fatima suka ce wai ka korosu daga islamiya, har tsawon sati biyu. Me ya faru ne?”

A karo na biyu kenan da ya daga idanunsa ya kalli Fatima. Ita ma shi din take kallo hakan ya ba kwayar idonsu damar haduwa.

Ta dan lankwasa harshenta kadan cikin bakinta tana juyashi, kafin ta janye idanunta a kan na shi.

Shiru bai yi magana ba, har zuwa lokacin da Abdullahi ya fito da tiren abinci.

Gabanshi ya janyo abincin, ya yi bismillah ya fara ci ba tare da niyyar amsa tambayar Hajiya A’i ba. Ita ma ba ta damu ba, ta san wani lokaci bai cika son magana ba. Hakan ya sa ta yi gaba ta ba shi guri. Lokaci zuwa lokaci Fatima kan saci kallonshi, ta murguda baki, kafin ta mayar da idonta a kan littafinta. Yayin da Mustafa ko sau daya bai saci kallon Fatiman ba, sosai ranshi yake bace a kanta, musamman yanzu da ya ganta sai yake jin kamar yanzu abun ke faruwa. Yana jin sauki ne kawai idan ya tuna ya yi mata dukan da shi kanshi sai da ya gamsu ya doketa.

“Sam! Albasa ba ta yo halin ruwa ba, dama an ce a gida dole sai an fitar da zakka, to a gidan su Aunty Hauwa dai Fatima ce zakkar da aka fitar. Yarinya ce kamar me aljanu, ba ta da tsoro ko irin yar alkunyar nan ta mata. Tsawon lokacin da ya santa ba zai iya kirga iya bugun da ya ga an yi mata a gabanshi ba. Shi ya sa sam baya shiga harkarta, duk da ba zai iya kirga ko sau nawa ita ta shiga ta shi ba.”

“Mtswww!”

Wannan karon a zahiri ya ja tsakin wanda ya sa Fatima waigowa ta kalleshi.

A wannan karon ma kwayar idonsu ta hadu, shi kanshi bai san lokacin da ya dalla mata harara ba.

Ba ta san lokacin da dariya ta subuce mata ba, ganin ya ta so cikin sauri zuwa inda take kwance, ya sanyata saurin sakkowa hade da fadin

“Don Allah don annabi ka yafe ni, don darajar iyayenka ka yi hakuri. Wayyo! Wayyo Allah Aunty Hauwa za’ a kashe ni. Aunty A’i ku fito za a kashe ni. Wayyo Allah mutanen gida ku fito za’a kashe ni.”

Mamaki ya cika Mustafa saboda ko yatsanshi bai dora a jikinta ba.
Kuma ba ta fasa zumduma ihun ba kamar wacce ake kwakulewa idanu dalilin da ya sa mutanen gidan fitowa suka taru a babban falon in da Fatima ke tsugunne a gaban Mustafa.

“Lafiya, me ya faru?”

Aunty Hauwa ta yi tambayar lokaci daya kuma tana kallon Mustafa.

Ya dan daga kafadunshi sama, “ku tambayeta.” Gama fadin haka ke da wuya ya fice cikin falon.

“Ya aka yi ne?’ Ta mayar da tambayar kan Fatima

“Dukana zai yi.” A takaice ta bayar da amsa hade da mikewa ta yi hanyar dakinsu.

Su ma kowa sai ya kama gabanshi suna dariyar abun da ya faru.

“Wai ke me ya faru ne?” Zainab ta yi tambayar lokaci daya kuma tana dariya.

Ita ma Fatiman tuntsirewa ta yi da dariya kafin ta ce, ” Dukana fa zai kara yi, dukan da ya yi mun dazu wallahi har yanzu gurin ciwo yake. Sai in kara yadda ya doke ni? Tabbb! Wallahi ba zan yarda ba, shi ya sa na tara mar jama’a.”

Tare suka kuma tuntsirewa da dariya.

“Gobe gida zan koma wajen uwata, ai ko mutuwa dai na jin kunyar idon mahaifa, kuma ma bai cika zuwa gidanmu sosai ba.”

“Ke dai kika sani.”

Cewar Zainab, da har yanzu take yar karamar dariya.

6:30 am ta fito janye da akwatinta.

Aunty A’i da ke kitchen tana duba yadda ‘yan aikin ke gabatar da abun karin kummallo, ta rike haba.

“Ina kuma za ki da sassafe?’

” Gidanmu.” Ta ba ta amsa

“Amma shi ne tun da safe haka, ko karyawa ma ba za ki yi ba?”

“Zan karya a gida.”

“To Auntynki ta san za ki tafi?”

“A’a ba ta tashi bacci ba.”

“Oh ni Aisha! Fatima Allah dai ya shiryeki. Ki gaishe da Maman.”

“Za ta ji.” ta fada yayin da take ci gaba da tafiyarta.

*****

Jamil ne zaune a kan wani dutse da ke jikin dakin Mama yana foolish na takalmansa.

Yayin da Mama ke tsaye a kofar kitchen, hannunta rike da karamin bokitin gasarar koko, da alama tana jiran tunkunyar ta tafasa ne.

Tattaunawa suke a kan aikin gonar da Alhaji Musa ya bayar da umarnin a fara kafin ya iso ranar jumu’a.

Shigowar Fatima janye da akwati ne, ya sanya su yin shiru, suka kuma zuba mata ido, har ta shige dakinta, ba tare da ta ce wa kowa kala ba, bayan sallamar da ta yi.

Mama ce ta tabe ba ki hade da fadin,

“Ai dama kyan d’a ya gagara gidan ubansa. Ni dama na san ina zaune za ki dawo ki same ni.”

Jamil dai bai yi magana ba, sai ma kwashe takalmansa da ya yi zuwa dakinsa.

Matar J 

Daga Karshe 2 >>

2 thoughts on “Daga Karshe 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.