Skip to content
Part 23 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Inna zaune a kan tabarma daga kofa, hannunta rike da kara, tana korar kaji, da awakin makota, a kan garin fara kal din masarar da ke shanye a tsakar gida.
A daidai lokacin Fatima ta shigo gidan dauke da sallama.

Sai da ta kwashe garin tass, sannan ta shiga cikin dakin Innan ta ajiye.

Lokaci daya kuma ta zauna, hade da daukar Hana da ta lokacin da ta shigo, ta mikawa Inna ita. kananan kukan nata dai take yi har sannan.

“Sai yanzu wai, har na fara tunanin Ummi tana dawowa ta bi ku, ko ni in lallaba asibitin in ji ko gado aka baku.”

Murmushi Fatima ta yi hade da kallon Inna “Tun dazu mu ka bar asibitin fa, muna gidan Aunty Hauwa ne.”

“Towooo! To me aka ce a can din? “

Zaman ta ta gyara hade da cewa “Ni an ce typhoid ce.”

“To ita Hana din fa?”

Ta dan yi shiru a kokarinta na kara yi wa Inna wata karyar

“Ita kuma ranar Laraba zamu koma, asibitin.”

“To basu fadi abin da ke damunta ba ne?” cike da kulawa Inna ta kuma jeho mata wata tambayar

“Matsalar a cibiyarta ne.”

Cike da tsoro Inna ta ce “Wace irin matsala ce a cibiya kuma ni ƴar nan?”

“Sai ranar larabar zamu sani.”

Cike da sanyin jiki Innar ta kuma cewa “To Allah ya kai mu larabar da rai da lafiya, Allah ya baku lafiya dukanku. Baban nata ya kira ne?”

“Eh, amma ya ce in yi hak’uri, zasu shiga aji karfe biyu sha Allah zai kira.”

“To ga abinci can fa.”

“Na ci a gidan Aunty, kila zuwa an jima” ta yi maganar daidai tana kwantar da Hana da ta yi bacci a kan gadon Inna.

Daga nan kuma ta fice daga dakin.

Kan kujera ta zauna, hade da zuba tagumi da hannayenta du biyun.

Tun lokacin da ta fito asibitin hankalinta yake tashe, ta rasa takamaimai wane tunanin za ta yi.

Tana son karatu sosai, musamman yanzu da take ganin da ace ta yi karatun kuma tana aiki, da basu shiga wata matsalar ba.

Iyakar tunaninta, ba ta gano hanyar bullewar karatunta ba, na farko dai ba kudi, idan ma da kudin to ya za ta yi da ciki da goyon da ke gaban ta.

Sannan rashin lafiyar Hana, likitan ya fada mata kudin aikin na Hana zai lamushe dubu hamsin.

A ina zasu nemo wadannan kudin? Ga shi duka a cikin kwana biyu ake bukatarsu.

Ba ta son neman taimakon yan’uwanta, ta san zasu yi mata, amma watarana sai ya zamewa Mustafa abun gori da ita kanta.

Alhaji kuwa so take ta jingina mishi karatunta. Sannan yana yi mata kokari sai, a shekarunshi bai kamata ace tana dora mishi dawainiya ba, kamata ya yi ace tana sauke mishi. Sai dai dole shi ne mafitar karatunta.

A yanzu dai ba ta da wani abu da za ta sayar ko Mustafa zai sayar , kayan daki sune kawai suka yi mata saura, Mustafa kuma sai gonaki.

Karar wayarta ne ya katse mata tunani, ganin Zainab ya sanya ta saurin dagawa.

Jikin Hana ta fara tambaya, Fatima ta tabbatar mata da aiki za a yi mata.

Sosai jikin Zainab ya yi sanyi, sai Fatima ce ma ke karfafa mata gwiwa.

Tana yanke kiran Zainab din na Mustafa ya shigo.

Bayan sun gaisa ya ce “Me ya faru a asibitin?”

Ba yanzu ne ta fara tunanin ta boye mishi ko ta fada mishi ba, Mustafa ba shi da komai yanzu sai damuwoyi, bai kamata kuma ta kara mishi wata ba.

Sai kuma wani bangaren na zuciyarta ya nuna mata rashin dacewar hakan, shi ne ya fi kowa cancantar ya sani, koda kuwa baya da wata mafita.

“Akwai matsala ne, na ji kin yi shiru?” Hankali a tashe ya katse mata tunaninta.

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali sannan ta ce “Ni dai an ce ciki ne da ni.”

“Ciki?” ya yi tambayar cike da mamaki.

Kamar tana a gaban shi, kai ta daga alamar eh.

“To Hana kuma fa?”

“Ita kuma cibiyarta ce ke nade yan hanjinta, shi ne suka ce kar ya wuce laraba ba a yi mata aiki ba.”

Tana dire maganar tata ya dora da fadin “Innalillahi Wa’inna Ilaihirraji’un!” Kalmar ya yi ta maimaitawa Fatima na sauraronshi, kafin daga bisani ya ce, “In sha Allah gobe zan zo.” bai jira cewarta ba, ya yanke wayar.

******

Kamar yadda ya fada hakan ne ya faru, misalin karfe 11am na safiyar Talata ya iso gidan.

Bai zauna ba, ya bazama neman kudi, duk inda yake tunanin zai samu bai samu ba, shi kuma yana jin nauyin tambayar Aunty Hauwa. Da dai ace kam ba Fatima yake aure ba, ita da Mama da kuma Alhaji sune farkon mutanen da zai fara tambaya.

Sai la’asar ya shigo gidan, ko abinci da Fatima ta ajiye mishi kasa ci ya yi, ji yake kamar dai gobe Hana za ta mutu idan ba a yi aikin nan ba.

Fatima da ta fahimci hankalinsa ya fi na ta tashi ta ce

“Tun da fridge din nan guda biyu ne, ba wani amfani muke da shi ba, me zai sa ba za a sayar da daya ba?”

Kallon ta kawai Mustafa yake yi ba tare da ya ce komai ba.

“Babu wata mafita Ya Mustafa bayan wannan.”

“Wai kina lura da komai naki yana neman karewa saboda matsalolina? Fatima wannan abun yana daga min hankali. Ba haka naso ba, so na yi ki ci gaba, ba wai ki dawo baya ba. Ba za a sayar da fridge din nan ba gaskiya, zan kara fita yanzu.”

Ya yi maganar hade da mikewa tsaye.

Ta yi saurin riko rigar shi” Ya Mustafa wannan fa duk wani tonon asiri ne, ka gama bude cikinka sannan ace ma abin da ka zo nema babu, a gaba haka za ka ji ana ta yawo da kai a gari, ni kuma bana son hakan, asirinmu rufe, a sayar da fridge din nan, idan ma kudin basu isa ba, a hada da generator, Allah zai bamu wasu a gaba. “

Ba karamar wahala Fatima ta sha ba, har Mustafa ya amince mata.

Zuwa magariba kuwa kudin fridge suka zo hannu 45k, dalilin da ya sa kenan suka hada da generator, shi kuma dakyar ya kai 25k.

Ranar Mustafa Sam bai yi bacci ba, abubuwa da yawa ne kuma suka hana shi baccin, tunanin aikin da za a yi wa Hana da halin da suke ciki, musamman yadda Fatima ke ta sayar da kayayyakinta daya bayan daya.

Ranar da yan’uwanta suka farga me zai fada masu, da wane idon zai kalle su.

Dole ne ya nemo mafita, kila kawai ya ci loan, ya mayar mata da duk abin da ta sayar, shi ne rufin asirin shi.

*******

Safiyar laraba misalin karfe tara aka shiga da Hana tiyata.

Fatima zaune a can nesa dasu Aunty Hauwa, duk yadda ta so boye damuwarta abun ya faskara, tun daga lokacin da aka fada mata damuwar Hana har zuwa yanzu hankalinta bai kara kwanciya ba.

Ko laulayin cikin ma ba ta jin shi, mantawa ma take tana da shi.

Mustafa ma yana wajen asibitin zaune da abokan shi biyu, jefi-jefi suke hira, kamar yadda su Aunty Ayyo ma ke yi jefi-jefi.

Ba a fito da Hana daga theater room ba, sai karfe sha biyu na rana.

Su Mama ne suka nufi dakin da aka kwantar da ita, Fatima dai ko motsawa daga inda take ba ta yi ba, bare ta bi su.

Ku san mintuna ashirin, suka fara fitowa, kowa na fadin albarkacin bakin shi.

Inna ce ta kara so inda Fatima take zaune ta ce “Ki je ki duba ta, mutane sun rage.”

A hankali ta yunkura ta nufi dakin, sai a lokacin ne kuma Mustafa ya fito daga wajen likita shi ma ya nufi dakin da Hana take kwance.

Ido Fatima ta zuba mata, tana kallon yadda take mayar da numfashi a hankali, hannunta ta kama tana kallon yadda ya kara yin shar a cikin kunshin da Ummi ta yi mata.

Mustafa ya shigo da abokanshi, dalilin da ya sanya Fatima fita.

Ta koma wurin zamanta na dazu, tana kallon shige da ficen mutane, yayin da a kasan zuciyarta take addu’ar Allah ya ba Hana lafiya.

Mama da Fatima ne suka ci gaba da jinyar Hana, sai da suka yi sati daya sannan aka sallame su, har zuwa lokacin kuwa yan dubiya basu yanke ba.

Mustafa ma ya koma makaranta saboda zasu fara jarabawa.

*******

Da misalin karfe biyar na yamma Aunty A’i ta shiga gidan Mama, a tsakiyar gidan ta samu Mama, don haka a nan ta tsaya suka gaisa.

“Daga ina?”

“Gidan Fatima na je, na kara gano Hana?”

“To ya jikin nata?”

“Da sauki sosai, tana ta yawonta ma”

Mama ta fadada fuskarta da fara’a “Wai tafiyar ta nuna ne?”

Ita ma murmushin ta yi “Ba dai can ba, amma kam tana yawonta.”

“Ai Shekaranjiya da na je gidan, haka na same ta tana daga kafar da kyar.”

“Wai na ga ma Fatiman kamar ciki ne da ita?” Aunty Aisha ta canja hirar tasu

Mama ta tabe baki “Oho mata, Lami ma da ta zo duba Hana haka take tambayata, na ce ban sani ba ni ma.”

“To Mama idan cikin ne ya maganar karatun kenan?”

“To da me za ta karatun?” Mama ta tambaya hade da kallon Aunty A’i

Aunty Aisha ba ta amsa ba, Mama ta dora.

“Da shekarunta za ta tafi karatun ko? To idan ba ki sani ba, Fatima ta kwashe kominta ta sayar, hatta fridge da generatornta an ce ta siyar da su.”

Cike da mamaki Aunty Aisha ta ce “Yaushe?”

“Ina zan sani, bakina da nata ba ta fada min ba”

“To me ta yi da kudin?” cewar Aunty Aisha jiki a mace

“Su suka sani ita da mijinta, ni dai nawa ido, Allah ya ara min rai da lafiya, in ga karshen son da Fatima ke wa Mustafa. Ubanwa ya fada mata ana ma namiji haka, mu bamu isheta shawara ba, ta siyar da komai ta ba miji kudi yana karatu. Hmmm a hankali za ta gane da gari ake tuwo, namiji ba a yi mishi haka.”

Aunty Aisha dai shiru ta yi, kafin daga bisani ta ce” Na tafi. Allah ya kyauta. “

” Amin. ” Mama ta fada cike da takaici.

Daga nan gidan Aunty Hauwa ta shiga, Aunty Sadiya ce tsaye ita da Aunty Hauwa, a Kofar part din Aunty Hauwan, da alama rakiya Auntyn ta yo mata.

Ganin Aunty Aisha ta shigo, sai suka mayar da hankalinsu a kanta, har zuwa lokacin da ta karaso wajen su.

Suka gaisa lokaci daya kuma ta na yi wa Affan wasa da ke bayan Aunty Sadiya.

“Daga Ina?” Aunty Hauwa ta tambaya hade da kallon Aunty Aisha

“Hana na kuma dubowa.”

“Ikon Allah, kin ga kuma fa ni ma can zan je.” Aunty Sadiya ta cafe

“Ya jikin nata to?” Aunty Hauwa ta tambaya

“Akwai sauki sosai”

“To Allah ya kara sauki. Bari ni ma in je ko na dawo.” cewar Aunty Sadiya a lokacin da take kokarin tafiya.

“Ni kam wai kun lura da abin da na gani kuwa?” Aunty Sadiya ta tambaya a lokacin da take dakatawa daga tafiyar da ta soma yi.

Duk suka mayar da hankalinsu a kanta, alamun jiran karin bayani

“Ni fa a zaman asibitin nan, sai na ga kamar Fatima na da ciki.”

“Allah yay miki albarka,, wallahi maganar da na gama yi wa Mama kenan” cewar Aunty Aisha.

Duk suka zuba ma Aunty Hauwa ido kamar ita ce Fatiman.

“To mace da mijinta don ta yi ciki har abun mamaki ne.” Aunty Hauwa ta mayar masu hankalinta kwance

“Kenan cikin ne da ita?” cikin sauri Aunty Aisha ta tambaya tana kallon Aunty Hauwan

“Sai dai mu yi mata, addu’ar sauka lafiya”

“Aunty Hana fa ko shekara ba ta yi ba.” cewar Aunty Sadiya a marairaice.

“To koma dai menene.”

“To Aunty karatun fa?” Aunty Sadiya ta kuma tambaya

“Allah masani.” Aunty Hauwa ta ba ta amsa.

“Uhmm! Ni ba ma wannan ba, Mama take fada min wai tana ta siyar da kayanta, don Allah Sadiya idan kin je ki yi kokarin tabbatar da hakan.”

Aunty Hauwa da ta saki baki ta ce “Ban gane ba.”

“Haka dai Mama ta ce min, wai an ce har fridge da generatornta ma ta siyar.”

“Me?” Aunty Hauwa ta kuma tambaya a kidime kafin ta kara cewa “To ta yi me da kudin?”

“Allah masani”

Aunty Sadiya da abun ya ishe ta, ta ce “To Allah ya kyauta, ni kam na tafi.

Daga haka ta wuce su ma suka shige ciki

******

Sai da Aunty Sadiya ta fara shiga sashen Inna suka gaisa, sannan ta dawo bangaren Fatima.

Komai na bangaren Fatima a killace, sannan tsab-tsab, zaune take a cikin baranda tana yankewa Hana farce.

Ganin Aunty Sadiya ya sa Hanan kwace kafarta ta yi kanta tana murna.

Aunty Sadiya ta dagata sama tana fadin “Oyoyo diyata, jiki ya yi sauki ko?”

Ta bi Fatima da kallo wacce ke murmushi daga zaunen da take.

Sanye take cikin atamfa quali wax riga da zane ta yi haske sosai hade da yin ƙiba madaidaiciya, ka rantse dai ba ta da wata matsalar.

Bangaren nata kuwa a share yake kal, ga kamshin turare na fita mai sanyaya rai.

Mikewa ta yi hade da daukar Affan tana mishi wasa, sannan suka shiga falon, shi ma gyare tsab, babu wani tarkace sai kamshi mai dadi.

Ruwa da abinci ta kawo mata, bayan sun gaisa.

Kadan Sadiya ta tsakuri abincin suka shiga hira. Har zuwa lokacin d ta ce “Ciki gare ki ko? Don kin canja gabadaya, kin yi wani haske da ƙiba.”

Dariya Fatima ta yi “Ba ni da komai.”

Aunty Sadiya ma dariyar ta yi “Ai idan dai ka ji mace an ce tana da ciki, ta ce ba ta da komai to tana da shi.”

Dariya kawai Fatima ta yi ba tare da ta ce komai ba.

Aunty Sadiya ta gyara zama, alamun maganar da za ta yi mai muhimmanci ce “Fatima to karatun fa?”

Shiru ta yi ba ta ce komai ba, ganin haka ya sa Aunty Sadiya ta ce “Kar ki bari dama ta kwace miki, kila gani kike a yanzu kamar ba za ki shiga matsala ba, to ba wai fata nake miki ba, amma akwai ranar da sai kin ce ina ma na yi karatuna kuma ina aiki. A wannan zamanin fa babu wani namiji da zai dauke miki duk wata dawainiya ta ki. Idan kika haihu, to ki yi planing don Allah, ki samu ki ci gaba da karatunki wlh karatun nan shi ne gatanki.”

Fatima ta nisa kadan sannan ta ce” In sha Allah.”

Jin kiran sallahr magariba ya sa Aunty Sadiya mikewa, lokaci daya kuma tana daukar Affan da ke wasa da Hana.

Tare suka fita, maimakon Aunty Sadiya ta wuce zuwa tsakar gida, sai ta shige kitchen din Fatima har babban store din da ke cikin kitchen din ta leka, don tabbatar da abin da take zargi.

Daga nan bangaren Inna ta koma ta yi mata sallama, har Kofar gida Fatima ta rakata, sannan ta dawo ciki.

<< Daga Karshe 22Daga Karshe 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×