Skip to content
Part 52 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Kai tsaye Fatima dakin Umaima tazarce, a lokacin Umaiman zaune take kan katifa tana yi wa Beauty video wacce ke koyon tafiya.

Ganin Fatima sai ta dakata tare da fadin “Har ya tafi?”

“Ban sani ba.” Fatima ta amsata bayan ta daure fuska.

Dariya Umaima ta yi kafin ta ce “What again?”

“Ba ki san me kika yi min ba ashe?” cewar Fatima tana harararta.

“Me na yi?” cikin dariya Umaima ta kuma tambaya.

“Yayana fa kika wulakanta.” har zuwa lokacin harararta Fatima ke yi.

Ta dakata da dariyar tata kafin ta ce “Shi ne ya fara wulakanta ni ai, shi ne fa nake ba ki labarin an hadamu yau, a matsayin wanda zai yi min bayani a kan project dina”

“Serious?” Cike da mamaki Fatima ta tambaya

“Ehen.” Umaima ta amsa.

“Ikon Allah!” cewar Fatima lokaci daya kuma tana zama gefen Umaima.

“Yayana ne. A madadinshi ina ba ki hakuri, haka yake kafin ku saba, but he is very simple”

“As you said” cewar Umaima cikin tabe baki

Dariya Fatima ta yi kafin ta ce “Da gaske fa.”

“Ke ni kyale ni, wlh abun da ya min ya zafe ni”

“Zan yi mishi magana to”

“Ya fi” Umaima ta fada hade bude ledar da ke gaban Fatima.

Daya dai tarkacen kayan kwalliya ne, tun daga sabulun wanka, maya-mayai, turarurruka, set of shampoo, bangles, sarkoki da sauransu.

Dayar kuwa kayan tea ne, sai kalolin juice masu kyau, wanda daga ganinsu daga can Indian ya taho dasu.

Sosai Umaima ta yaba kayan, Fatima ta ce ta zabi duk abin da take so, amma Umaima ta ce ba za ta dauka ba, saboda abin da Jamil din ya yi mata, duk magiyar da Fatima ta yi mata Umaima kin dauka ta yi.

Ta ce har sai Jamil ya ba ta hakuro sannan za ta yi amfani da duk wani abu da ya fito daga hannunshi.

Wannan kenan.

*****

Shekarar karshe ta zo wa Fatima da abubuwa da yawa, ga lectures, ga aikin da take yi, ga rubuta project sannan ga hidimar auranta. Don ma Beauty babu rigima sosai, za ta kai ta gidan Baaba ta wuni, ko kuma ta zauna wurin Umaima. Shi ya sa take jin saukin wasu ayyukan.

Yanzu ma zaune take a tsakar daki ta ware fan, daga ita sai zane a kirjinta, wani bincike take a Google gami da project din da take rubutawa, karar karamar wayarta ne ya katse ta, ganin Mustapha ne sai ta daga, hade da soka wayar cikin hular da ke kanta.

“Ina Beauty?” abin da ya fara tambaya kenan bayan ta daga kiran.

Ta mayar da idon ta kan Beauty wacce ke bacci sannan ta ce “Bacci take yi. Lafiya ko?”

“Na saba idan na kira muryarta nake fara ji.”

Ta murmusa kadan kafin ta ce “Ya mutanen Abuja”

Shi ma sai ya kalli su Hana da suke zaune a tsakar dakin Mama suna cin abinci, ya ce “duk suna lafiya”

“Da kyau” ta amsa daidai tana rubuta wani point da ta samo a Google din.

“Ina fatan dai za ki shigo Abujar ranar Laraba” yadda ya yi maganar sai ya so ba ta dariya, don a marairaice ya yi ta.

“Ya Mustapha ina mun gama wannan maganar, na fada ma da ace ba a daga walimar nan ba, an yi ta a lokacin da aka sanya ta tun farko da zan zo. Amma yanzu abubuwa sun yi min yawa wlh, yanzu haka rubutun project dina nake yi. Fisabilillahi ta ya zan zo Abuja in yi har sati daya, yadda abubuwan nan suka taso ni.”

Ita ma ta karashe maganar kamar za ta yi kuka.

Ganin su Hana na kallon shi, sai ya yanke kiran, ba tare da ya ce komai ba.

Wannan ya sa Fatima ta ji kamar ya yi fushi ne. Shiru ta yi rike da wayar bayan ta zare ta a kunnen ta.

Ta jima a haka kafin ta aje wayar a gefe ta ci gaba da abin da take yi, saboda hannun hagu dai ba bakon kazanta ba ne, ya saba irin wannan fushin ya huce.

Ita kuwa zuwa Abujan ne sam ba ta so a yanzu, ta fi son sai ta kammala karatunta.

A can bangaren Mustapha kuwa aje wayar tashi ta yi daidai da shigowar Mama cikin dakin.

“Yanzu za ku tafi din ne?” ta tambaya tana kallon su Hana da suke zaune a tsakar dakin.

Kai ya daga tare da fadin “Ban son mu yi dare ne”

“Mustapha tun muna shaidar juna ka biya Katsina ka kai wa Fatima yaranta ta gani, wajen wata biyar kenan fa ba ta sanya su a idon ta ba.”

Ya dan sosa kai ba tare da ya ce komai ba.

Ta dora da “a rika sara ana duban gatari mana, ko don kun ga ba ta ce muku komai. Nan dai da kar biyu sha Allah ka isa Katsina, zuwa karfe hudu sai ku wuce Abujar, ita ma ai daga nan ta ga sabuwar motar ta ka.”

“In sha Allah”
Ya furta a hankali.

Shadaya daidai kuwa na safe suka baro garin Sandamu tare da daukar hanyar Daura wacce za ta sada su da garin Katsina.

Misalin karfe biyun ranar kuwa, Umaima ce shanye cikin ma fi soyuwar kwalliyarta, wato doguwa riga, ta nade kanta da vail din rigar, kafadarta kuwa Beauty ce ta saba, yayin da Fatima ke tsaye da karshen barandar block din nasu suna magana da Umaiman.

Gidan Goggo Halima za ta je, shi ya sa ta dauki Beauty ko Fatima ta samu damar yin rubutunta a nutse.

Umaima na dora Beauty a front seat Maigadi ƴa Bude gate, yayin da Bakar motar ta silalo cikin gidan, hasken rana kara fito da sabuntakarta.

Fatima ce kawai take kallon motar Umaima kuwa zagaya ta yi mazaunin direba.

Daidai tana yi wa motar Key, su Hana suka fito a guje suna ihun Momy.

Cike da mamaki Fatima ke kallonsu, ganinsu ta yi kamar daga sama.

Ta hade su gabadaya ta rungume a kirjinta.

Wani farin ciki ya cika kirjinta.

Umaima ta fito rike da Beauty ita ma cike da mamakin ganinsu.

Hana ta karbi Beauty cike da murnar ganin yar’uwarta, sannan suka hada baki wajen gaishe da Umaiman.

Gabadaya suka runguda wajen motar, Mustapha da ke hakimce a ciki ya fito, hade da satar kallon Fatima ya aika mata da harara, ita kuma sai ta yi murmushi.

Suka gaisa da Umaima sannan ya dauki Beauty yana mata wasa.

Cike da zolaya Umaima ta ce “Yau kam a ina mu ka yi sallah ne, kai ne a lodge din mu ko mafarki?”

Ya dan murmusa kadan kafin ya ce “Ni ne dai, dama ai kune ba ku gayyace ni ba, yanzu ma gaban kaina na yi.”

Cikin dariya Umaima ta ce “Amma kwana za ku yi mana ko?”

Ya zaro ido, hade satar kallon Fatima wacce take tsaye cikin zumbulelen hijab har kasa tana murmushi. Ya ce “Wucewa za mu yi ai kam, da kuka samu ma mu ka zo”

“Amma da gaske?” Umaima ta kuma tambaya

“Sha Allah!”

“Aiko to su Hana su zo mu je a yi musu tsaraba, dama fita zan yi” kawai ta fadi hakan ne, don ba su Fatima waje, ta lura da yadda Mustapha ke ta kallon Fatiman kamar yau ne ya fara ganin ta.

Sosai kuwa ya ji dadin hakan, shi ya sa ma bai yi gardama ba, ya ce a dawo lafiya.

Haka ta kwashe yaran duka ta fice dasu, bayan ta radawa Fatima a ci amarcin lafiya.

Haka ta bar Fatima na ta dariya kamar wawuya.

“Gidan kun ya yi kyau” Mustapha ya katse ta yana karewa gidan kallo.

“Mun gode” ta amsa a hankali.

“Where your room is?”

Ta nuna mishi da yatsanta.

Sai ya rufe kofar motar hade da takawa zuwa dakin.

Ita kuma ta bi bayan shi.

A tsakar dakin ya tsaya, yana kare masa kallo, komai tsab ga kamshi mai dadi.

“Very nice” ƴa fada hade da bude kofar toilet din ya shiga.

Nan ma a tsabtace sai pant din ta da ta shanya a ciki.

Ya nuna pant din tare da cewa “Wandon mai dakin ne?”

Tura baki ta yi hade da harararshi.

Ya yi dariya, ita ma sai ta yi dariyar don ta san ina maganar ta shi ta dosa.

Wani lokaci ne can baya Aunty Bilki ta taba zuwa gidan Mama ta yi wanka, lokacin tana ji da kuruciya, don ka haihuwa ba ta yi ba. Sai ta shanya pant din ta a toilet.

Shi ne Fatiman ta ce wane mara kunya ne ya shanya mana pant a bayan daki.

Wannan magana ta sanya ce-ce-ce-ku-ce tsakanin Aunty Bilki da Fatima, har sai da Aunty Bilkin ta dauke pant din.

Shi ne ita kuma Fatima watarana ta shanya nata pant din a tsakar gida, sai ko ga Aunty Bilki kuwa gaban Mustapha ta ce “Wane marar kunyar ne ya shanya mana katon wandonshi a tsakar gida, bai jin kunyar masu shigowa.”

Sosai Mama ta yi dariya a lokacin. Ita kuma Aunty Bilki ta daga pant din a gaban Mustapha ta ce “Au ashe na yar masu gida ne”

Ba komai yake ba Fatima kunya ba. Amma ranar sosai ta ji kunya. Shi ma kuma a lokacin ya san ta ji kunyar, saboda sai da suka rika wasan ƴar ɓuya da ita.

Duk suka dakata da dariyar kafin ya ce “Dakin da gidan duk sun yi kyau. Na yi farin ciki sosai da na same ki a sutuuce, and I’m very sorry da ban tsaya da kafafuna wajen ganin kin samu muhalli da ya dace ba, bayan nine ya kamata in yi hakan. Sosai na ji kunya yau. Don Allah ki yi hak’uri”

Ya kafe ta da idanu, yayin da ta sauke ajiyar zuciya tana fadin “Ba komai. Ai ka yi min abubuwa da yawa na alkairi.”

Ya murmusa kadan kafin ya ce “Me Umaima ta ce miki a kunnenki lokacin da take fita?”

Ta yi saurin kai tafukan hannayenta kan fuskarta ta rufe tana dariya.

Ya karaso dab da ita, tare da sanya hannunsa ya sauke hannayen nata kasa, ta rufe idonta har lokacin dariya take yi.

Ya yi kissing din goshinta” I missed you ” ya fada hade da murza hannayenta da ke cikin nasa.

Ba ta amsa shi ba, amma ta dan bude ido kadan suka kalli juna.

Hijab din jikinta ya zare, ya dan murmusa” Har yanzu ana karin kirjin ne? “

Ya ja ta zuwa kan katifar, ba ta yi mamakin yadda a aikace ma ya nuna ya yi kewarta ba, ita din ma ta yi tashi kewar almost 2 months.

Ita ta matsa mishi ya yi wanka wai ba ta so Umaima ta dawo ta same su a daki.

Duk da yadda jikinsa yake a mace haka ya je ya yi wankan, ya shirya tsab tamkar komai bai faru ba.

Sannan ya fito zuwa mota kamar yadda Fatima ta matsa, ita cikin sauri ta yi wankan, hade da sanya doguwar riga milk colour, sama-sama ta murza powder hade da zizira kwalli, ta shafa Humra sannan ta biyo shi zuwa wajen.

Front seat din ta zauna tana kallon yadda ya jingina bayanshi da kujerar tare da lumshe ido kamar mai tunanin wani abu.

“Sosai kin canja, tell me the screet please”

Ta bi jikinta da kallo, kafin ta ce wani abu ya dora “Fatima ina hada ki da girman Allah ki je wajen taron nan, ba na son a yi walimar babu ke” wannan karon ya bude idonsa yana kallon ta.

Kafin ta amsa wayarta ta shiga vibration alamun kira “Muna hanya ko ba ku kammala ba mu koma?” Umaima ta yi maganar cike da tsokana

“Bari in hadaku ki tambaye shi.”

Cikin ihu Umaima ta ce “Rufa min asiri”

Duk suka yi dariya Fatima ta yanke kiran.

Ya janyo ta jikinsa sosai, cikin marairaicewa ya ce “Please Fatima, please”

Cikin kasalalliyar murya ta ce “But not 1week please”

“Na amince” ya yi maganar hade da kissing din goshinta alamun jin dadi, daidai lokacin motar Umaima ta shigo, don haka duk suka daidaita kansu.

Yaran ne suka fara fitowa aguje ko wacce rike da Leda, wannan ya tabbatar mata Umaima ta kashe musu kudi.

Mustapha ya yi mata godiya sosai yayin da suke ta tsokanar juna, inda ya dora mata nauyi kawo masa Fatima ita kuma ta dauki alkawarin yin hakan.

4:30pm suka bar cikin lodge din, bayan ya yi sallahr la’asar Fatima ta so a bar mata Hana amma Mustapha ya ki, wai sai ta zo Abuja sannan.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 51Daga Karshe 53 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×