Skip to content
Part 7 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Ya zuba mata ido yana kallon fararen hokaranta da suke shirye a cikin bakinta, wanda bakin dasashi ya kara kawatasu.

Yau sosai ya ga fuskarta ta canja ya rasa dalili, tsawon minti biyu yana kallon ta a lokacin kuwa ta fara tsagaitawa da dariyar muguntar tata.

Ya dauki tsintsiyar ya nufi inda Mama take tsaye, gaishe ta ya yi kafin ya mayar da hankalinshi kan Fatima.

“Sau biyu kenan ake hukuntani da zunubinki, kar ki bari a kara na uku.”

Hannu ta kai hade da rufe bakinta tana karamar dariya.

“Ai dama abun arziki bai gaji kare ba, ba yadda yan’uwanki ba su yi ba a kan in basu leshin nan na hana su. Dama Auntynki ta ce ba a miki gwaninta, ga shi nan kuwa kin watsa mun kasa a ido, barkana ma da basu a kusa. Maradin ki baya kunya.”

Dakatawa ta yi da dariyar, ta narke fuskarta,

“Ayyah!!! Haba Mamata, ki yi hakuri don Allah, ni da ke ai kamar tib da taya ne.”

“Da kika gama kwance mun zanen a kasuwa?” Cewar Mama tana shigewa daki don ta san Jamil ita yake jira.

Mustafa da yake ta kallon Fatima yana kokarin gano abin da ya canjanta farat daya, cikin sa’a kuwa ya kai idonshi a kan gashinta. Ya lumshe ido lokacin da ta gama yi wa Mama shagwaba da sunan lallashi.

“Me ya sa tun da kika dawo ba ki je Islamiya ba?” Ya jefa mata tambayar a kokarin shi na korar yanayin da yake ji a kanta.

“Yau na ga ta kaina kishi da me cizo, yo yaushe na dawo? Ko fa sati ma ban yi ba, kuma ka san ai biki dai za a yi a gidanmu.” Ta karashe maganar hade da turo baki gaba.

“Amma Zainab na zuwa ai?”

“Yo Zainab yar gidanmu ce? Yar gidan hakimi ce, tsohuwarta ce yar gidanmu.” Ta Yi maganar hade da mimmirgina kanta gefe.

“To ai kamar yar gidan nan ce, tun da dai yar uwarki ce ta kusa.”

“Hu’umm” hade da tabe baki ta yi maganar.

“Na yi karya ko?”

“Ban ce ba, amma ni fa bana wani damuwa da yan’uwa nesa ko na kusa, ka ga daga uwata, ubana sai yayyuna, wani ‘ya’ yan yan’uwa can bana wani damuwa dasu, kai ni fa ko kaka bana lissafawa a cikin yan’uwa.”

Kallonta yake har ta gama maganar wacce take yinta cikin yamutsa fuska da hannuwa

“Eh lallai Fatima, dama dai ana ta cewa ba ki da hankali, bana yarda, amma yau dai na yarda, kin ga tafiyata.”

“Umma ta gaida Assha.” Ta fada a hankali daidai lokacin da ya mike yana kakkabe rigarshi.

Har ya kai kofar fita daga harabar gidan sai kuma ta kwalla mishi kira da karfi.

Ya waigo ba tare da ya amsa ba,

“Ba ka ga kaina bane?”Ya yi murmushi me laushi kafin ya ce,

“Na gani.”

“Shi ne ba ka ce na yi kyau ba?”

“kin yi kyau sosai, na fada a zuciyata.”

Mama da ke daki tana sauraronsu ta daga murya cikin dariya,

“Ba kwa batawa ba kwa shiryawa, Fatima ta Malam Mustafa.”

“Kin san Mama neman shiga take yi a gurina ai.” Cewar Mustafa yana kallon Fatima.

“Wa? Wai ni kake nufi? Ai kai ma ka san ni matar manya ce, tun da a gabanka aka yi, kawai ina yi ma kwalele ne.”

Mama ta kuma yin dariya bayan Fatima ta karashe maganarta.

“Ki kara cewa Kwalele kike mun don Allah?”

“Kwalele nake…”

Ganin ya yunkura kamar zai taho ne ya sa ta zunduma da gudu zuwa daki tana dariya, a can kuma kafar Jamil ta taka.

Saurin ja da baya ta yi, tana kallonshi, kamar ba shi ta taka ba, duk kuwa da ta san ta taka shi da karfi.

Wani lokaci ɗaurewarshi dariya take ba ta, kamar yanzu ma da ta ka sa rike dariya,

“Yi hakuri gold din Mamar gidanmu?” Da kyar ta furta hakan saboda dariyar da take yi ƙasa-ƙasa.

A maimakon ya yi magana mikewa ya yi ya fice daga dakin.

Kan kujera ta fada hade da sakin dariya,

“Kai muna ganin ikon Allah a wannan gida.”

“Ke damuwata da ke ba kya gane me miki wasa da wanda baya miki.” Cewar Mama.

“Hummm! Ni ina ruwana, ni fa lokacin da na fahimci mutum baya son abu, a lokacin ne nake yi mishi.”

“Ai kuwa watarana za ki ji haushin hakan.”

“Haushi kuma? Mama ni fa ba komai ne yake ban haushi ba, abin da yake ba mutane haushi to ni wallahi sau tari ma dariya yake ban. Ni fa ko kukan mutuwa ban iya ba.”

“Uwarki da Ubanki basu mutu ba ne Fatima. Lallai har yanzu ke yarinya ce, bari in ta shi da shirmenkin nan in yi sallahr magriba ga shi can an kira.”

“Mu shehu ya roka mana” Fatima ta fada a hankali a lokacin da take gyara kwanciyarta a kan kujera.

*****

Yau juma’a gidansu Fatima a cike yake da jama’a kasancewar gobe asabar daura auren Kabir, kowa ya zama busy hayaniya ko ta ina, yara kaca-kaca ko ta ina. Ni kaina ina mamakin yadda kowa zai gane na shi.

Tun  goma na safe Fatima suka tafi gurin kunshi, amma har aka sakko masallaci basu dawo ba, motsi kadan Mama sai ta ce “Oh! Wai ba wanda ya ga Fatima ne, wannan wane irin kunshi ne, ko karin safe me kyau ba ta yi ba tana da ulcer.”

A wannan karon Aisha ce ta ba ta amsa, “Mama hala dai Fatima nono take sha? Wannan damuwar ta yi yawa, wai ga mu mu shidda ba duk yaranki, ga jikokinki kuma, amma don ba Fatima tun dazu kin damu ita da kike ma ganinta kullum.”

“Gane mun hanya dai Indo, Fatiman kamar wata bakuwa, a fa garin nan aka haifeta za ta bata ne?” Cewar Sadiya cike da mamaki.

“Bana son wulakanci fa, na fada miki ban son Indon nan.”

Babu wanda Mama ta ba amsa ganin gilmin Jamil ya sa ta yi waje.

Shi ta sanya ya bi su Fatima gidan kunshin ya gano mata lafiya.

A kofar gidan kunshin ya yi parking hade da aiken yaro daya da suke wasa a kofar gidan a kan ya kira mishi su.

A lokacin kunshin Zainab ya bushe, tana kankarewa, Fatima kuma na hannu ne ya bushe na kafa bai gama bushewa.

Zainab ce ta fita, jim kadan ta dawo tana fadin, “ke Kawu Jamil ne ashe.”

Fatima ta zaro ido “Ki ce jaraba an nan.” lokaci daya kuma tana yayibar hijabinta.

A kofar gida ta karasa sanya hijabin, ta kalminta a hannu.

Kai ya dago yana kallonsu ya dire idonshi a kan Fatima.

“Ita kominta ba natsuwa, ko yaushe za ta fara abu a natse?” Ya fada a zuciyarshi

A zahiri kuma da ido ya yi amfani wajen nuna masu su shiga motar. Zainab ce ta fara shiga.

“Ke!” Ya fada cikin kasaitacciyar muryarshi. Fatima da take kokarin shiga ta dakata, Zainab ma da take kokarin zama dakatawa ta yi.

“Kin san dai bana son kazanta ko? Kar ki sanya mun dattinki.”

Kallon juna suka shi ga yi, don basu san da wa yake ba, da wacce ta shiga ko me shirin shiga.

“I mean you” ya nuna Fatima da key din motar da ke hannunshi.

Ta rufe bakin da ta bude, hade da kallonshi, ranta ya baci sosai da maganarshi, tsawon mintuna suna kallon juna ba wanda ya janye idonshi. Daga karshe dai Fatiman ce ta janye idonta bayan ta manna mishi yar karamar harara hade da tura bakinta gaba.

“Dadin abun ma ni ba rokonka na yi ka zo ka dauke ni ba, kai ne ka zo. Kuma na gode ma Allah da ba kai ne mutum na farko da ka fara sayen mota ba a duniya.”

Can ƙasa ta yi maganar amma hakan bai hana ya ji abun da ta fada ba. Ya bude kofar motar ya fito zuwa inda take, tun kafin ya karaso ta aje gwiwarta kasa hade da kunshe kanta cikin hannuwanta tana jira saukar mari ko hauri.

Amma tsawon dakikai ba ta ji hakan ba dalilin da ya sa kenan ta dago kai ta kalleshi, kuri da idanuwanta masu maiko ta yi mishi.

Janye nashi idon ya yi yi, lokaci daya kuma ya koma cikin motar bayan ya rufe duk kofofin.

Mikewa ta yi hade da kakkabe gwiwowinta tana kallon motar ta shi da take shiga kwana.

“Hmmm! Yaya Jamil, ko don kai, sai na yi karatu me zurfi, albashina na farko sunanshi motar Fatima, don kuwa shi ne zubin farko a adashen sayen motata, sai na bude ka da kura, na watsa ma kwata. Kuma ina zuwa gida cikin dare zan je duk in huje tayoyin motar, in ga ta fadi wai kwarkwata ta kada kudin cizo.”

<< Daga Karshe 6Daga Karshe 8 >>

1 thought on “Daga Karshe 7”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.