Da na sani ƙeya ce, shi ne abin da Salim ya fara tariyowa a cikin ƙoƙon ƙwaƙwalwarsa. Tare da goge guntun hawayen da ya zubo masa daga kumatunsa.
Ya ce, “Dan Allah! Ku yi haƙuri ku barni wallahi na fasa na yafe ba na son kuɗi ku bar abin ku zan ci gaba da haƙura da takaicin da Allah Ya nufe da shi.” Tsawa aka daka masa tare da cewa, “Hahaha! Kai ɗan saurayi ka sani, ka riga ka makara domin aikin gama ya riga ya gama, in an shigo cikin wannan ƙungiya ba a fita har abada sai dai mutuwa. Don haka ka natsu da kyau, yanzu zan ɗauke ka zuwa Fadar mai girma Sarauniya Murabbbatu. “Mutumin na gama magana ya nuna Salim da ɗan yatsarsa sai suka ɓace ɓat.
Saukarsu fadar ke da wuya. Mutane ne maza da mata sun yi shigar baƙaƙen kaya sun ɗaura jan ɗan kwali akansu. Hannunsu ɗauke yake da ƙwarya, sun shafa farin fenti da bulu a fuskarsu.
Can sai wani daga cikinsu ya ce,
“Yaku ‘yan ƙungiya kowa ya shirya yanzu mai girma Sarauniyar sarakuna za ta iso wannan faɗar domin amsar gaisuwa da gabatar da sabon ɗan ƙungiya.”
Nan take wutan da ke kunne a ilahirin wurin ya ɗauke, hayaƙi ya turniƙe a ko ina ba ka iya ganin kowa da ke gurin.
Can bayan wasu lokuta sai haske ya dawo nan take kowannensu ya zube a ƙasa warwas! suna kai gaisuwa ga Sarauniya Murabbbatu.
A daidai lokacin ne aka dawo da Salim daga hayyacinsa, nan take ya fara tunano abubuwan da suka faru a baya.
A daidai lokacin ne ya haɗa idonu da Sarauniya Murabbbatu nan take ya ji gabansa ya yi mugun faɗuwa, domin ya firgita matuƙa da ganin kamanninta abin tsoro ne, domin tsayinta ya kai a haɗa mutane goma a tsaye girman kanta yakai girman kan mutum biyar, ƙafatunta kuwa da hannayenta zara-zara bakinta yana kama da na jaɓa. Duk illahirin jikinta gashi ne.
Sarauniya Murabbbatu za ta kai kimanin shekara casa’in da uku a duniya, ita ce shugabar ƙungiyar asirai.
Sarkin Fada Dumaki ya fara magana ya ce, “Ya mai girma Sarauniya Murabbbatu! Yau mun zo mi ki da babban burin da kika ɗauki tsawon shekaru kina jiran ganinsa. A yau mafarkin ki zai zama gaske. Mun kawo ma ki saurayi mai jini a jika ajin farko wanda zai maye gurbin abin da kika rasa tsawon shekaru talatin da bakwai da suka wuce. Ya mai girma Sarauniya Murabbbatu yanzu za mu kawo shi gare ki domin ya kwashi gaisuwa tare da yin mubaya’a.
Sarkin Fada Dumaki ya je ya janyo hannun Salim, suka fara tawowa gurin Sarauniya duk da cewa Salim ya so ya gudu daga gurin amma sai ya ji ya kasa tunda suka haɗa ido da Sarauniya Murabbbatu ya ji ya kasa koda motsa jikinsa sai yadda aka yi dashi.
Suna isa gurinta Salim ya sa guiwowinsa a ƙasa tare da yin abin da Sarkin Fada Dumaki ya umarce sa da ya yi na ya ɗaga hannayensa sama. Haka kuwa ya yi. Can sai Sarkin Fada Dumaki ya ci gaba da cewa, “Ya mai girma Sarauniya Murabbbatu ga matashin saurayi sunansa Salim shi ne zai maye gurbin Maharaz da ya bijire maki. Duk da cewa ya kwashi ayar sa a hannu.”
Miƙewa Sarauniya ta yi daga kan kujeranta tare da zuwa kusa da Salim. Ƙwarya Sarkin Fada Dumaki ya miƙama sarauniya domin ta watsama Salim ayi masa wankar shiga Kungiyar Asiri. Duk da cewa Salim ya shiga cikin ruɗani da tsoro, amma hakan bai hana shi tuno da wasu addu’o’i ba don haka ya fara a cikin zuciyarsa ya ce, “Lah ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minal zalimin. Haka ya ci gaba da maimaita wa nan take Sarauniya Murabbbatu Jiri ya ɗibe ta ta zube warwas ji kake “Duhm! Tare da sakin wani mawuyacin ƙara wanda ya ƙaraɗe gurin tare da guguwa mai ƙarfi.
Shin me yake shirin faruwa kenan?
Mu haɗu a cigaban labarin domin jin yadda za ta kaya.