Gari ya waye duhu ya yaye. Yau ta kasance Laraba tabawa ranar samu. Masu azancin magana na cewa babu maraya sai rago.
ƙarfe shida na safiyar ranar Salim ya fito daga gidansu, hannun sa ɗauke da fayel na takardunsa domin zuwa neman aiki ko wannan karan Allah zai sa adace, domin Samu ba shi ga rago.
Ko da ya isa gurin neman aikin (scuirity ) tsaro. Matasa ya gani birjik babu mafaka tsinke sun jeru akan layi kamar masu amsar sadaka ko in ce wanda za a raba ma kyautar masu gidan rana kuɗi.
Shiga cikinsu ya yi shi ma ya bi layin Baba sai ya gani, shi ne na kusan tamanin da bakwai a kan layi.
Wasa farin girki, tun Salim na ɗaukar abin da wasa ga shi har la’asar sakaliya ya riskesu a gurin ba a zo kansu ba, zuwa yanzu saura mutum biyu a zo kansa.
Haɗa kai ɗa guiwa ya yi, sai ka ce wanda aka aiko masa da saƙon mutuwa saboda gajiyar da ya yi.
A daidai lokacin ya tuno da nasihar haifiyarsa Inno da take yawan yi masa, ” Kabi duniya a sannu Salim komai ya yi farko zai yi ƙarshe, idan ka duba da kyau yaro da rarrafe yake tashi. Komai yana da lokaci, kuma rabon ka na nan zuwa idan ka yi haƙuri, ka yi ƙoƙarin samun aiki ta hanyar halal ba ta hanyar haram ba, domin mai haƙuri shi ke dafa dutse har ya sha romonsa.
“Yaushe ne zan tashi daga dogo rarrafen da nake ta yi ni kam?” Salim kenan ya tambayi kansa a zuciyarsa. Ya ci ga ba da cewa, “Yau kimanin shekarata uku da gama digiri a Jami’a. Na karanci ɓangaren ƙimiya da fasaha amma shiru kake ji an ce da shawo ya ci shurwa, Babu amo babu labarin samun aikina.
Ina daga cikin ɗalibai masu hazaƙa da ƙoƙari a ajinmu domin da First Class (Na ɗaya) na gama makaranta. Ada-da-can mutum yana kammala karatunsa zai samu aiki, amma yanzu ba haka abun yake ba domin reshe ya juya da mujiya.
Nauyayyiyar hamma Salim ya sauke tare da jin kayan cikisa suna yi masa faretin sukuwa, domin tsabagen yunwar da ke addabarsa. Rabonsa da cin abinci tun safe. shi ma wani wanda suka zama abokai ne a gurin mai suna Mahmud ya siya musu fanke na naira Hamsin suka haɗa da ruwa suka ci. Yana kan layi har yanzu ba a kira shi ba, domin a gabansu an sha kawo wasu matasan masu hannu da shuni a shige da su ofis ɗin Ogan a basu aiki. Su kuma ko oho, wannan shi ake cewa Talaka baya tashin talaka sai tashin talaka ya zo.
Wani mutum ne ya fito daga ofis ya ce, ” muna masu ba ku haƙuri akan mun ɗauki iya mutanan da muke buƙata aiki. Yanzu za ku iya tafiya mun Sallameku.
Innalillahi wa innalillahim rajiun! Salim ya fara furtawa, sannan ya ji jiri ya fara ɗibansa hakan ya sa ya samu guri ya zauna a ƙasa. Mai zai faru jin wani sabon al’amari ya yi wanda ya so ya fitar da shi daga cikin haiyacisa wato wani ƙasurgumin ƙato ne ya buga masa dorina a baya. Akan wai me ya sa ya zauna a gurin bai tafi ba. Ina shirin yi masa magana na ƙara jin wani saukar bubular kamar saukar angulu. An yi ba a yi ba, shuka a idon makwarwa. Hakan ya sa ys yi saurin ɗaukar takardunsa tare da saka takarmisa silifas da ya suɗe ya ɗaure shi da leda. Tare da ba ma mutum haƙuri ya bar gurin.
Tafiya Mahmud yake tare da jan ƙafarsa domin galabaitar da ya sha. Bai da ko sisi a aljuhunsa ga yuwa ga baƙin cikin da ke tare dashi na rashin nasarar samun aiki. Tasha ya wuce gurin mahaifiyarsa ke siyar da koko da ƙosai da hamma. Yana isa yaga taron jama’a sun yi cincirindo a gurin sana’ar mahaifiyar tasa wasu sun yi kalar tausayi wasu sun yi tagumi.
Kutsawa ya yi cikin mutanan mai zai gani. Mamansa ya gani a kwance cikin jini, ba ta cikin hayyacinta. Mutanan gurin na cewa wai ina ‘yan’uwanta nan wasu suka nuna Salim. Salim sandarewa ya yi a tsaye tare da sakin kuka mai tsuma zuciya yana kiran sunan mahaifiyarsa . Cikin zafin na ya ɗauke ta cak ya sa ta a cikin motar ‘yan’ sandar da aka kawo. Suka wuce asibiti. Nan da nan likitoci suka fara ba ta taimakon gaggawa.
Wani mutum ne mai siyar da itace a tashar yake faɗa ma Salim abun da ya faru. Ya ce, “Mahaifiyarka tana tsaka da suyan ƙosai wata mota ta kufcewa direban ya zo ya fi ta ƙafafunta, nan take mai tuyar shima ya zube mata a jiki. Lokacin da abun ya faru kafin mu an kara direban ya gudu sai ya bar motar na shi yanzu motar na ofishin ‘yan’sanda.
“Innalillahi wa innalillahim rajiun.” Salim ya furta yana zubar da hawaye. Yanzu ya zai yi dama mahaifiyar suce kai kulawa dasu shi da ƙanwarsa.
Yana cikin wannan tunanin ne Likita ya buƙaci da su shigo ofis su sa mesa. Nan ya ce, ” Mahaifiyarku ta ƙone a fuska kuma ta samu karaya bakwai uku a ƙafar dama huɗu a ƙafar hagu, don haka tana buƙatar ayi mata aiki domin ceto rayuwarta.”
“Innalillahi wa innalillahim rajiun! Yanzu likita nawa ne kuɗin da za ayi ma mamar mu aikin?” Ya faɗa ne tare da goge ƙwallarsa shi da ƙanwarsa Fatima.
Takarda Likitan ya miƙa masu tare da cewa, ga dukka kuɗin da za a kashe naifi miliyan uku ne za ayi mata aiki, kuma in sansamu ne karku daɗe ba ku kawo kuɗin ba, domin idan kuka daɗe za ta iya rasa ƙafafuwan ta domin za su iya ruɓewa.”
Cikin tashin hankali Salim suka tashi suka fito harabar asibitin. Nauyayyiyar ajiyar zuciya ya yi ya ce, “Fatima ki shiga ki zauna tare da Mama zan je gida na dawo, ko Allah zai sa a dace na samu kuɗin na kawo.”
“To! Yaya Salim. Amma ka san ba mu da hanyar samun wannan kuɗin domin ko gidan da muke zaune na haya ne, bare mu ce za mu siyar a yi ma Mama magani. Gashi mahaifinmu baya raye su kuma danginmu kowa ka taɓa yanzu za ka ji suna ƙorafi na rashin kuɗi a hannayensu, sanadin hauhawan kayan abinci da sauran kayayyakin aikin yau da kullum.”
“Haka ne kam Fatima! Kar ki damu bari dai na je na dawo ko za a dace.”
“A dawo lafiya Yaya Allah ya sa a dace.”
“Amin Ya Allah.”
Kai tsaye unguwansu ya nufa, gidan wani maƙocinsu ya shiga domin neman taimako, aikuwa ya ci sa’a Alhajin yana nan. Bayan sun gaisa ne Salim ya yi masa bayanin komai na rashin lafiyar mahaifiyarsa da kuɗin da ake buƙata. Bayan Alhaji ya gama sauraronsa ne ya ce, “Ɗana kasan yanayin da kuke ciki yanzu babu kuɗi a hanayenmu, don haka ga dubu biyar Allah ya ba ta lafiya.” Cikin sanyin jiki Salim ya amsa tare da yin godiya.
Gurin masu siyar da waya ya je, dubin ya siyar da wayansa, naira dubu uku aka taya domin ƙarama ce kamfanin Vivo. Hakan ya sa yaƙi siyarwa. Ya rasa yadda zai yi shi da ake neman miliyan uku ko dubu ɗari ba a samu ba sai dubu biyar da Alhaji ya bashi. Guri ya samu ya zauna tare da yin tagumi a dai lokacin wasu samari suka zo in yake suka zaro masa wuka suka ce ya basu wayar hannunsa tare da duk abin da ke gurinsa, cikin damuwa Salim ke fasu haƙuri amma suka ƙi suka ce in ya ƙara magana za su kashe shi, nan suka yi da salim ya basu kuɗin da ke ajjuhunsa ya ƙi har ɗaya ya ɗauki wuka zai saramasa akansa. Jikake Salim ya rusa wata ƙara.
Kash! Mai karatu anan zamu tsaya. Sai a shiri na gaba. Zan so na ji ra’ayoyinku akan wannan labari tare da yin comments don samun ci gabansa.