MAIDUGURI, BORNO STATE
Unguwar GRA
Fitowa ya yi daga toilet ƙugunsa ɗaure da towel, ɗaya kuma ya ɗaura a kansa yana tsame ruwan jikin sa. Dressing mirro ya ƙaraso ya jawo table ɗin dake wajen ya zauna yana cigaba da tsame ruwan jikin sa, sanda ya tsame ruwan tas sannan ya ajiye towel ɗin a hanun bed, lotion ya jawo mai ƙamshin gaske ya fara mulke jikinsa dashi, sannan ya hau gyara gashin kansa shima da mayuka masu ƙamshi sanda ya mulke ko ina na jikin sa da lotion sannan ya ɗauki body spray ya dinga. . .