Faɗime ce ta yi zaman ‘yan bori, ta murɗema zakaru biyu wuya, ta fige ma kaji biyu gashi da ransu, ta kwaɓa dusarsu da ruwa ta shafe a jikin figaggun kajin. Ta haɗa itatuwan girkin da uwale ke ajiya a ɗakin, ta sheƙa musu ruwan da aka aje dan kajin, ta ɗora figaggun kajin bisa kansu a manufarta na masu kyakkyawan gashi. Uwale nacan shegen karaɗinta ya sa ba ta ji kukan da kajin suka dinga saki ba sa’adda ake musu wannan izayar.
Kuka za tai, ihu za tai, a’a kwantattun Aljanunta ne za su tashi? Ita dai kawai ganinta ta yi tana dosar bakin rijiya, ta wawuro bokiti cike da ruwa. Da shi ne kaɗai za ta fara hora Faɗime ta ji saukin tafasar da zuciyarta ke yi. Kajinta fa ? Kajinta da ta ɗau burin duniyar nan kansu? Kajin da da sune ne take tarin auren Hansai. Kajin da take musu kiwon da batawa cikinta. Asalima dusar bature take ba su. Kaji ne da ta sai da gadonta ta siye su ta gwammace ita ta kwanta saman tsummokara.
Malam da ke gefe ya yo kanta cikin tashin Hankali yana mai riƙo kafadunta. Doke hannunsa ta yi gami da fasa masa tsawa.
“Idan na yarda Kakale babu jini ta haife ni Malam! Na rantse da tsarkin mulkin Allah yau yarinyar nan sai ta bar gidan nan. kanta aka fara hauka ? Yau kwana goma da abin nan amman asarar da ta mini tafi ƙarfin hankalina…”
“Na ji ! Na ji, to yanzu aje ruwan nan sai muyi magana na miki alkawari duk inda kike so za ta tafi, amman ki nawa Allah karki hukunta ta ki ji tausayi halin da take ciki…”
“Ban san shi ba, tausayi dai ko ? To ba na fatar naji shi a raina in dai kan wannan abar ce. Maganar inda nake so kuma ai kafi kowa sani. Mari nake so a kaita can gidan gagararrun yara. Ai ba tun yau ba Malam Musan yace akaita…”
Ta yi shiru ganin Malam na zare idanuwa.
“Wallahi ko za ka mutu sai an kaita tunda ba kai ne ubanta ba balle ya dame ka, ka ji na rantse. ” Ta faɗa gami da fyace hance. Sai dai majinar bata faɗa ko’ina ba sai gaban rigar Malam. Ya yi baya da hanzari yana sharewa da hannun rigarsa, goshinsa na tsattsafo da gumin tashin hankali.
“Amana ta ce fa Uwale ? Me Bashari ya mini da zan saka masa da haka ? Na rasa wa zan kai mari sai gudan jininsa mafi soyuwa a ransa, da ta rage masa a duka duniya mai masa addu’a tunda babu shi? Haba Uwale, ki yi hakuri mana. In dai Kaji ne zan biya ki amman kibar Faɗime gabana. “
Ƙanƙance idanuwa ta yi tana watsa masa wani banzan kallo, sai kuma ta buga hannu cinya gami da doka shewa.
“Lalle Malam, ashe Maluntar taka ta ƙaryace tunda gashi yau ka zo gabana kana ƙero ƙarya. Yaushe Bashari ya ba ka Amanar Faɗime ? A gaban wa akai haka waye kuma shaida ? Basharin da har yau ina ce babu wanda ya ga ko sauran ƙashinsa? In ce kaine dai ka ga damar riƙewa. Ba fa ta Kaji nake yi ba a halin yanzu. Wannan na sani ko za ka sai da rigar jikinka sai ka biya ni. Ita yarinyar ce ba na so na ƙara buɗar ido na ganta cikin gidan nan. Na fi sonta can cikin sasarin karfe tana gurza haukanta…”
Ido jajir ya dago yana kallonta. Ganin yana rikiɗe mata ya sa ta kaɗuwa tayi shiru gami da saurin luma idanuwanta cikin nasa. Sadda kai ya yi kamar bawa gaban ubangidansa.
Murmushi ta yi mai sauti.
“Faɗi mana, na ga ka taso mini a zuciye.”
A sanyaye ya fara magana.
“Shi ke nan za a kai ta yadda kike so. Amma ki bari sai ƙarshen satin nan. Kin ga sannan na samu abinda za a basu su rike tan. Tunda dai ba haka kawai suke karɓar yaro ba.”
“Ko kai fa Maigida na Uwale. Da haka kake mini ina faɗa ka aikata ba gaddama ai da ba a dinga jin kanmu ba.”
Ta faɗa tana kifta masa tika-tikan jajayen idanuwanta da nufin fari.
“Allah ya kyauta.”
Ya furta gami da ficewa daga gidan duk ko da U’uwar yunwar da ke gurzarsa
Ta maida hankalinta ga ɗakin kaji tana sakin Murmushi. A hankali dai dukkan burirrikanta na gabda cika. lalle Salamatu tayi gaskiya da ta hanata aiwatar da mummunan nufinta a wancan lokacin. Ta tabbata da yanzu tana cikin nadama marar misaltuwa. Ina ma Bashari zai dawo ya ga yadda gudan jininsa ta koma ? Ba ta san irin farin cikin da za ta ji ba musamman idan taga zubar hawayensa. Ta sauke idanuwanta a kan Faɗime dake barci kishirɓan ta yi matashi da mushen kajinta. Ta dade tana ƙissima kamanninta da mahaifinta. Tana ji a ranta da tuni wannan yarinyar ta ta ce. Da ace Falmata ba tai kutse ta shige gabanta ba ta haramta mata mutumin da bata taɓa son wata halitta irin yadda ta so shi ba. Lamarin take tunawa da kuma ranar. Ranar da ta fara ɗora idanuwanta a kansa. Shi ne ya fara maidata duk wani abu da take a yanzu. Shi ya zare mata tausayi har ta iya kashe mutum duk a dalilin sonsa, duk a dalilin ya ƙi ta ya so ƙawarta. Zafin kishi, zafin kishi ya sa ta ji za ta iya murɗe wuyan ‘yar yarinyar Falmata da dukkan tunaninta ke bata silarta ne ma kome ya faru. Silar haihuwarta da ta tabbata ko da ba ai auren ba tunda an rubuta sai ta fito sai fa fito ɗin ko ma ta wacce hanya ce. Numfasawa ta yi abubuwan na dawowa cikin kwakwalwarta kamar yanzu suke faruwa.
Falmata ƙawarta ce koma ta ce ‘yar uwarta ce da suka tashi tare a matsayin maƙota. Daidai da kwanun abinci ba a taɓa raba musu ba har girmansu.
Ko da suka girma suka isa aure, ɗaya ba ta yarda ta yi zance ba ɗaya ba. In dai ba za a yi sallama da su a tare ba to ko waye saurayin ya kama gabansa ba wacce za ta fito a ciki. Haka aka saka musu ido dan wanda ya ce zai shiga tsakaninsu ma shi zai ji kunya.
Halin yau ya sa kowacce uwarsa ta fara kasa masa talla, musamman Falmata da ba ta tashi da mahaifinta ba. Uwarta kuma ta tsufa, haka su biyu kawai ta haifa. Asalima auren yayarta da ƙyar aka ganganɗa aka yi shi tun ba ta da wayo. Tana aure a can wata Karkara da ake noman rake, Maƙarfi. Ba su da wani dangi na kusa da za su yi tinƙaho da shi. Har gwara ma Uwale ita Babanta Malamin soro ne, ba kasafai suke tashi a babu ba. Dan dai gidan nasu gidan yawane.
Nan dai suka fara kaiwa Gareji, Uwale na sai da Rogo, yayin da Falmata ke sai da Wainar Gero.
A hakan ma duk wani na garejin sai da ya shaida amintarsu. Dan kuwa idan ɗaya ya sai da nasa baya taɓa tafiya sai ya taya ɗayan shi ma tasa ta ƙare.
Suna wannan rayuwar a wata ranar Litinin mazan biyu suka shigo cikin rayuwarsu. Gyaran Babur suka kawo gare jin. Sai dai tun shigowarsu gabaɗaya hankalin gudan yana Uwale. Haka ita ɗinma sosai take ta leƙensa tana yashe masa baki.
Tana kula da sanda gudan mai zubin Alarammomi ya ɗan zanguri wanda ya burgetan suka yi ɗan ƙus-ƙus suna dariya. Sai kuma taga ya dago yana mai tahowa gare su. Nan da nan ta hau ɗan gyaggyarawa tana gwada da murmushin da za ta tare shi. Sai dai kafin ta ida shiryawar har ya iso, ya kuma wuce ta ya isa ga Falmata da bata ma ankara da zuwansu ba.
“A ba Ni wainar”
Ya furta da murmushin da ya tsinka zuciyarta ta manta ɓacin ran da ya fara ta so mata. A karo na farko ta ji ba ta so Falmata ta ɗago ta dube shi balle ma ta ji abinda ita ta fara ji kansa.
Sai da aka gama zuba masa wainar, har ta fara fidda ran zai mata magana. Sai kuma ya dawo saitinta yana dubanta da fara’ar da take saka ta manta ko ita wacece.
“A ba mu kwatance, za mu zo roƙon iri. Zan rako Ɗan uwana.”
Jiki na rawa ta fara zayyana masa kwatancen har sai da Falmata ta ɗan zungureta tana mata ishara da ta nutsu mana.
Tunda ya tafi take ta sakin murmushi tana tuna fuskarsa. ‘Wallahi yana da kyau.’
“Shi wa?”
Tambayar Falmata ta ankararta ba a zuci yake maganar ba.
Shiru ta mata. A karo na farko ta ji ta kasa furta mata abinda ke ranta. Sai ma ta samu kanta da jin haushin ya sai wainarta ita bai sai kome gurinta ba.
“Uhum! Idan ta yi wari ma ji. Ana tambayarki kin wani sadda kai ƙasa kamar wata sabuwar Amarya.”
‘Na kusa zama ai.’
A daren ranar da ƙyar Uwale ta iya barci saboda ɗokin gobe zai zo gidansu. Duk da zuciyarta na jaddada mata bai fa saka rana ba.
Sai dai a ranar ne suka wayi gari da haihuwar yayarta da suke uwa ɗaya uba ɗaya wanda dole ita ce za ta tafi ta mata zaman biƙi. Haihuwar da har yau ba ta bar tsinewa ɗiyar ba, dan ita ma tana cikin waɗanda suka nesanta ta da Bashari.
Ba yadda ta iya haka ta shirya ta tafi tana bawa Falmata sallahun duk wanda ya zo nemanta ta riƙe shi karta bar shi ya tafi. Za ta dawo. Kuskure na biyu.
A daren ranar suka zo, abin Allah kuma kwatancen sai ya musu daidai da gidansu Falmatan. Ko da ta ji aiken da har ba za ta fita ba, sai kuma ta tuna saƙon Uwale, dan haka ta miƙe da hanzari tana son sanin wanda ƙawartata ke ta tunawa tana kwarara murmushi motsi kaɗan.
“Af! Kamar kinsan ke na zo nema dama.”
Ya furta yana gyara zaman zungureriyar tagiyarsa.
“Ba dai Ni ba, ta ba Ni saƙon ko da ka zo na riƙe ka karka tafi. Ita an mata haihuwa ne, ta tafi za ta dawo nan da sati.”
“Kinga wanda za ki riƙe nan. Shi ne ya ganta sama da sati yana so ya kasa furta mata har sai da ya ta so ni, Ni ma kuma na yi gamo da ke. Fatan za ku ba mu haɗin ka. Suna na Bashari. Wannan kuma Yaya na ne, shi kaɗai ya rage mini a duniya. Gun mahaifinmu muka tashi. Sai dai a yanzu babu shi bai daɗe da rasuwa ba. Sai dai tarin yan’uwa da abokan arziki. Muna zaune a Bebeji. Fatar babu wata damuwa.”
Shiru ta yi tana murmushi tana juya bakin gyalenta. Ita kam ya mata, musamman da ta ji su biyu suka zo nemansu. Abinda suka daɗe suna Fatansa ita yar uwarta. Haka a cikin hasken farin watan take hango cikar haibarsa. Dan haka ta gyaɗa kai.
“Shi ba ya magana?”
“Kinsan Alaramma ne, bai iya hira da mata ba, ta yiwu kuma dan bai ganta a kusa ba ne.”
“Ya yi haƙuri, za ta dawo ai. Ina dai Uwale ce na ba shi.”
“Kafin sati ya kewayo shaƙuwa mai ƙarfi ta ƙullu a tsakaninsu. Kullum suna tare, idan ba ya gidansu da dare, to kuwa za ka tarar shi wurin sana’arta.”
A sati na biyu da haɗuwarsu ya fara bijiro mata da batun aure. Shi fa zai zo gida kawai a tsaida lokacin biki. Dan kuwa duk sun gama shirin su da albarkar gonar gadonsu da ta rage musu.
Ita ɗin ma hakan take so kasancewar duk sa’anninsu sunyi aure dama. Sai dai fa ba yadda za a yi a tambaye ta ba tare da Uwale ba. Dan haka ta samu uwar Uwalen ta faɗa mata kome dan a aikawa Uwale wannan fa da ta ce a riƙe mata shi ɗin so yake ya fito.
A sanda Uwale ta samu saƙon ba ƙaramin farin ciki ta yi ba. Tunda ta tafi ba ta da aiki sai tunaninsa. Duk a takure take jinta, gashi an ce sati huɗu za ta yi. Wannan saƙon shi kwantar mata da hankali jin cewar shi ma son ta yake yi. Gashi har zai aure ta ba tare da ko sunanta ya sani ba, ko ya yi hira da ita. Dan haka ba ɓata lokaci ta ce a sanar masa ya je ya samu Malam ta amince. Kuskure na uku
Nan da nan kuwa kowane ɓangare ya amsa. Aka tsaida lokacin bikinsu watanni huɗu.
Ba a daɗe da hakan ba Uwale ta dawo, ta tarar da abin da ya ya sata suma sau uku a yini. Ya kuma tarwatsa duk wani buri da take da shi a duniya. Ya rusa kyakkyawan zumuncin da ke tsakaninta da Falmata. Ta zame mata maƙiyar da ba ta ƙi ta tsira tsinin mashi a tsakiyar maƙogwaronta ba.
Mutumin da take mafarkin ta gama mallaka, take jinsa daidai da numfashin da take shaƙa bai fishi muhimmanci ba, ba ita yake so ba, ‘yar uwarta maƙociyarta yake so. Har ma ya tsaida lokacin aure da ita. Yayansa kuma, wanda suke jini ɗaya shi ke sonta. Har ma da yawunta ta tura shi gurin mahaifinta a rashin sani, an tsaida lokacin aurensa da ita. Abinda ko karen haukane ya cije ta ba za ta koma gurin Malam ta ce ba shi take nufi ba, ba shi take so ba, ƙaninsa saurayi ga Falmata shi take so, shi kuma take nufin ta turo. Wannan abu ne ta sani da ba zai taɓa yiwuwa ba ko da kuwa a mafarkinta na barcin safe. Tana tuna sau uku Malam ya turo yana tambayarta ita ta wuro wane. Tana ba da amsa da eh. Ƙarshe ma har korar ‘yan aiken ta yi ganin ana ta tambaya kamar ba a son a ba ta shi. Abinda ba ta sani ba shi ne, Malam na ta nanata tambayarsa ne ganinsa da ya yi Alaramma, bai burge shi ba sam, a matsayinsa na Malamin soro irin mutanen nan na yawan kawo matsala da wannan haram ne wannan makaruhi ne. Wannan abu ne da ba za ta taɓa yafewa kanta ba, haka Bashari. Dan kuwa ai ita ya fara gani, tana tunawa har murmushi ya mata. Me ya sa sai da ya kula tana rawar jiki kansa zai komawa Ƙawarta?Ko bai gane shi take so ba? Wane irin zalunci ne zai sa ya haɗa ta aure da yayansa, saboda karma ta yi zaton za ta same Shi ko? Menene Falmata ta fita? Ta ga dai ta fita manyan idanu, ko kuwa dan nata jajaye ne? Amma ai ta fita hasken fata, ko kuwa shi duka wannan bai burge shi ba? Waɗannan wasu tambayoyi ne da taje ta zube a gabansa ta kwarara masa su. Ya kuma amsa mata da hujjojin da suka tabbatar mata Bashari bai taɓa sonta ba daidai da kwayar gero. Ya tabbatar mata dama yayansa ya rako ya ganta. Murmushin kuma da take zaton ita ya yiwa. Ya yi ne a matsayinta na wadda Yayansa zai aura. Ta zube a gabansa a kan gwiwowinta, tana roƙansa da ya hakura da Falmata ya dawo gare ta, ya ji ƙanta ya duba girman soyayyar da take masa ya aure ta. Ta yarda idan Falmatan ce ita ma ya aure ta. Amma ya ce a’a. Falmata kaɗai yake da ra’ayin aure, ba ma yada damar auren mace sama da biyu. Ta ce masa idan wannan ne ba damuwa ko sadaki za ta ba shi ya biya. Ya ce a’a, shi fa tsakani da Allah ma idan ta matsa masa zai sanarwa Falmatan dan ta san irin zaman da za ta yi da ita. Tsoron hakan ya sa ta barshi da zancen da wani da mummunan ƙuduri cikin ranta. Sai dai abinda ba ta sani ba shi ne, da ace an faɗawa Falmatan da ta gane wacece ita a rayuwarta. Falmata za ta iya bar mata kome, za ta iya bar mata kome ciki harda mijin da take aure. Zuciyoyinsu ba iri ɗaya ba ne.
Amma kuma da Allah ta yi rantsuwa ba za ta taɓa barinsa ya ji daɗin auren ba, yadda ita ma ta tabbata ko wa za ta aura, ko da ace zai bata duka daɗin duniyar nan to fa ba za ta ji daɗi. Mutum ɗaya ne take so ya kuma mata nisa. Ƙudurinta ba za ta barsu su haihu ba, ita ba za ta haihu ba haka shi ma ba zai haihu bare ‘ya’ya su shiga tsakaninsu ya ƙara yi mata nisa. Dan haka ta haɗa kai da wani yaron Babanta da aikinsa yake kamar yankan wuta. Ya mata aikin da ya bata tabbacin duka su biyun ba za su haihu da su ba.
A haka har lokacin bikin ya zo aka fara shirye-shirye ba ta taɓa bari Falmata ta gane soyayyarta ga mijin da za ta aura ba. Ba kuma ta fasa bibiyarsa ba dan akwai ranar da ta mamaye shi ta shige cikin kirjinsa tana kukan ya aure ta. Marin da ya aza mata saman fuskarta ne ya sata dawowa hayyacinta, daga ranar kuma ba ta ƙara kuskuren tsayawa kusa da shi ba, sai dai fa ya dasa mata mummunan ƙiyayyar Falmata a ranta.
Anyi biki lafiya an gama kowacce ta tare a muhallinta. Ba gida ɗaya suke ba, sai dai tazarar da ke tsakaninsu babu nisa. Anan garin Bebeji suka zauna.
Da ke abin na Allah ne sai gashi ba a rufe wata ba duka su biyun sun samu ciki. Wannan abu ba ƙaramin tada hankalin Uwale ya yi ba ganin Falmata ma ta riga ta samu ko ace nata ya riga fara nunawa. Ta yi duk ‘yan dabarunta dan ta samu ta zubar da cikin ta hanyar ba ta abinda tasan zai fitar da shi, amma duk a banza. Ƙarshe dai ta zubawa sarautar Allah ido, har suka isa lokacin haihuwarsu kowacce ta samu albarkar ɗiya mace. Ta wajen ta ci sunan Hafsa(Hansai) Yayin da ta wajen Falmata ta ci sunan Faɗima(Faɗime).
A haka suka ci gaba da tafiya har bayan shekara Bakwai. Zuwa lokacin Uwale ba makircin da ba ta ƙulla ba na ganin Bashari ya kori Falmata amma abin ya ci tura. Idan ma ta haɗa su abin ba ya wuce kwana biyu sun shirya. Ƙaunarsa kuwa ta yi nisa cikin ranta da take jin kamar ta yi hauka. Ko alaƙa take yi da Malam ba shi take gani ba, Bashari kawai take gani cikin idanuwanta. Ana hakan ne watarana ta shiga gidan tana neman su Hansai, kunnuwanta suka zuƙo mata maganganun da suka sakata ɗaukar matakin da har yau ba ta fara nadamarsu ba. Falmata ta gani cikin ƙirjin Bashari tana kuka, yana rarrashinta, yana furta mata sirrin da ke tsakaninsa da ita, ya kuma rantse mata, ya sake rantsuwa da abinda zai kashe shi cewar ba zai taɓa auren Uwale ba ko da kuwa shi da ita ne kawai zasu rage masu numfashi a doron duniya. Wannan shi ne furucin da ya kiɗimata ya hargitsa tunaninta ta ruga da gudu zuwa gidanta, ta sunkuto galan ɗin Fetur na Babur ɗin Malam, ta haɗo da Ashana, ta dawo gidan ba tare da sun ankara da ita ba, ta zazzaga fetur ɗin a labulayen ɗakin, ta wawwatsa a dankin zanan dake saman ɗakin. Ta jefa galan ɗin da abinda ya rage masa cikin ɗakin. Suka ɗago suna dubanta da tsoron da ta gaza mantawa. A haka tana hawaye ta ƙyasta Ashanar ta jefa ciki. A kan idanuwanta suka taso za su fito, sai dai Asabarin da ya tokare ƙofar yana cin wuta shi ya hanasu fitowar suka ruƙunƙume juna cikin fidda tsammani da rayuwar. A haka ta fice daga gidan a bayan ta jawo ƙofar gidan. A cikin ranta ba ta ji abinda ta yi kuskure ba ne. Ta gwammace su mutu, ta gwammace ta kai su inda ba za su ƙara wanzuwa gabanta. Ba Falmata kaɗai ta kashe ba, a jikin Falmatan akwai ɗan ta yi. Da shi ta haɗa ta kashe. Da tsohuwar mahaifiyar Falmata kaka ga Faɗime ta haɗa ta murƙushe duk saboda wata halitta kwalli ɗaya da take so!