Skip to content
Part 37 of 37 in the Series Fadime by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Da idanu take kallon kowa yadda ake ta shirin bikin ɗan lelen Hajiya. Sai gyarata ake yi cikin ƙamshi zuwa kayan mata na ‘yan asalin Maiduguri. Fatima ‘Yar mutan Borno aka gayyato domin kawai ta zo ta gyara amarya. Duk wanda ya kalli Faɗime sai ya sake kallo. Ita dai bata um bare uhum wai Uwar gulma ta yi cikin shege, sai dai ko me aka ce ta yi bata musu.

Ƙawarta Linda da Yayanta suka faɗo mata a rai da suke can a rufe duk a dalilinta na ƙin Sagir, gashi a yau Ubangiji ya gwada mata ƙarfin ikonsa na duk abinda ya faru da bawa dama can rubutacce ne gare shi. Hawayen ta goge tana jin wani irin abu na sukarta. Ta tuna Abbati dai ya guje su gabaɗaya yana gun Hajiya.

An ɗaura aure lafiya, haka da yamma aka ƙaraso da Zuby gidan Hajiya daga gidan za su wuce wajen Dinner da aka haɗa musu, daga can kuma kai tsaye gidan miji za a dire su.

Faɗime ta rasa a irin halin da za ta kira kanta tana ciki. Farin ciki ko akasin hakan? Tunda aka ce ga amarya can an kawo ta rasa dukkan natsuwarta. Da gaske da za a bata wuka ace wa za ta kashe babu shakka Zuby ce mace ta farko.

Wata daga cikin dangi ta shigo tana dubanta, “An kawo miki kayan Dinner ɗin da zaki sa, wanda Sagir ya aiko ya ce ki yi sauri da kansa zai kwashi Matansa zuwa wajen.”

Sunkuyar da kanta ta yi ba tare da ta iya cewa uffan ba. Kayan da aka ajiye mata ta ɗauka tana kallo tana sake dubawa. Sam! Basu burgeta ba, jikinta ya bata iri ɗaya ne da na me kama da Turmin can. Dan haka ta cillar da kayan ta buɗe Akwatinta ta ɗauko wani sabon Material bata taɓa saka shi ba. Kawai tasa. Ta zauna da kanta tayi ɗauri sannan ta zuba awarwaro da sauran tarkacen. Duban kanta tayi a madubi, a karo na farko tun wayewar garin ranar da murmushi ya wanzu a fuskarta.

Duk wanda ya shigo sai ya hau faɗin kyan da ta yi. A hankali aka sauko da ita har bayan motar. Ta sani Zuby ta jima da shiga, haka shi ma Sagir ɗin ya ja tsaki yafi a ƙirga saboda irin ɓata musu lokaci da ta yi.

Sai dai tana shigowa motar komai ya kwance masa. Ita kanta Zubyn sai da ta raina kanta duk kuwa kurara kanta da ta gama yi gaban mirror. Haka ta zuba masu idanu tana kallon shigarsa da na Faɗime kusan iri ɗaya, kala ɗaya sak. Ranta ya ɗan sosu sanin ya ce mata kayanta irin nata ne, amma sai ta share kawai.

A hankali Sagir ya kamo hannun Zuby yana dubanta ganin kamar yanayinta ya canja. “Kin yi kyau sosai, ji nake kamar in sace ki in gudu, kamar daga nan mu zarce gida kawai.”

Ai kuwa tarkon da yake son ɗanawa tuni ya kama masa abinda yake buƙata. Dan kuwa Fadime kawar da kanta ta yi tana jin kamar ta cewa Driver din ya tsaya ta sauka.

Farin ciki ya kama Zuby, tayi Farr! Da idanu, “Na gode Noorie.” Tana jin duk irin hirar da suke yi sai ta ɗauke kanta kamar bata san suna yi ba.

Haka suka isa wajen Dinner din. Duk abubuwan da aka yi babu wanda ta ɗaga kai ta kalla. Har aka tashi ranta a jagule yake. Kowaccen su aka direta a ɗakinta, babu bata lokaci kowa ya kama gabansa aka bar Ango da Amarensa.

A babban falon da ya zama yana tsakiya ya hada su ya yi masu ‘yar nasihar da zai yi sannan ya dubi Faɗime ya ce. “Yau kwananki ne a matsayinki na babba.” Faɗime ta ji kamar ya watsa mata fetur daga ƙarshe ya ƙyasta ashana. Duk da a wani ɓangare na zuciyarta ta ji daɗi da aka fara ɗaurawa da ita. Girgiza kai kawai ta hau yi, cikin ɗakiya ta ce.

“Na yafe ka tafi ɗakin Matarka. Ni roƙona anan kawai a dawo mini da Abbati gabana. Idan na shirya karɓar girkin da kaina zan yi magana.”

Har zuciyarsa bai ji daɗin kyautar da tayi da shi a rana mafi mahimmanci irin wannan ba ko da kuwa ba za a taɓuka kome ba. Amma sai ya dake ya ce. “Okey Amarya tana godiya da wannan kyauta. Abbati kuma kin fi ni sanin inda yake ki je ki dauƙo shi ba ni da matsala.”

Tabbas ta fi shi sanin inda yaron yake, haka ko giyar wake tasha ba za ta taɓa fara tunkarar Hajiya da wannan maganar ba. A wautarta idan ta yi kyauta da shi zai damu ne, har ma ya ce bai amince ba. Sai dai a gaban idanunta ya jawo hannun matarsa suka shige ciki.

Zuby har waigowa ta yi tana kashe mata ido. Burinta ya gama cika, ta gode Allah, ta godewa Tsohonta da ya nusar da ita. A lokacin da Sagir ya ce mata su biyu zai aura kaɗan ya rage a rufeta a gidan mahaukata na Sokoto. Sai da ƙarfin rubutu da nasiha ta dawo hayyacinta. Dama banda yaudarar kai ai tasan Sagir ba zai taɓa rayuwa da ita ɗaya ba, dole zai auri wata, sai dai ba ta za ci a kusa ba ne ƙarin. Amma da ta yi haƙuri gashi taga ribarsa, ranar farkonma an bar mata. Ita kam ba ta ga wautar da za ta saka ta barwa kishiya kwananta ba ko da kuwa mijin na yankar namanta. Kanta a kumbure haka ta juyo ta rufe ƙofar a fuskar Faɗime.

Shuru ta yi takaici na daɗa cikata da tarin nadama. Haka taja jikinta ta shige ɓangarenta. Tun tana daurewa har tsakar dare ta miƙe a tsakiyar gadonta tana risgar kuka kamar ranta zai fita, idanunta suka kumbura. Shi kenan wata ta gama sanin Sagir ɗinta a ɗa namiji. A haka ta kwana tana juye-juye da ƙisseme-ƙisseme.

Da safe bayan ya tashi ya yi wanka ya kintsa ya je ƙofar ɗakinta ya yi ta kwankwasawa bata buɗe ba. Haka ya gaji ya ƙyale ta. Wasa-wasa har ƙarfe ukun rana bata buɗe ɗakin ba. Wani Key ya je ya ɗauko ya yi amfani da shi wajen buɗewa. A zaune ya sameta idanun nan sun kumbura saboda kuka. Zaro idanu ya yi, “Subhanalillahi. Kuka kuma? Me aka yi maki ke kuwa?”

Haushinsa yasa ta kawar da kanta gefe ta ce, “kawai ina son ganin Hajiya ne ka kai ni gurinta.” Girgiza kai ya yi, “Wannan ɗan dalilin bai kamata ya saka ki kuka ba, shekara nawa baki tare da ita ma. Idan na kai ki yanzu Hajiya zata yi mini Faɗa. Ki bari ayi kwana biyu na yi alƙawarin da kaina zan ɗauke ki ke da Ƙanwarki in kai ku ku wunin mata.”

Baki Buɗe kawai ta yi tana kallonsa. Tana kula da wani rawar kai da yake yi kamar wanda aka yi masa albishir da shiga Aljannah. Kai ita Allah ya isa ma da Zuby ya kira ta wai ƙanwarta. Matar da a cikin idanuwanta kawai ma za ta bata shekara bakwai. Ta tsani tana magana yana sanyo mata ita.

Ganin ba ta yi magana ya saka shi fita yana bata umarnin ta fito ta musu abincin dare. Zuby ta gaji sosai da ɗawaniya da shi, shi kuma ba zai iya fita siyo abinci ba. Wanda aka aiko musu da shi kuma sun cinye har da yaran gidan.

A haka ya ja mata ƙofar bai ji mummunan tsakin da ta sakar masa ba.

Miƙewa ta yi ta faɗa toilet ta yo wanka ta kintsa kanta cikin korayen riga da siket na wani lallausan koren leshi. Fitowa ta yi da zummar shiga kitchen ta samawa cikinta mafita. Sai da ta kai tsakiyar falon idanuwanta suka hango mata abinda ya tsinka yawun bakinta. Zuby ce zaune a bayan Sagir yana mata doki tun daga cikin ɗakinta har ƙarshen falon. Suna ta ƙyaƙyata dariya abinsu tamkar ma basu san da wanzuwarta gurin ba.

Takaici ya ƙume ta har bata san lokacin da ta saki tsaki me ƙarfi ba, ta juya da sauri ta koma ɗakinta. Ranar ba ita ta ci abinci ba sai bayan ƙarfe tara da ta daina juyo motsinsu a falon.

A kwanaki bakwan da Zuby ta yi na ranakunta ba ƙaramin juriya ta yi ba da bata daddatse yan ƙafafunta ba. Ita taga Bariki tsirararsa. A gabanta Zuby ke kwaɓewa Sagir kaya su wuce ɗaki ta masa wanka. A idonta yake tauna abinci a bakinsa Zuby na cinyarsa yana dura mata suna lasar juna.

Abun bai fara fin ƙarfinta ba sai a daren da bakwan Zuby ta cika ta fito falon ta hange su Dining ta daddage tana zuba masa abinci.

Ranta ya ɓaci a karo na barkatai. Ta tuna ita ma fa macece kuma tana sonsa. Ta tuna mijinta ne fa ya riga da ya zama dole ta aje kome saboda zunubi, idan shi ya nuna bai buƙata sai ta ƙyale shi. Tuna hakan ya saka ta dire kofin hannunta ta taka da sauri gurinsu. Ba su ankara ba suka ganta tana tattara abincin zuwa gabansa, ba tare da ta ɗaga kanta ba ta ce.

“Bar shi na gode, lokacina ne”.

Ba Sagir ba, hatta Zuby tasha mamaki, dan haka ta yatsine fuska ta juya idanuwa irin na daga baya ke nan. Ta yi ɗakinta tana kaɗa mata mazaunanta irin na Agwagwa.

Hannunta na rawa haka take ta loda miyar cikin shinkafar har bata san sa’adda ya tashi ya kewayo ta bayanta ba, sai jin kansa ta yi a jikin wuyanta yana mata magana cikin kunnuwanta.

“Ya isa haka Fati, ya isa, kinga shinkafa ce ba tuwo ba ne.” Dire ludayin ta yi tana runtse idanuwanta da ƙarfi hawayen har sun fara sauka. Ji take har yanzu zuciyarta ta ƙi yi mata sanyi.

“Subhanallahi! Menene kuma? Me na miki?” Ya furta yana juyo da ita saitinsa. Sai kuma ya zaunarta a kan kujerar dining ɗin, ya ciko tambulan da ruwa ya miƙa mata. Da hannunsa ta haɗa ta riƙe tana dubansa a marairaice.

Ganin haka ya saka shi duƙawa saitin gwiwowinta. Yasa hannu a hankali ya ɗauke mata hawayen fuskarta.

“Menene Fati, ki faɗa mini zan fahimce ki. Kukan nan ya ishe ni haka.”

Da ƙyar ta sassauta kukan ta buɗe baki.

“Wallahi Allah shaidata ina sonka, Allah kuwa.”

Ba ƙaramar dauriya ya yi ba wurin hana dariyar suɓucewa. Duk da ya yi mamaki da jin kalaman, sai dai yadda ta furta da haƙiƙancewa da tarin yarinta dole ya ba shi dariya.

Ganin ya yi shiru kawai yana kallonta ya sata tunanin bata burge ba. Dan haka ta muskuta a sanyaye za ta miƙe, ya yi saurin tashi yana duban cikin idanuwanta. Sunkuyar da kai ta yi saboda ba za ta iya jure kibiyoyin da ke harbinta daga cikin baƙin kwayar idonsa ba.

A hankali ya cika muradinsa ta hanyar jawota gabaɗaya tsakiyar ƙirjinsa, suka sauke ajiyar zuciya a tare suna daɗa ƙanƙame juna. Cikin kunnuwanta ta ji sautinsa.

“Fati ban taɓa jin ina ƙaunar wani abu a rayuwata kamar ki ba. Soyayyata gareki ba ta da ƙarshe. Ƙi yi mini Alƙawarin ba za ki Kara nisa da ni ba. Ni kaɗai nasan yadda na kawo i yanzu da wannan ciwon. Ki yi haƙuri dan Allah, ki yi haƙuri, ki manta…”

Kasa ƙarasawa ya yi sakamakon lalubar harshensa da ta yi da nata salon tana girgiza kai na bata son zancen cikin hawaye. Abin ya kiɗimashi gabaɗaya har bai san sa’adda ya sureta gabaɗaya ba ya dire ta a tsakiyar gadonta. Tana sambatun ya yafe mata yana sambatun ta yafe masa a haka suka nausa rayuwarsu.

“Kinsan Allah sai kin tashi”.

Ya furta yana mata tafiyar tsutsa a ƙafa. Janye ƙafafun ta yi ta ƙara ƙudunduna cikin bargonta, da barci sosai cikin idanuwanta.

Ganin haka ya saka shi ɗaga bargon gabaɗaya sai ji ta yi yana goga mata gashinsa da ke ta ɗigar ruwa a wuyanta da doguwar rigar jikinta ba ta rufe ba.

“Allah ba na so.”

Ta furta tana ture shi.

“Ki tashi ki ji wata gulma”.

Jin ya ce gulma ya sakata zabura ta miƙe zauna.

Ya kuwa tuntsire da dariya yana kallonta.

“Kai mata kun shiga uku, ji be ki ko kunya.”

Ta zunɓuri baki tana ƙoƙarin komawa, kome ta tuna sai kuma ta ɗan nutsu tana dubansa.

“Abban Abbati dan Allah ka yafewa Linda da Yaya?”

“Na yafe, ya wuce har abada!”

“Ni ma kin yafe mini abin nan?”

“Me fa?”

“Na jiyan nan? Dan Allah Yaya kar ka mini ciki.. Dan Allah.. Wayyo Hajiyata zai mini ciki.”

Ya furta yana kwaikwayon muryarta.

Ta kuwa miƙe ta yi kansa.

A’a tsaya kiji.

Ta ɗan dakata tana harararsa.

“Ɗan faɗa mini da ina da ina wannan Mahmudan ya taɓa taɓa miki?”

Kwafa ta yi kafin kuma ta yi murmushi mai kyau.

“Kawo kunnanka ka ji to.”

Ya matso da sauri harda saƙalo wuyanta.

Ta kuwa lalubi kunnen ta gartsa masa cizo.

Ya ɗanyi ƙara yana shafa gurin. Sai kuma ya kwakkwaɓe fuska yana dubanta a marairaice harda lanƙwashe kai.

“Wallahi Allah shaidata ina sonka, Allah kuwan.”

Ya furta da irin sigarta.

Ta kuwa ƙule ta biyo shi da gudu ya yo falo yana mata dariya. Har ta yi nasarar riƙe shi tana kallon ƙofar Zuby.

“Ba dan halina ba ka raba mana gida.”

“Ba dan halinki ba Abuja ma za mu koma, kina ƙasa tana sama.”

Ta yi wani tsalle ta ruƙunƙume shi. Daidai nan Zuby ta fito, ganinsu ya sakata mazewa za ta koma ya kirata.

Ta taho ba yabo ba fallasa ta tsaya gefensa.

Sai kuma ya kalli wannan ya kalli wannan kafin kuma ya tuntsire da dariya harda riƙe haɓa.
“Oh Ni Sagiru Autan Hajiya, wai mata biyu gare ni? To Allah ya bar ni da ku.”

Ya ƙarasa yana cuno baki yadda Zuby ke yi. Hakan ya basu dariya suka furta Amin a tare.

Ƙarshe!

Alhamdulillah! A karo na barkatai ni Ɓingel na kammala littafi guda. Na gode sosai da jimirin bibiya. Na gode ga ƙungiyar Fikra. Na godewa kowa da duk wanda ya ba ni gudunmawarsa cikin rubutun nan. Allah ya bar zumunci.

Sai mun haɗu a Hakabiyya idan da yawan rai.

<< Fadime 36

4 thoughts on “Fadime 37”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×