Skip to content
Part 28 of 30 in the Series Falsafa by Haiman Raees

MUN GODE RABBA 

Alhamdulillah, Ni dai na gode Rabba.

A’uzubillah, neman tsari ni ke yi ga Rabba.

Sai Bismillah, zan fara da sunanKa Rabba.

Kai ke da raina, Allah Ka yafe wa Abba.

Haɗa har da Ummi, da ni kaina da Baba.

Tsira da aminci, Allah Ka ƙaro ga babba.

Manzona ɗan Amina, da ya wuce duk wani babba.

Allahu ka yi mana komai, ba ko da ko kwabo ba. 

Iska mu shaƙa, mu wataya ba da hantara ba. 

Bacci mu yi, mai isarmu ba da mun biya ba.

Ɗanɗano na lasa, harshen ba a hana ba. 

Bawali mu yi shi, hutu ba da fargaba ba. 

Ga jinin jikinmu, yana ta gudu ba da ya zube ba. 

Ruwan jikunanmu, ga su nan ba da shamaki ba. 

Rayuwar mu duka jimla, muna yinta ba da mun biya ba.

Ai ko domin wannan, bauta ba ma ƙi yi ba. 

Mu tuna dangina, imani ba siye mukai ba.

Manzon tsira, da ya zo mana ba wayonmu ne ba. 

Kyauta ce aka ba mu, bisa ni’imarSa babba. 

Ka gani da idonka, ba tare da ka biya ba. 

Ka ci tuwo da hannu, har ma ka suɗe yatsu da laɓɓa.

‘Ya’ya ka haifa, ba fa sai ka siya ba. 

Kyautar Ilahu na da yawa, jero su duka ba za iya ba. 

Haiman Raees na Kaduna, na gode Rabba. 

Mutanen Arewa duka, muna godiya ga Rabba. 

Sarki guda ɗai, da bai da Ummi balle fa Baba. 

<< Falsafa 27Falsafa 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×