Skip to content
Part 12 of 30 in the Series Fasaha Haimaniyya by Haiman Raees

WAKAR CORONAVIRUS

Bissmillahi Jallah sarki

Sarkina Ubangiji mai mulki

Kai ne silar zuwansa Ma’aiki

Manzona da ya fi kowa kirki

Da Sahabbai mutanen kirki

Tabi’ai har malamaina ‘yan kirki.

*****

Haiman a yau zan fara batuna

Babu sarki sai Allah a wajena

Za na y waƙe akan cutar Corona

Wacce ta zagaye dukka garina

Tana ta ɗaukar rayukanmu da rana

Allah ka kawo mana sauƙi da ni da duk ‘yan uwana.

*****

Mun wayi gari a yanzu kowa na ɓuya

Babu babba babu yaro babu ko mai talla akan hanya

Cutar Corona na kashe yara har da manya

Da talakka da mai kuɗi da masu jinya

Ƙare dangi take ta yi a ko’ina ba sanya

Ya ku jama’a ku mu gane dujal yana kan hanya.

*****

Gamu nan yau muna ta kuka ba baƙauye babu na birnina,

Babu yaro ba wani babba ba mace ba jinsi na,

Ba na sama ba na ƙasanmu su ƙannena

Ba bazara ba rani balle damuna

Wahala ta yi mana tsauri ya Rabbana

Ga mu mun tuba ka yafe mana.

*****

Ƙarshen duniya ya matso alamu na ta bayyana

Mutuwa dai tana zuwa gareku har ma guna

Ko ka gudu ko ka tsaya ko kana gida ko gona

Mutuwa zata iske ka aboki da ‘yan uwana

Ko da shiri ko babu abokaina

Kuma ba wanda zai rage tun da har ta ɗau Manzona.

*****

Mu daina dariya da nishaɗi da yi wa juna barka

Da cewa ai fa da saura a cikin rayuwarka

Mu roƙi Allah dare da rana kar mu je gun boka

Kuma kar tsoro ya sa mu je mu faɗa shirka

Kar mu manta addu’a da halin barka

Kawai mu koma ga Allah zai mana maganin duk wata cuta.

*****

Duniya dukka ta jigata babu sauran watayawa,

Hatta Jakin da yake cin harawa,

Ya san duniya ta sauya tunda babu sukunin yawatawa,

Bar batun baƙin fata ko baturen yammatawa,

Duniya kaf tana ta kuka da zuwan cutar Corona,

Rabbana mun yi nadama a gare ka mu ke ta tuba.

*****

Muna tuba a gare ka ubangijina sarki kai ke da kowa,

Mun yi tawassili da ƙur’ani magani ga komai,

Mun yi sujjada gare ka Rabbana kai ke da kowa,

Muna ta roƙo a gareka Rabbi kai ne kake da komai,

Ka yafe mana laifukanmu kar ka bar mu da wayonmu,

Domin in ka bar mu da wayonmu babu sauƙin da za mu samu.

*****

Cutar nan ta Corona Rabbana ta dame mu

Cutar nan ta Corona tana shirin ƙarar da mu

Cutar nan ta Corona Rabbana ka kiyaye mu,

Ka tsare mu ubangijinmu da mu da iyalanmu,

Ka yaye mana ita a gida har ma garinmu,

Da maƙwabta da duniyar mu don mu samu zaman lumana.

*****

Rabbana albarkar watan Ramadana ka sa cutar nan ta bar mu,

Rabbana ka sa ta tafi don mu samu shiga garinmu,

Ka sa ta zamo labari a kunnuwanmu,

Watarana mu yo zance da tunanin ta a rayuwar mu,

Ta zamo mana tarihi abin tunawa a tsakanin mu da juna.

Zan ɗan tsaya a nan wajen don na sarara

Allah tsare mu da mugun gani irin na asara

Da mugun ji ko gida ko da can a sahara

Ka tsare mu da ga dukkanin taɓara

Kai ke da ikon komai Allah Jalla tabara.

<< Fasaha Haimaniyya 11Fasaha Haimaniyya 13 >>

2 thoughts on “Fasaha Haimaniyya 12”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×