Skip to content
Part 21 of 30 in the Series Fasaha Haimaniyya by Haiman Raees

Hawaye

So ne ya sani gaba

Don gashi a yau

Ina fargaba

Zuciya tana marari

Don Allah ki zo

Ki yi mata zabari

*****

Ƙaunarki ce ta sani hawaye

Ai son ki ne ya sani hawaye Begenki ne ya sani hawaye

Ƙaunarki ce ta sani hawaye

Ƙaunarki ce ta zam min farincikina a koda yaushe

*****

Mai sona

Mai sona

*****

Masoyiyata

Don Allah karki barni

A sama in maƙale

In kika barni

Komai da ke gare ni

Dole zai dagule

Habibiyata

Don Allah sai ki so ni

Kada in sagale

In kuma kika ƙi

Na san zan koma

Tsummar da aka sagale

*****

Domin ki ne nake yin hawaye

Ƙyale su sui ta gulma wawaye

Auren ki ni nake yin fata ye!

‘Ya’yan mu ya zamo kin haifa ye!

Ƙaunarki ce ta zam min farincikina a koda yaushe

*****

Mai sona

Mai sona

*****

Zara kin haska gari

Birni da ƙauye

Kin cinye gari

Zuciya tana fahari

Da murmushin ki

Take fahari

Domin ki ne nake yin du’a eh

Ƙyale su sui ta gulma guntaye

Auren mu ya zamo an ɗaura ye!

Gidana ki ta haifo ‘ya’yaye

*****

Mai sona

Mai sona

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.8 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fasaha Haimaniyya 20Fasaha Haimaniyya 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×