Skip to content
Part 23 of 30 in the Series Fasaha Haimaniyya by Haiman Raees

Ki So Ni

Kar ki guje ni ‘yan mata

Gara ki so ni ai ya fi.

*****

Ya abar so nai sallama a gare ki

Nai gaisuwa ta girma a gare ki

Yaya kike shin ina kwanan ki

Huta kawai dai ki sha kurumin ki ‘yan mata

*****

Ni dai ka daina bina bana so

Me ma yasa kake min kallon so?

Dama ka daina don bana so

Da ace fa in so ka gara na bushe don ya fi

*****

Haba Sahiba ni ina ƙaunarki

Kuma zuciyata tana mararinki

Kyawunki ke sani in ta mafarki

Ko zan mace ni ina ƙaunarki ‘yan mata

*****

Lallai fa yau ni ko na ga ta kaina

Ga mahaukaci yau yana fa ta bina

Wai shi so yake ya nunan ƙauna

Je dai kawai kai bara fa ka barni don ya fi

*****

Ni na yi hauka akan ƙaunarki

Don na yi nisa cikin begenki

Ko me kike so fa ni zan baki

Da ki ƙini ai gara ma in sheƙe don ya fi

*****

Don Allah ɗan uwa karda ka sheƙe

Kibiya ta ƙaunarka tuni ka feƙe

Ta soke ni ba batun yin feleƙe

Da ka sheƙe ai gara in aure ka don ya fi.

*****

Nai godiya gunka sarki Allah

Da ka ba ni ‘ya wacce bata da illa

Zuciya yau fa zata bar yin ƙwalla

Hadarin so ya haɗu ruwan so na yayyafi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.8 / 5. Rating: 6

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fasaha Haimaniyya 22Fasaha Haimaniyya 24 >>

1 thought on “Fasaha Haimaniyya 23”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×