Mujahid kawai kama hannun Jamil yayi ya fito dashi gurin da Momin Zahra take yace" wannan ita ce Mahaifiyar Zahra su kuma sauran duk ƴan uwanta ne, tsohon can shine kakan ta".
Jamil duban Momin yayi idonta yayi ja ga kamanin Zahra kwance akan fuskarta.
Ya tsuguna ya gaida Momi tare sauran waɗɗan da suke gurin duk da a cikin ruɗani yake.
Ya juya ya bar gurin zuwa dakin da Zahra take ya shiga ta kifa kanta akan katifar da Mama take tana kuka a hankali ya dafa ta.
Tana dagowa yace" zo muje " ya riketa daman ta ajiye Ajmal. . .
