Ina cin dankalin ina tunani a raina na irin zaman da zanyi da mutumin nan wanda ko sunan shi barin ce na sani ba har yanzu, na ji dai ko da abbu ma ya fada amma ba zance na rike ba. Ni banga yana faraa ba ma, oh zanyi rayuwar kunci indai haka zan zauna ni kadai a gidan nan. A rayuwa kullum burina in samu miji da zai ganni yace yana so na tsakani da Allah sannan ya bani kulawa kamar dai yanda naga a fina finai na India suna yi. Kar ku ga laifina, ba ma kallon fina. . .