Skip to content
Part 4 of 6 in the Series Fudayl by Aysha I. Ahmad

Ina cin dankalin ina tunani a raina na irin zaman da zanyi da mutumin nan wanda ko sunan shi barin ce na sani ba har yanzu, na ji dai ko da abbu ma ya fada amma ba zance na rike ba. Ni banga yana faraa ba ma, oh zanyi rayuwar kunci indai haka zan zauna ni kadai a gidan nan. A rayuwa kullum burina in samu miji da zai ganni yace yana so na tsakani da Allah sannan ya bani kulawa kamar dai yanda naga a fina finai na India suna yi. Kar ku ga laifina, ba ma kallon fina finan Hausa a gidanmu, tashoshin mu gaba daya larabci ne shiyasa, suma India din sai serials da suke muke kalla ba kowane shirme ba.

Ina shiga damuwa sosai saboda rashin samun miji na kwarai gashi ina zaune a gida ba wani abun yi, Abbu yace shi yafi so sai nayi aure in ma zan cigaba da karatun ne saboda jami’an nan tarbiyyar yara na lalacewa duk da yasan tarbiyyar da suka bamu bazai sa mu kauce ba amma hakan yake ga shine mutunci kuma na gamsu shiyasa ban damu ba.

Ina gida har Haleefa ya tafi jami’a shima, ya Abba kam yana can India karatun likita da Abbu ya sama mai scholarship (daukar nauyin karatu) da gomnati ke bayarwa, ina alfahari da Abbu na saboda irin haka, sanin manyan mutane na gomnati yasa Abbu yake kokarin yi, indai ka same shi zai kokarta yaga ka samu musamman yaran da iyayen su basu da halin biya masu kudin makarantar kuma Allah da ikon sa gomnan da ke mulki a wannan lokacin mutumin sa ne sosai duk da yake Abbu kan ce shi ba ruwanshi da siyasa amma suna tare da shi sosai tunda sun san ya musu suma lokacin da basu samu mulkin ba, yanzu ne dai da harkokin suka yi baya amma Alhamdulillah ana dan samu ba laifi.

Rayuwar gidanmu rayuwa ce mai sauki kuma mai ban sha’awa saboda kulawa da muke samu daga Ammi da Abbu, mu kuma baka jin kanmu, karami bazai raina na gaba da shi ba kuma muna son junanmu shiyasa har a unguwar da muke ana yaban gidanmu dan bamu da kwaramniya ko ka ganmu a layi muna wasa a’a muna gida kullum. Daga makaranta sai islamiyya sai ko in zamu gidan yan uwa ko wani aika haka shima direban Abbu Malam Idi ne ke kaimu.

Muna zama da su Abbu kusan sau uku kowace rana, da safe lokacin karyawa muna haduwa a wurin cin abinci a babban falo, Abbu ne ke fara diba sai Ammi sannan ya zagayo kanmu ko kuma in karba in zuzzuba mana tare da su Hanan, wataran ayi dankali da kwai ko doya da kwai a hada da farfesun nama ko kaza, Haleefa da ya tafi makaranta sai muka sake raguwa tunda ya Abba ma baya nan, kowa sai yayi bismillah ya fara cin nashi, ana ci ana hira cikin raha.

Bayan mun gama karyawa sai Abbu ya ce ‘ayyi mishkilatan?’ Yana nufin ko da akwai wata matsala ko bukatar wani abu, in babu shikenan sai kowa ya tashi sai makaranta, su Hanan kam anan inda na gama suke suma, duk ma nan muka yi har ya Abba saboda makarantar na da kyau, private ce ta kudi. Hanan yanzu tana aji uku a sakandare, Nurain kuma na aji biyar na firamare shekara hudu ne tsakanin su suma, ni da Leefa ne ma ba rata sosai dan shekara biyu ne tsakaninmu yanzu gashi har ya shiga level na biyu a jami’a, da yake kuma daga aji biyar ya yi paper ya samu sai ya jona jam’iar kawai.
Da daddare ma kamar yadda muke da safe haka ake haduwa aci abincin sai kuma mu koma falo mu danyi kallo, su Abbu falonshi suke tafiya da Ammi ya kalla labarai na karfe tara network news’ kafin ya kwanta, mu kuma in ba cartoon ba sai ko in ana wani drama mai dadi na larabci kuma Ammi na mana kashedi banda kallon shirme. Leefa ne in yana nan yace zai canza mana channel saboda dakinshi ba TV, ya Abba kam baya kallo ma ko da yake nan, shima Leefan bai kallon drama din nan yace shirme ne sai dai yaga labarai ko wani documentary(tarihi akan wani abu) haka da tashar China ke yi, su Nurain kuma su ce cartoon suke so musamman in ana power rangers ko wani ‘miraculous’ nima har naji ina son shi saboda nacin su duk kuma da larabci ake yi.

Ko da yaushe muna gida kuma Karfe shida kowa ya dawo gida duk inda yaje har mazan saboda gudun karya dokar Abbu. Har na tuna Sitti maman Abbu ta kan ce kiyi ta zama a gida dai kekam, in baki fita ba wa zai ganki har ki samu mijin? Sai dai inyi dariya kawai dan har na saba da mitan ta, ammi sau da dama zata ce kar in damu, yau ko a cikin roba kike a rufe karewa kenan sai mijin ki yazo ki cigaba da addua ke dai. Nikam addua ta kullum Allah ya bani miji nagari da zai so ni ya mutunta iyaye na kuma, ban taba son wani ba saboda na sama raina sai mijin da zan aura ne zan so har karshen rayuwata indai har ya ganni yace yana sona shikenan nasan zan so shi nima amma bana raayin soyayya daga wajen nan kazo kuma ba auren mutum zaka yi ba sai inga kamar hakan yaudara ce.

Shiyasa ko da na hadu da wani ma dan da wuya in na fita in dawo ba tare da na hadu da wani ya tsai da ni ba duk da yake ba tsayawa nike ba tunda nasan tsarin gidanmu sai dai in ya matsa in bashi nambar waya, toh wani ikon Allah ko da ya kira ba zaifi sau daya ba daga nan baza ka sake jin shi ba, na kan ce Allah ya san ba shine miji na ba shiyasa ya hana shi sake nema, Ammi ma abun na damunta wani lokacin har ta fini damuwa ma amma sai ince mata ‘Ammi ba komai dai in Allah ya yarda miji na zai zo ko ba dade ko ba jima, nima danne nawa damuwar nike dan in kwantar mata da hankali, Abbu kam kan ce mata “har nawa Amnan take ne wai, da a can Sudan ne yanda baba ke fada ai ko tunanin aurenta ba a fara ba.” Ita kuma Ammi tana gudun surutun dangi ne ba wani abu ba amma ta bangaren Abbu babu ruwansu su, dangin ta ne masu surutu har da masu cewan Abbu yafi so ya nemo mun balarabe ne a dangin shi wai shiyasa ya ki aurar da ni. Sai dai yayi dariya kawai dan maganar su bai taba damun shi ba asalima ko kulawa bai yi sai in yaga Ammi ta damu ne zai kwantar mata da hankali.
*****
Kiran waya ta ne ya dawo da ni daga tunanin da na afka.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fudayl 3Fudayl 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×