Skip to content
Part 13 of 32 in the Series Hakabiyya by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Huzaif ya ɗaga ƙafa zai ƙarasa gurinta, sai kuma ya hangota tana tahowa gunsa da gudu-gudunta.

“Me yace maka? Naga kun daɗe? Wai mutum ne ko? Ka duba ƙafarsa kuwa ba ta doki ba ce? Ko a cikin sau ciki take? Kai wallahi ba ni nake faɗa masa inda zani ba kawai ganinsa nake! Jiya ma fa na ganshi a mota kusa da gidanmu, har ya min waya ya ce yana bibiye da Ni, bansan wane ya bashi number ta ba, kasan shi ne naga kuna ta magana yana dariya, yauwa…”

“Ya isa dan Allah!”

Ya furta a hankali yana kallonta.

Ta yi shiru tana kallon yanayinsa ganin kamar baya jin daɗi, sai kuma ta ware ido sa’ilin da tsoro ya shigeta, ta matsa kusa da shi tana kwalala masa idanuwa.

“Lafiya? Wani abu ya maka wai? Mene wai?”

“Kai! Ke kam ki yi mini shiru mana inyi tunani! Zo muje dai!”

Ya faɗa yana yin gaba ta bishi da sauri zuwa cikin motarsa.

Tada motar ya yi ya miƙe zuwa hanyar da za ta maidata gida. Ta kwalalo ido tana kallonsa ta kasa magana ganin kamar baya buƙata gashi ya tamke fuska tamkar bai taɓa fara’a ba, hankalinsa gabaɗaya ya maida shi kan tuƙin da yake yi.

Ta yi tsuru zuciyarta nata azalzalarta ta tambayeshi shakkarsa na hanata. Da ƙyar dai ta rarrashi kanta tana taɓe baki. _oho dai idan ta yi wari na ji, mutum sai wani ƙunci yake shi kaɗai.

Ni ka kunnan Radio to.

Ganin kamar ya ji mai ta ce dan ya waigo ya dubeta ya sa ta ja gyalenta ta yane fuskarta. Ya girgiza kai kawai yana mai maida kansa kan tuƙin.

Sai dai suka isa kwanar gidansu ya tsaida motar. Ya ɗago ya kalleta suka haɗa ido ta yi saurin janye nata idon. Ya mata murmushi yana mai yin ‘yar gyarar murya.

“Haƙabiyya da gaske kike so na ko?”

Ya furta a sanyaye yana tsurawa yatsun hannunta da take ta murzuwa ido.

Ta yi wal!Da ido, wata kunya da ta rasa daga jihar da ta fito na baibayeta, ita fa jira kawai take ya ce yana sonta ta fasa masa ihu cikin kunnuwansa, amma sai wani salo yake mata yasa duk kunya na kamata, sai ta yi ƙasa da kanta kawai tana ɗaga masa kai alamun I.

Ya jinjina kanshi sam bai za ci zata yi shiru ba, ya sha yana tambayarta za ta zabura ta ce masa fiye da kome take sonsa yadda ta saba.

“Za ki mini duk abinda nake so ko?”

Ya furta a hankali kamar mai raɗa, hakan yasa har tsigar jikinta ta motsa taja a’uziyya tana ɗan janye jikinta daga kusa da shi. Sai kuma ta ɗago jikinta ya yi sanyi ƙalau ta dube shi, idanuwansa sun kaɗa sosai, sai dai bata fahimci kome ba ta maida kanta ƙasa tana jijjiga kai.

“Zan maka kome Sir, ko menene kuwa idan har ba zan saɓi mahaliccina ba.”

“Kin yi alƙawari ko?”

Ta ɗan nisa tana jan numfashi.

“Na yi alƙawari, kar ka yi shakka kan hakan, zanyi duk wani abu idan har zai sakaka farin ciki, wai menene? Ka zama wani mai sanyi fa?”

“Kinsan abinda ya ta’allaka da farin cikina?…”
Bai jira amsarta ba ya ci gaba.

“Farin cikin mahaifina, ina son ganin farin cikinsa fiye da duk wani abu da kike tsammani, kinsan menene farin cikinsa a yanzu?”

Ta girgiza kai cikin rashin fahimta.

Ya nisa a bayan ya rufe idanuwansa ya buɗe.

“Ke ce Haƙabiyya, mahaifina ya ganki yana sonki da aure, ki so shi ba domina ba, ki so shi domin Allah Haƙabiyya, wallahi a cikin idanuwansa na hangi ɗumbin ƙaunar da yake miki wadda na tabbata ba za ki samu wani da zai miki irin ta ba. Ki manta da ni, ki manta da duk wani abu na so da kike mini, ki ɗau mahaifina a matsayin ni, ki ɗauke ni a matsayin ɗan uwanki ɗan mijin da za ki aura. Ki yi hakuri da kome ki yi hakuri da Ni, kar ki guji mahaifina domin Allah kar ki guje shi saboda ni. Ki so shi yana da tarin kirki da alheri, kin gan shi ai a gidana ba tsoho ba ne ko? Ki tuna yadda kike so na da abinda kike ji kaina, ki tuna a shekarunsa shi ma fa haka yake ji kañki, ko domin…”

“Mugu…!!” Ta furta da ƙarfi tana sanya hannayenta ta toshe kunnuwanta.

“Ya isheni wallahi Allah!!”…

Ta ƙarasa tana rushewa da ihun kuka.

“…Kai amma Huzaif kai mugune, maƙetaci, mai son kansa, to wallahi Allah kai kaɗai nake so, kai!

Wai ni, Ni fa Huzaif? Saboda baka ƙaunata sai ka ƙaƙabani ga Babanka? Menene ya yi zafi har haka? Tsabagen mugunta da baƙar zuciya haramtani gareka ma zaka yi? Shin idan na auri Babanka ta yaya kai zan sameka? Wai dan kaga ina na ce maka shi ne za ka haɗa baki da shi ko?”

Ta ƙara sanya kuka da ƙarfi tana toshe bakinta.
“To ba za a daina son naka ba, ba kuma za a so shi ba ko zai mutu, to wai ta yaya ma zan so wancan mutumin mai zubin ghost? Shi Banda mutuwar zuc…”

“Ki iya bakin ki!”

Ya furta a tsawace idanuwansa na daɗa ƙanƙancewa.

“Ki faɗi duk abinda za ki faɗa kaina amma kar ki ci mutuncin mahaifina a gabana ko a bayan idona zan iya yafe kome ban da wannan!!”

Ta yi ƙasa da kanta cikin shesshaƙa da rashin sanin abin yi.

“Huzaif domin Allah ka ji tausayina kar ka mini haka, Babanka fa? Wai to da wane idon zan dube shi, suruki nane fa?”

“Da idon da kike dubana, ki yi haƙuri dan Allah, kinyi fa alƙawarin za ki yi mini duk abinda nake so.”

Ya furta a tausashe.

“A’a wallahi na goge alƙawarin, son zuciyane wannan abin da za ka aikata, zalunci ne wannan, kasani kai kaɗai nake so, ba mahaifinka kaɗai ba ko da ace wani ne mijina ba kai ba na tabbata gangar jikina kawai za ta rayu da shi, zuciyar duka kai ke kewaye da ita.”

“Ki bashi gangar jikinma idan har za ta sanya shi farin ciki muna so, na sani da sannu watarana alkhairinsa zai sa ya samu zuciyar taki.”

“Ba zai yiwu ba, kai nikam na shiga uku, Huzaif ka tuna daɗewar da na yi cikin soyayyarka wai ya kake so na yi da ƙaunar da nake maka, wai ma ina aka taɓa haka?”

“Ki haƙa rami ki binneta inda ba za a iya tono ta ba balle watarana Abba ya gane kin so ni, kin sani hakan zai sa ya haƙura da ke, Ni kuma abinda ba na so kenan, yana sonki sosai Haƙabiyya, ba na ji kince kina son auren mijin da ke mutuwar sonki ba?”

“Banda Babanka ai”

Ta furta  tana daɗa rushewa da kuka, ya yi tsai yana kallonta kansa na daɗa zafi. Shi bai ma taɓa ganin lalura irin tasu ba. Yarinya ƙarama ta bi ta haɗa musu zafi, ya bita da kallo cikin nazari, _ko me ya rikita Abba kanta duk tarin manyan matan da ke biyowa ta gurinsa ya musu hanya?_ oho_, sai kuma ya girgiza kai da ya tuna yanzu ba yarinya ba ce gunsa, matar Babansa take shirin zama, yadda yasan halin Abba idan yana son abu gaggawa gare shi, yasan bai ƙi ayi auren cikin mako guda ba. Dan haka ya nisa yana kwantar da murya da sigar rarrashi.

“Haƙabiyya ki yi haƙuri mana, yanzu dai ki je gida ki yi nazari zuwa gobe In SHA Allah za ki Ji ya fara burgeki, za mu zo ma gun Baba.

Ki tuna fuskarsa fa saboda Allah menene marabarsa da Ni ɗin?”

Ta wara ido sosai tana jan hanci tana dubansa taga ta inda suka haɗu da mai zubin ghost.

Ta girgiza kai da sauri tana buɗe motar a fusace ta fice.

“Ni ba shashasha ba ce da zan ƙare a jikinku. Kai ɗin dai ba za a bar sonka ba, shi kuma ba za a so shi ba ko zai mutu. Kar ku kuskura ku zo gidanmu dan wallahi yadda nake jin zuciyata zan iya fasa muku kai. Shi ɗin kuma ka sanar masa an daɗe da yi mini Miji, dama ƙaunar da nake maka yasa ba zan yi biyayya ga abinda uwata ke so ba. Yanzun ina shiga gida zance mata ta turo mini wanda ta zaɓa minin.”

Ya bi ta da kallo cike da mamaki, bai taɓa zaton ta iya zuba rashin kunya ba sai yau, duk da ɓacin ran da yake ciki sai da ya murmusa da ya tuna wai za ta fasa musu kai, yasan lamarin da ya zo mata da shi ne duk ya ruɗata ta haukace masa. Ya jinjina kai yana kiran sunan Allah da ke juya dukkan lamura, ya nisa a hankali yana tada motarsa ya fice daga layin.

<< Hakabiyya 12Hakabiyya 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×