“Idan zan rufe gidan nan sau goma sai ta fita sau goma, wannan sakacinki ne da iya ɗaurewa ƙarya gindi. Na ce shi wankan dole ne? Idan za ki kauce daga gabanta me ya sa ba za ki rufe ta a ɗaki ba?”
“Haba Maigida, a mari take ne da zan dinga kulle ta ko a gidan mahaukata? Ina dalilin da za ka matsa har haka, na faɗa maka bana sanin za ta fita, yanzun ma zaune muke tana gyaran zogale na ce bari na kewaya kafin na fito ta fice, idan tsaron dole ne ka ƙara tsayin katangarka. . .