Skip to content
Part 4 of 12 in the Series Halimatus Sa'adiya by Ameenat Auntyn Khalil

A babban falon gidan muka zauna, daga bisani kuma Aunty ta sa aka ƙara shirya min ɗakin da zan zauna.

Wanka na fara yi bayan na shiga ɗakin, sannan na yi sallah aka kawo min abinci, sosai na zage na ci na ƙoshi sannan na sha magani, daga nan kuma sai bacci ya fara ɗauka ta, har na kwanta sai kuma na fara jiyo muryoyin yaran gidan da alamu baƙo aka yi. Sandan da nake dogarawa da shi sakamakon ciwon da ke ƙafata na kama na tashi a hankali, kafin na kai ƙofar fita ma an turo ƙofar an shigo, wa zan gani? Abbana ne, take na sakar masa murmushi, ko ba’a faɗa ba na san ya ji daɗin ganina, ga yadda shi ma fuskarsa take a sake ga wani murmushi da yake yi min wanda yake nuna tsantsar soyayyar ɗa da mahaifi.

“Ashe nan kuka taho? Lami ba ta faɗa mini ba sai zuwa na yi asibiti aka ce ai an sallame ku.”

Washe baki na yi na ce,

“E, Abba an sallame mu, ni na ce wa Anty Lami mu taho nan kafin na warke.”

Ina maganar ina kautar da farantin da na ci abinci gefe na ba ahi wuri ya zauna kan dardumar sallah, da alama bai ji daɗin kawo ni nan ba, na fahimci haka ne daga canjawar da fuskarsa ta yi da kuma furucin da ya biyo bayan haka.

“Ai shi kenan, amma ya dace ace kun sanar dani, ba wai ku kamo hanya kawai ku yi gaban kanku ba. Sai Muttaka na kirawo a waya bayan na je asibitin ba kwa nan sannan ya shaida min kuna nan.”

Na ji ba daɗi, kuma ba mu kyauta ba, ko ba komai ya kamata mu faɗa masa mun taho nan, to amma ya zan yi, idan na koma gida ba ni da mai jinyata, da na yi tunanin kirawo takwara to amma ai ita ma ba zaman kanta take ba, tunda tana da iyaye, daɗin daɗawa kuma ba jituwa take yi da su Ummee ba. Mama kuwa ba ta so na da kowa don haka duk abin da ya shafe ni gaba take yi da shi tun ina ƙaramata na san wannan.

“Abba ka yi haƙuri, Anty Lami ta yi hidima dani sosai, kuma idan ina tare da ita ina jin kamar ina tare da Ammana ne.”

Tsawa ya daka min,

“Idan ina magana da ke kada ki ƙara sako min sunan wannan shashashar.”

Take na shiga cikin nutsuwata don ko kaɗan Abba ba shi da wasa, ba ya sakar mana ko da kuwa akan iyayenmu mata ne.

“Ka yi haƙuri Abba ba zan sake ba.”

Idona cike da ƙwalla na yi wannan maganar, kallo na yake kuma na san ya fahimci ban ji daɗi ba sai ya canja maganar da tambayar magungunan da aka rubuta mini,

“Kina shan maganin dai ko?”

Ba tare da na ɗago kai ba na ce,

“E Abba.”

Ya ce,

“Allah ya ƙara lafiya, ki kuma dinga jin magana.”

“Amin, in Sha Allah zan kiyaye.”

Ya ce “Madalla.”

Muna nan zaune aka kawo masa abinci, su Nana duk suka zo suka zagaye shi, bayan sun gaishe shi suka fice, ya ci abinci sannan ya tafi.

Tun bayan tafiyarsa na koma na kwanta, amma ba bacci nake ba, tunani na shiga yi ko ina mahaifiyata take? Ko a wace duniya take oho, Allah ne masani.

Wasu zafafan hawaye ne suka soma zirya saman fuskata, sai da na yi mai isa ta na haƙura.

*****

Kwana na uku gidan Anty Lami sannan takwara ta zo, zuwa lokacin na yi fushi da ita sosai, ko da ta shigo ma ciki na amsa sallamar ta, kuma ta fahimci na yi fushi.

Wuri ta samu gefen katifar da nake kwance ta zauna, dariya take son yi ganin yadda na cika na yi fam! Sanin halina ya sa ta gimtse dariyar ta ce,

“Wai fushi kike dani?”

Ɓata rai na yi na ce,

“Ban sani ba, da kin sani ma ba ki zo ba.”

Mayafinta ta cire, ta ɗauki roba ɗaya daga cikin abin shan da Fatima ta kawo mata ta fara sha, sai da ta sha rabin kofi ta ajiye ta ce,

“Pop Apple din nan kamar ya fi ma Lacaseran ainahi daɗi.”

Ban san lokacin dana kwashe da dariya ba, saboda duk lokacin da aka yi zancen lemon Pop cola ko apple ɗin nan sai na yi dariya, wanna kuma wani dalili na ne na daban.

Juyawa na yi na kalleta,

“Kin kyauta sai yau kika zo, ashe da mutuwa na yi ma ba za ki zo ba.”

Kan katifar ta hau sosai tare da jingina da bangon ta fara jero min uzirinta,

“Kin san meye yake bani haushi da ke?”

Na ce,

“Ina zan sani uwar kare kai.”

“Ba kya iya yi wa mutum uzuri, da kina asibiti akwai ranar da ta fito ta koma ban zo ba?”

Na ce,

“A’a.”

“Yanzu da ban zo nan ba, kin tambaye ni dalili na faɗa miki da gangan naƙi zuwa?”

“A’a.”

Na kuma cewa, ina kallon fuskarta, ita ma ni ɗin take kallo.

“Zan faɗa miki dalilin rashin zuwa na, kuma kada ki ce na yi haƙuri don na fuskanci ɗabi’ar rashin yi wa mutum uzuri na so ta shiga jikinki, idan ta shiga jikinki kuma mun shiga uku, don ko aure kika yi ba za ki ringa ɗagawa mijinki ƙafa ba.”

Sosai na maida hankalina gareta, saboda takwara yarinya ce amma ta fahimci duniya kamar wata babbar mace, wannan ya sa ba na son nesa da ita ko kaɗan, ina koyar abubuwa masu kyau daga gareta sosai, ban sani ba ko don ban taso gaban uwata ba ne ya sa ba komai na sani game da rayuwa ba oho Allah ne masani.

“Bayan kun taho da Anty Lami na je asibiti aka ce an sallame ku, to ban san gidan nan ba, na je gidanku Mama ba ta ma amsa sallama ta ba bare ta faɗa min inda kike, ina fitowa kuma na haɗu da su Firdausin Inna sun zo karɓar ɗinkin ƙanwar su kuma ba kya nan, na faɗa musu kina asibiti ba su yarda ba, Ummee ta yi musu rashin mutunci har muka yi faɗa da Haneefa kanwarku.”

Shiru ta yi tana kallo na tana murmushi, a wannna lokacin na mance ma da cewa ni sabuwar tela ce saboda tsabar ruɗu dana shiga kwana biyu.

“Ban san nan kuka taho ba a lokacin, sai yaya Muttaka ne ya zo da mukulli ya buɗe ɗakin ki ya ba su kayansu. Shi ya faɗa min kina nan gidan, washegari na ce zan zo, sai kuma Kawu ya tashi da Malaria (zazzaɓin cizon sauro) haka dai abubuwa daga wannan sai wancen, shi ya sa sai yau na samu na zo.”

Allah sarki takwara ina matuƙar son ta, amma wani lokacin ba na iya yi mata uzuri, na ji kunya, ashe mahaifinta ne ba lafiya.

Cikin neman sulhu tare da jimami na ce,

“Ayya! Ai ban san Kawu ne ba lafiya ba, Allah ya sawaƙa masa ya ba shi lafiya.”

“Amin.” Ta ce min, muka ci gaba da hira.

Cikin hirar da muke ne take faɗa min Abdulfatah ya zo nema na, amma bai same ni ba.

Ko amsa ban ba ta ba, saboda ta san ba na son shi, shi kaɗai yake ta wahalarsa, baya ga haka ma ni karatu zan yi don haka ko a jikina wai an tsikari kakkausa.

“Magana fa nake miki kin mini Shiru.”

Ruwa na sha sannan na ce,

“Ai kin san ba na son maganarsa, amma har yau kin ƙi daina yi mini ita.”

Cewa ta yi,

“Shi kenan, zan faɗa masa ya daina wahalar da kansa kawai ba kya yi.”

Tana maganar tana dariya, saboda ta san ko ba na son mutum to ba na iya yi masa rashin mutunci, saɓanin wasu ƴan matan.

“Ba ni da abin cewa akan wannan.”

Na faɗa mata fuskata a ɗan murtuke.

Duk tsawon zama na da takwara ban taɓa ganin wani saurayi ya zo wurinta ba, ban taɓa ji ta yi min zancen wani na son ta ba, gwara ma Khalid ya nuna alama, shi ma kuma har yau bai furta mata kalmar so ba, ina son tambayarta amma duk lokacin da muka haɗu kawai sai na mance da tambayar, da abin ba ya damu na, amma yanzu na fara damuwa a kai, domin Allah ya sani ba na so na yi aure na barta ba ta yi ba.

Da Allah zai karɓi addu’a ta ma na fi so a fara yin aurenta kafin nawa, saboda na gama yadda da ingancin halayen takwara, ina ƙaunarta saboda Allah.

Abun haushi yau din ma dai na manta ba mu yi maganar ba.

Sai wurin shida na Yamma ta tafi, cike da kewar juna muka rabu, Aunty ta ba ta turare da kuɗin mota, sosai ta yi mata godiya sannan ta wuce.

<< Halimatus Sa’adiyya 3Halimatus Sa’adiyya 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×