Skip to content
Part 14 of 53 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Ina kallo Asabe take fitowa daga wanka ta shafa maina tayi kwalliya da kayan kwalliyata in ta gama ta jawo akwatin kayana ta zabi wanda yayi mata ta daura,  bana cewa komai saboda ina tsoron kar maganar da zan yin ya zama sanadin da zamu yi fadan da zata rama cizon.

Sannan in ta gama abinda take yin sai ta mike ta bar komai a hakanshi sai na gyara wanda ni shi ne ma yafi bata min rai.

Rannan da hantsi Mubarak yazo muna tsaye muna magana sai ga Sallau yazo ya wuce mu yana taku dai-dai, ya bishi da kallo kafin ya dawo da kallon nashi gare ni wannan ya bai tafi ba ne? Na ce mishi eh, ya dan yi shiru jimawa kadan ya ce uhun, wato shi Baba ke kadai yake iya hukuntawa?

Ban ce mishi komai ba sai ya sake kallona “Ba suyi miki wani abu ba ko? Har na ce mishi Eh, sai kuma naga to in ban gaya mishi ba wa zan gayawa?

Don haka na kwashe bayanin komai nayi mishi, ya ce To babu laifi.”

Hirarmu muke yi sosai ina daga cikin zaure yana waje sai ga Asabe tazo zata shiga cikin gida, cikin dace zanina ne a jikinta kuma shi ya saya min shi, wani lalataccen kallo tayi mishi ta wuce da nufin shiga gida, ba karamar kiyayya Asabe ke yi wa Mubarak ba.

Duk sanda ta bude baki zata yi magana akanshi munanan kalamai take yi. Ina wuni Asabe? A lalace ta ce mishi lafiya, dan saurare ni mana minti bivu. Ta waiwayo tana yi mishi kallo na sama da kasa.

lafiya? Ta ce, bani da lokaci.

Ya ce To je ki zan aiko agogo yazo ya gaya miki amma kafin ki ji sakon daga wurinshi kina shiga gida ki cire wannan zanin da ke jikinki ki wanke shi ki goge shi ki maida shi inda ki ka same shi ki ajiye. Ta ce ai ka san don ku kadai Bature yayi iinshi, bai tanka mata ba sai kawai ya kira wani yaro mai kimanin shekaru sha biyar da ke can gefe.

Zo nan Isiyaku, maza haura can saman layi ko bayan layi kaje ka kira min agogo ka ce mishi ina nan na jiranshi yazo yanzu.

Hankalina yayi matukat daurewa saboda ganin yanda jikin Asabe yayi matukar yin sanyi da jin an tura a kira agogo. Me ke tsakaninta da agogo? Kuma wancne ma agogo? Wadannan sune tambayoyin da suka tsaya a raina.

Ga ni! Ta fadi tana mai kallonshi cikin natsuwa ya buda baki ya ce mata, in kin shiga ki gayawa Mamanku saboda nasan uwa ta gari tana karbar shawara wurin danta in dai tasan shi din mai hankali ne.

Ki bata shawarar kar ta sake saki ke ko wani ku bugi Maryamu, kai ko da ita kanta ne kar ta sake? Ku barta ta zauna lafiya a gidan ubanta don ta samu tayi ta bin dokokin da yake saka mata.”

A lalace ta kalle shi ta ce, in ba haka ba fa? Bai kau da ido daga gare ta ba ya ce in ba haka ba ranku ne zai fi na kowa baci, don ke da ni zan shiga cikin lamurranki ba kadan ba, kin san babu abinda ban sani ba a kanki zan sa a gayawa Agogo labarin, Dangana kin kuma san abinda hakan ke nufi.

Zan sa shi Agogon-ya kula min da lamarin gabadaya, ina yi muku wannan kashedin ne saboda kiyaye hakkin makwabtaka tunda akwai iyayenmu a tsakani, in kuma ba ki ji ba to kuje kuyi.

Ke Maryam kar ki tsokani kowa a cikin su, amma mugun kallo idan suka yi miki ki gaya min, na ce to.

Ya kau da kai daga garcta alamar maganar ta kare ta gane hakan don kanta ta wuce ta shiga gida ba a dauki lokaci mai tsawo bayan nan ba nima na shiga cikin gidan.

Daga shigan da nayi na gane akwai wani canji a tare da Asabe don ban samu kayana a jikinta ba, Babah Lantana ce dai na same ta tana huci tana fadin, Aikin banza aikin wofi, ni kam ai rashin jinni rashin tsagawa.

Abinda zai hana ni dukan mutum bai tabo ni ba ne kawai, amma duka ai har da na tsiya zan yi mata ko ma don in ga abinda za ayi min, sai nayi na wuce daki na barta tana maganganunta.

Asabe dai na gane ta dan ji abinda Mubarak ya gaya mata, ana cikin haka sai ga Sallau ya shigo gidan. “Mama ina so muyi magana da ke.” Ta bar abinda take yi ta tsaya tana kallonshi, yayinda shima yaja ya tsaya Kerere a gabanta suna kallon juna, “Menene ya faru? tayi mishi tambayar tare da sauraron abinda zai gaya mata.

“Wannan yarinyar ce nake so in ce miki ki fita hanyarta, ki bar kowa ya zauna lafiya, abinda kawai zan gaya miki ke nan.” Da sauri ta tambaye shi, “Wacce yarinyar?” “Mero.” Ya fadi sunan cikin wani yanayi.

Kan ya gama karasa sunan ya ji saukar mari a gefen fuskarshi tau! Da iyakacin karfinta tayi mishi marin, a kan wannan shegiyar yarinyar ka ke yi min wannan maganar, in ce ko dan tumurmusan da yayi maka ne yasa ka tsorata da shi haka har yake aiko ka da irin wadannan maganganun ka gaya min?

To na rantse sai nayi mata duka har cizon da ta yiwa Asabe sai na sata ta rama ko in rama mata da kaina, aikin banza aikin wofi, barazanar banza da wofi. Ni za a kawowa iya shege?

Ni fa nan da ka ke ganina ni ba matsoraciya ba ce, bana tsoron kowa duk iya shegen mutumn kallonshi kawai nake yi, yauwa!

Ya’yan Babah Lantana sun dan shiga natsuwarsu kadan saboda ta ki yarda suyi aiki sosai da kashedin da aka yi musu wanda ya tsorata su, amma duk da haka Asabe ta fita hanyar kayana ta kuma kiyaye yi mun wulakanci. na kai tsaye. Illa iyaka dai ba ma magana da juna.

Ina zaune a cikin gidan babu mai magana da ni in ba Mubarak ne yazo ya kira ni ba, shi kanshi Baban nawa gaisuwa ce kawai take hada ni da shi, amma bayan nan babu wani abu.

Tsananin kewa da kunci suka tarar min cikin zuciyata, na gane babu abinda yafi mu’amalla tsakanin mutum da mutum dadi, wanda ya rasa abokin mu’amallah kuma to ba karamar wahala ce ta same shi ba.

Ana cikin wannan haki na kamu da wani irin matsanancin rashin lafiya, zazzabi mai zafi gami da mura ga matsanancin ciwon ciki saboda lokacin al’adata ya gabato, babu wani taimako da nake samu daga gidan, sai dai in Babah Lantana taga ina rarumen abinda za ayi ko zan ci, saboda yunwar da ke yawan damuna, sai ta rinka fadin ba dai kin ce da ni za ki yi ba? Ai mun sa kafar wando daya ke nan ni da ke, naga wanda zai fara zare kafarshi.

Mubarak yazo duba ni da yamma yana daga waje ina cikin zaure, yanzu ke kin rinka zama da ciwo ke nan? An ce ki fito a kai ki asibiti kin ki, shi Baban ba ya ganin irin ramar da ki ka yi ne ya bar ki a haka?

Ban ce mishi komai ba na juya na shiga gida ina rike da ledar sayayyar da yazo min da ita. Ina shiga daki na zauna na bude ledar na jawo robar nono zan sha don kuwa nasan barin da jikina ke yi bana ciwo ba ne har da na yunwar da nake ji.

Na gama shan nonon na dawo-dashi gaba daya ta hanyar yin amai mai wani irin yawa da wari, ga shi yayi wani irin kala.

Amai a -daki? Asabe tayi tambayar cikin wani yanayi na nuna tsananin kyama, to na rantse sai dai ki kwashe ke da kanki, don ni bana taba amai.

Ina kwance ina jin ta ko daga ido in kalleta ban yi ba, cikin zuciyata dai fadi nake yi dadin abin ma a kan kayana nayi.

Babah Lantana tana jin Asabe tana ambaton sunan amai ta rugo a guje, amai? A nan gidan yau’?

Uhum, abinda na gudanwa Mallam ke nan abinda na gudanwa Mallam ke nan, abin da na gudanwa Mallam ke nan, bai gudunwa kan shi ba to tunda bai gudanwa kan shi ba kuwa ga shi nan ya same shi.

Ni kuwa babu wanda zai zauna ya renan min cikin shege a gidan nan yauwa, don mu abin kunya gudun shi muke yi saboda ba mu gaje shi ba, su dai ina jin suna da gadonshi shi yasa nake tayi mishi kashedi bai ji ba.

Sannan al’ amarin Mallam ma ai in ka duba akwai matsala, mutumin da bai da dangi Mallam fa ko sunan garinsu bai kira balle ya ambaci wani dan uwa nashi, wa ya san abin da yayi ya bar gidan?

Duk da tsananin ciwon da ke damuna sai da na zubawa Babah Lantana ido ina kallonta.

Ta ce, Eh kalle ni da kyau ko karya nayi muku? Ana barin gida haka kawai ne? Ai yawanci abin kunya a ke yi a tafi in kin ga dama ki gaya mishi kema kin san a tafin hannuna yake.

Ta muno min cikin tafin hannun nata, ta juya tana tafiya tana gayawa Asabe tafi can wajen tumatirinshi ki kira min shi yazo ya gani da idonshi kar ya ce karya nayi mishi, daganan kuma sai ya kwashe donni da hannuna ba zan kwashe aman cikin shege ba.

Ina kwance ina jin shigowar Babana da irin maganar da Babah Lantana ta tare shi da ita, ai babu abinda ban gaya maka ba kan ciwon da yarinyar nan ke yi ba haka kawai ba ne, ciwo kwana da kwanaki kuma mai zafi haka ai kowa ma yasan menene sai dai a yi shiru.

Da sauri Babana ya fadi cikin dakin jikinshi sai rawa yake yi, me ya same ki acuuwuna? Me ya same ta ko me ya same ta kai nan sai an gaya maka abinda ya same ta? Yasa hannu ya daga ni a’a har da amai ki ka yi? Yasa hannu ya nade ya fitar ya dawo, Babah Lantana tana fadin ai gara kaga aman da idonka, kar ka ce ko sharri a ka yi mata.

Tashi muje in kai ki asibiti, yasa hannu ya daga ni yana rungume da ni a jikinshi muka fito daga dakin za ka kaita a cire ne? ai binka zan yi don ba za ku ce ku dawo kayi min karya ba tunda dai wannan ciwon nata ai kowa ya ganta yasan ciki ne da ita.

Ina jin irin kaduwar da jikin Babana yayi sanda Babah Lantana ta ambata mishi cikin nan ya dan ja ya tsaya na yan dakiku bai motsa ba, kafin ya ci gaba da tafiya.

A asibiti a gaban Babah Lantana da Babana Likita ya gama duba ni ya gaya musu cewar maleriya da yunwa ne suka kama ni. A ka sanya min ruwa saboda ramar da nayi tayi yawa, a ka hada min da magunguna a ka sallame mu, Likita yana dada jaddadawa Babana lalle ne a kula da abincina don na rasa nauyi mai yawa a tare da ni.

A gida ina jin Asabe tana tambayar Babah Lantana me Likitan ya ce? Ta tabe baki ta cc bai kai ta wurin wani asibiti na gaske ba, can wurin wani dan iska ya kaita da bai ma iya aikin nashi ba, wai ciwon sauro ne da yunwa. Har yana wahi daura mata ledan ruwa in ma hada baki suka yi ya boye ai shi ciki dan duma ne muna nan sai ki ga ya fito mun ganshi da idonmu.

Washegari Babana ya kawo min ‘yan abubuwan ciye-ciye da yake ganin za su taimake ni. a gabanshi Babah Lantana ta rabe komai ta bani abinda take ganin shine daidai a wurinta, tana yi kuma tana fadin “In dai cizon sauro ne lalurarta to wanene mai lafiya ne a cikin gidan nan ba gara ita ba ma tana fita ta sha sharholiyarta a waje, mu kam ai kullum muna ciki muna tare da saurayen.

Inda na samu kulawa ta sosai-sosai daga wurin Umma ne da danta sai ko Yaya Dijah da mijinta, kusan kullum sai tayi min aike, kusan kullum din kuma zata ce wa dan aiken ya gaya min in naji sauki in zo tana son ganina in ce mashi to.

Na soma jin sauki ke nan Mubarak ya zo yayi min sallama kan za su tafi Umra shi da Babanshi, nayi addu’ar Ubangiji ya dawo da su lafiya, ya kuma sa suyi aiki karbab6e. Ya ce, To amin.

Ban yi miki sayayya ba saboda sanin yanda gidan naku yake da nayi don haka ungo wannan ki rike a wurinki ki adana kar ki bari su gani, balle su kwashe miki duk abinda ki ke so ki saya kar ki yarda ki zauna cikin damuwa.

Na gayawa Isiyaku kullum da safe yazo yaje miki aika ko wankinki ne ya taru ki ba shi zai yi miki, na ce mishi to. Lokaci mai tsawo ya dauka yana yi min kalamai na bada hakuri kan tafiyar da zai yi a cikin dani din ko wadatacciyar lafiya ba ni da itana ce mishi a’a babu komai.

Na dawo daki na kirga kudin da ya banin Naira dari ne cif wato fan hamsin ke nan, a wancan lokacin kuwa mafi yawancin sadakin yanmatan unguwarmu da a ke aurarwa ma bai wuce fam goma wato Naira ashirin, in yayi yawa a karbi arba’in ko hamsin da kyar kwarai za ka ji an bada sadaki fan hamsin Naira dari ke nan.

Mamaki ya kama ni, na in da Mubarak ya samu irin wadannan kudin ya kuma iya bani su, ganin kimar kudin da yawansu ya sanya ni tunanin in kaiwa Babana su sai naga to ai in na kai mishi ma wurin Babah Lantana zai dawo da su.

To ko in kaiwa Umma ta ajiye min? nayi maza na canza saboda tunanin anya ya gaya mata zai ba ni irin wadannan kudin? In bai gaya mata ba ke nan na hada su, don haka na mike da sauri na fita na bar gidan ba tare da na gayawa kowa ba.

Na tafi na kaiwa Yaya Dijah kudin da sauri na dawo nazo na boye Naira goman da ta bani ta ce in rike a wurina, saboda bukatuna.

Kamar yanda Mubarak ya gaya min cewar Isiyaku zai rinka zuwa min aika hakan a ka yi, da sassafe ya shigo ya gaida Babah Lantana kafin ya zo in da nake na dauko kudi na bashi, na gaya mishi abubuwan da zai kawo min yaje ya kawo ya karbi wankina ya fita da su.

Ba a wani dade sosai ba sai gashi ya kawo min su a goge, dadin hakan yasa na mike’da nufin in je in yi wanka don in kara jin dadin jikina.

Naje kicin da nufin in sanya ruwan da zan yi wankan da shi a risho don ya dan kore sanyinshi tunda ba gama wartsakewa nayi ba. Babah Lantana tayi maza ta ce min kar ki shigar min wurin nan ba ki da komai a ciki in dai ba tsamar min naman miya za ki yiba.

<< Halin Rayuwa 13Halin Rayuwa 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×