Kin san ba zai yiwu in ce mishi nawa ne ba don ya ma taba tambayata su na ce mashi ai tunda ubansu ya rasu danginshi suka kwashe su suka tafi dasu ni ko zuwa bana yi ke ce mai zuwa don na gaya mishi ke Yayata ce.
"Au, haba? Yanzu nan ni surukarshi ce? Ta ce, Eh abinda na gaya mishi kenan, ta ce to ai shi kenan su kuma yara kin fadawa Alhaji Tanimu ko? Tunda shi kam ya mutu ai magana ta kare, sai mu tafi a hakan tunda kuma abin ya zama haka to bari ni. . .