Skip to content
Part 7 of 59 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Kin san ba zai yiwu in ce mishi nawa ne ba don ya ma taba tambayata su na ce mashi ai tunda ubansu ya rasu danginshi suka kwashe su suka tafi dasu ni ko zuwa bana yi ke ce mai zuwa don na gaya mishi ke Yayata ce.

“Au, haba? Yanzu nan ni surukarshi ce? Ta ce, Eh abinda na gaya mishi kenan, ta ce to ai shi kenan su kuma yara kin fadawa Alhaji Tanimu ko? Tunda shi kam ya mutu ai magana ta kare, sai mu tafi a hakan tunda kuma abin ya zama haka to bari ni kuma kiga abinda zan yi miki.

Zan je miki wurin Mallam na kan tudu a kan damowowin naki duka sai mu ji abin da zai ce, da sauri Babah Lantana ta ce ma to Delu na gode.”

“A’a ba kin gode ne maganar ba, saura kuma in yi miki rana ke kiyi min dare, in taimake ki ke ki samu mijinki a hannunki ni kuma kiyi min iya shege menéne naku ban sani ba?”

“A’a to ni kam ai ba sanin yau ki ka yi min ba, in ma ya ya nake kin fi kowa.” “To ni kawo min abinda za ki kawo min in tafi.” Ta tashi ta shiga daki ta fito ban san nawa ta kawo mata ba, amma naji ta tana godiya tare da fadin wannan duka?

Ai babu komai kuma tunda ba wani nisane damu ba zan sa miki kwano ki rinka turowa ana daukar miki abincin dare, bakuwar Babah Lantana Dela tayi ta godiya tamfar dai wacce aka ce an baiwa kyautar kujerar Makkah.

Rannan na shirya zan tafi makaranta da safe a bakin kofa na tsaya nayi sallama aka amsa min na bude baki nace Babah zan tafi ne? Tunda abinda Babana ya ce in rinka yi kenan. Da saurinta ta fito tana fara’arta har kin gama shirin ne?

Na ce mata eh, ina kallon irin kallon da tayi wa gidan amma ba ta ce min komai ba sai ta ciro sule ta miko min, “To ga sule nan sai ki sayi abinda ki ke so ko? na ce, To. Na juya na tafi.

Ina dawowa gida ko amsa salamar da nayi mata bata yi ba ta rufe ni da duka titim-titim “”Ni ki ka mayar ‘yar iska saboda kin ganni a gaban ubanki ko? Ba kiyi min sharar tsakar gida ba ki karasa min wanke-wanke ba ki ka kama hanya kika tafi, ni baiwarki ce?

Nayi maza na ce, a’a, mara kunya kawai mara tarbiya dama kin nemi zama lafiya dani da ya fiye miki, ina canjina? Nayi maza na kara zaro ido cikin tsananin tsoro a dalilin ban san tana bukatar in kawo mata canji ba.

Ko duka ki ka kashe kudin da sauri na ce mata eh, don kar ta ce na bata mata lokaci wajen amsawa, ai duka kika kashe? Uh lalle ina da aiki, ni Lanti ni Lanti in ban yi da gaske ba lalacewa za ki yi a zo ana cewa ni ce sanadi wato a yadda ki ke din nan kina iya kashe sule guda a wuni.

To in ba ki bi maza ba kuwa kiyi me? Tayi wuf ta sake kamo ni ta tittime ni kafin ta sake ni ta wuce ta tafi tana to kuma a bakin abincin ranarki kin ji na gaya miki.

A wannan lokacin kusan kullum sai Delu tazo gidanmu ta kawowa Babah Lantaa wani abu ta kuma karbi kudin wani abu da za a sake karbowa kusan duk lokacin da ta zo kuma za kaji ta tana tambayarta kina ganin wani canji a tare da shi?

Ta ce to abinka da wanda baya magana wancan na sakawan dai a karo min shi, ta ce to kin gane kyanshi ke nan ta ce eh.

Rannan Babana ya dawo daga wurin tumatir din shi ta kawo mishi abincin shi ban san dalili ba naji ya kwalo min kira da sauri na amsa na fito ungo cokali Yaacuwuna zauna kici abincin nan kin ji.”

Cikin hanzari na gyara na zauna na kama cin abincin nan da nan na cinye shi tas na debi kwanukan naje na wanke su na kife na sake daukan tsintsiya na share wurin tas na dawo zan wuce in shiga dakina sai naji Babana yana cewa ni Malama in tambaye ki mana.

Da sauri ta ce mishi “Menene fa?  Ya ce, ba ki lura da irin ramar da yarinyar nan tayi ba, gaba dayanta fa ta zube kasusuwa sun bayyana a jikinta, ita kuma fa ba mai kashi ba ce, ramar tata tayi min yawa tun ina daurewa ina hadiyewa har abin ya gagaren na gaji na furta.

Ita mai cikakkiyar fuska ta zama wata yar siririya, in dai ba bata da lafiya ba ne yasa ta zama haka ai akwai matsala babba ke nan a tare da ita wanda ya kamata a bincika.

Da sauri Babah Lantana ta ce, cikin hanzari kuwa, gara ma a fara binciken tun yanzu, ke Yacuna zo nan, ta sake zabura cikin hanzari ta shigo dakin nawa ta taso ni a gaba ta tsugunar da ni a gabanshi. To gata nan tayi bayani da bakinta, yauwa bawa da bakinshi ai wuyan sai dawa gare shi.

Ina dalilin wannan kiran da kika yi mata? Babu halin’ muyi magana ni da ke sai ki kira yarinya ki tsomataa a ciki? Yarinya? Tayi tambayar cikin wani yanayi na tsananin fusata wannan ce yarinyar? Tafdijam, ba yarinya ba ce mace ce. To menene bata sani ba Mallam? Ai da kadan na fi ta sanin duniya wane sharri da makirce-makirce ne bata kulla min?

Tun farkon zuwana gidan nan fa kana ganin irin karbar da tayi min amma me na mata? Gata nan ai tayi magana da bakinta, ke ta zuba min ido tana kallona ina ba ki abinci ko ba na ba ki? Na ce kina ba ni.

Ta gyada kai to, ina zaginki ne ko dukanki? Na girgiza kai tare da fadin a’a, ta ce to amma a hakan ne ki kaje ki ka hada ni da ubanki a dole ke ga mai uba ko? To mu ma da bamu da uban ba kinmu a ke yi ba yasa a ka daukan mana su masharranciya kawai.

Watakila shirun da Babah Lantana taga Babana ya yi ne yasa ta tayi ta maganganu da tashin hankali mai yawa, bai ce mata komai ba yayin da ni kuma nayi matukar tsorata don gani nake tanfar zata mike ta rufe ni da duka ne.

Har tayi ta gaji bai ce mata komai ba nima kuma ban matsa daga inda ta durkusar da ni ba, sai da a ka kira sallar Magriba ya mike zai fita sai ya ce min je ki kiyi sallah nå ce mishi to.

Ina zaune a dakina bayan na idar da sallar Isha’i naji shigowanshi a tsakar gida ya samu Babah Lantana tana goge kafarta da dutse bayan ta fito daga wanka naji shi ya ce mata “In kin gama abinda ki ke yi kije gidanku sai nazo.”

Ko da bana nan a kusa nasan ba karamar firgita Babah Lantana tayi ba da jin maganar tashi saboda irin na’am din da naji tace kafin daga baya ta soma maganganu irin na borin kunya “Ai gara haka, ni dama tuni na dade ina jiran irin wannan maganar ta fito daga bakinka ba ka furta ba ne sai a yau. To kuma sai me? Ai ta fi nono fari in dai a kan wannan munafukar yar taka ne ai yanzu kasa hannu da aure. Bai ce mata komai ba har ta gani da maganganun ta figi gyalenta ta fita.

Tana fita ya tashi ya fita shima bai wani dade ba sai ga shi ya dawo min da gasasshen nama, nayi maza na karba na lamushe sabanin da da in ya kawo min na rinka yanga kenan yana rarrashina ina cewa an labta yaji yayi ta karkadewa yana cewa to ungo wannan na cire miki yajin.

Washegari ma haka tare muka karya gidan ya zama gwanin dadi kusan kwana biyar babu Babah Lantana alama na Babana bai bi bayan nata ba tunda cewa yayi taje sai yazo, cikin zuciyata babu abinda nake fata irin a ce ta tafi kenan ba za ta sake dawo mana gidanmu ba.

Tun kwanaki ukun farko na barinta gidanmu yanayin jikina ya soma sauyawa na soma dawowa cikin hayyacina.

Rannan muna zaune ni da Babana tsiren Salim mai nama ya kawo min ina ci ina korawa da ruwan tea mai kauri, sai kawai muka ji sallama, Babana ya amsa yayin da ni kuma na dauki abinda nake cina shige dakina na zauna cikin fargaba da faduwar gaba saboda sanin Delu ce tare da Babah Lantana.

Cikin ladabi naji Baba na yana yi mata gaisuwa irin ta surukuta saboda gaya mishin da Babah Lantana tayi cewar ita din yarta ce.

Kayi hakuri Mallam maigidan ne baya nan sai dazun nan ya dawo ya samu Lantana a gida na kuma yi mishi bayanin kwanakin da tayi a gida shine ya hau ni da fada ina dalilin da zan barta tayi ta zama haka ban dawo da ita ba?

Na ce, To naga baya nan ita kunma ta ce min kace kana zuwa ya dai yi ta fada kan rashin hankalin da ya ce nayi ita kuwa in ban da da mutane a gidan nan yau da ta gane kurenta ba kadan ba, don niyya yayi ya bata ka shi sosai, to sai a ka rirrike shi, ya ce in. baka hakuri kafin ya zo da kanshi.

Da sauri Babana ya ce mata, aa ba sai yazo ba nima zan zo gidan, kuma ayi min godiya amma gaskiya in ban da wannan bayani da ki ka zo min dashi da kuma ganin girman surukuta ba zan iya tozartata ba, wannan da cewa nayi ku koma tare. To ina jin kunya.

Da sauri Delu ta yi ta magana tana ba shi hakuri, “Ai shi ma maigidan ya ce ba karamin abu tayi maka ba.”

Kalamanta suka sanya har Babana ya shiga yi mata bayanin abinda ya faru duka, a gabana tana aibanta min yarinya har tana cewa wai da kadan ta fi ta sanin duniya, me take nufi? Ni fa saboda irin wadannan al’amuranne yasa nayi ta zama a haka dagani sai ‘yata, saboda bana son kananan maganganu da fitina, ban saba da su ba.

Ni matata bata saba min da irin wannan kace-nacen ba, ba kuma zan yarda in saba da su ba, a yanzu da girmana da komai. Gaskiya ne Mallam, wannan maganar taka ita ce gaskiya in ban da rashin hankalinta ita wannan yarinya ai ‘yarta ce yanzu ita marayunne da ita ba hawa-hawa?

Ga nata na kanta ga kuma na yarta da su kuma babu uwa babu uba, to don me ba za tar  rike wannan da kyau ba, shi al’amarin duka ai yiwa kai ne, kayi hakuri in naje gida kuma zan yi mishi bayanin da kayi min duka.

To na gode Yaya, in ji Babana, ina ita uwan take? Babana ya kwala min kira saboda jin Delu tana kirana, don haka na fito nazo na durkusa na gaishe su, uh’uh uh lalle yarinyar ta zube amma ba ka ga kamar har da macijin ciki a ciki ba Mallam?

Ina ganin a nema mata maganın macijin cikin, ka san shi shegen abu ne sai yayi ta ci a ciki ba a sani ba šai dai ayi ta tsotsewa ana motsewa a tsaye ba a kwanta ba, tana maganar tana tafiya bayan tasa hannu biyu ta karbi abinda ya bata na alheri tayi godiya.

Kwana biyu bayan dawowan Babah Lantana, Babana bai sake mata ba, itama kuma ta shiga cikin natsuwarta sosai.

Rannan sai ga Delu tayi sammakon dawowa tun Babana bai fita kasuwarshi ba, suna gaisawa naji tana ce mishi maigidanne ya ce in zo in kara duba ku in kuma kara baka hakuri don babu abinda ban gaya mishi ba da na koma ranshi ya baci sosai hankalinshi yayi mummunan tashi ya ce wannan ai nema take ta zubar mishi da mutunci.

Ya dan yi murmushi kadan tare da fadin a’a haba, ai ba a haka ka hukunta wani kan laifin da wani ya aikata maka ba adalci ba ne, ita kam mace ai dama kowacce da irin halinta ba a kuma yin shaida a kanta iyaka dai kawai akwai wacce tafi wata dama-dama.

Haka ne Mallam, suka ci gaba da yan hirarrakinsu irin na surukai kafin yayi mata sallama da cewar zai tafi kasuwa ta sake sa hannu biyu ta karbi alherin da ya bata tare da godiya.

Sai dai yana barin gidan ta juya wurin Babah Lantana, uh’uh’uh kai wannan miji naki da taurin kai yake, bai rusunawa kan ra’ayinshi, gashi da kafiyar tsiya bai kuma damu ya fadi abinda ke ranshi ba, ko da kuwa yasan hakan zai iya batawa wani rai.

Babah Lantana ta ce, Uhun, ai ba ki ma sani ba, tunda muka dawo din nan fa bai saki jikinshi da ni ba, ba ya ma yarda ya hau gado ya kwanta sai kawai yayi shimfidarshi a kasa.

To me ki ka ce mishi? Zuba mishi ido kawai nake yi in na nuna mishi na damu ai sai ya rinka yi min irin wannan wulakancin. Ai ke ce ma Lantana da wautarki ba ki tàbbatar kin kama shi a hannunki ya kamu ba za ki fara kawo mishi iya shege.

Wannann iya shege ne, don me za ki tasa mishi ‘yarshi a gaba? Tasata nayi a gaba Dela? Babah Lantana ta taso, Delu ta ce, ai ke dama haka ki ke, in mutum ya ce zai gaya miki gaskiya sai ki zabura ki ce za ki yi fushi don ba kya Sonta.

Sannan kuma a kan wannan yar tashi in ba ki yi hankali ba komai ma zai iya faruwa, kar ki ce ba komai ma zai iya faruwa kar ki ce ban gaya miki ba, yanzu dai ga wannan shi wancan mutumin ne ya ce a kawo miki ki samu gero kwaya bakwai ki hada da wannan garin maganin ki make shi a gefen bakinki sanda ki ka tabbatar kin shawo kanshi zai kula ki sai ki kwana da shi gari in ya waye sai ki juye har da yawun baccina faranti ki shanya shi a dakinki kar rana ya taba, sai ya bushe sai ki dake shi lukui-lukui shi za ki rinka zuba mishi a abinci da komai ma ko da kuwa ruwan da zai sha ne.

Ta ce mata to, Delu na gode babu kuma addu’ar da za a yi ko? Da sauri ta ce, a’a za ki yi addu’a mana kar ya ji kar ya gani, abinda za ki rinka fada ke nan tayi maza ta sake yin godiya.

Delu da kanta tazo ta samu Babana ta roke shi wai ya yi wa wata yarta da ke gidan miji taimakon ta samnu zaman lafiya da mijinta, saboda kullum a cikin barazanar korarta yake, ga ta kuma da kananan ‘ya’ya har guda biyar.

<< Halin Rayuwa 6Halin Rayuwa 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×