Dayar ledar kuma, less, atamfa, da kuma shadda ne masu kyau, sai ta kalmi gyale, turaren Wuta, na kaya da kuma na jiki.
Ban san lokacin da na fashe da kuka ba, maimakon Rahma ta lallasheni ita ma sai ta fashe da kukan.
“Aunty kayan da Momy ta saya miki ne ba kya so?” cewar Khalil bayan ya dafa kafadata.
Girgiza kai na yi alamar a’a.
“Aunty wai Mamana da Ramla sun mutu?” cewar Affan yana kallona
Nan ma girgiza kan na kuma yi.
“To suna ina, Abbanmu ba shi da lafiya, amma su ban gansu ba?” ya kuma tambayata
“Suna Ruma” Na ba shi amsa hade da share hawayena
“Amma Aunty mutane sai cewa suke sun rasu, yanzu shi kenan ba mu da Mama.” cewar Khalil yana kallona.
Take zuciyata ta kuma karyewa na kira Affan na rumgumesu gabadaya ina fadin “Kuna da Mama Khalil, ga ni ga kuma Aunty Rahma mu duka iyayenku ne, na yi alkawari zan yi maku riko tamkar Sakeena na raye, zan rike amanar da ta ce ta bar ma ni, muddin ina raye ba za ku yi kukan rashin uwa ba sha Allah.”
Kuka mu ka yi sosai, har sai da mu ka gaji don kanmu. Sannan Rahma ta tafi, bayan ta bar su Affan a kan za ta zo da yamma ta daukesu.
Duk wata hidimar zuwa school nasu ita ce ke yi, haka asibiti kullum sai ta je ba ta gajiya, kullum cikin hidimarmu take.
Sosai su Khalil suka debe min kewa fiye da su Zainab, duk da suna yawan tuna min da Ramla.
Saboda muddin suka shigo bangarena da ita za su yi ta kiriniyarsu, abu kadan ta sanya kuka, wani lokaci sai na koresu bakina yake yin shiru.
Amma yanzu sai su biyu kawai suke yi, sai ni da nake taya su kadan.
Yamma kam sai ga Rahma ta zo daukarsu. Time din ma daga ni har ita, kowa sai da ya yi kuka sannan suka tafi.
*****
Safiyar talata misalin karfe tara na safe na fito cikin doguwar riga mai kalar ja, babu wata kwalliya a kan fuskata, dan ƙaramin hijab fari na yi amfani da shi wanda ya tsaya daidai saitin cikina.
Baby sanye cikin riga yar kanti, irin Sayayyar Sakeena, ta yi kyau sosai Jamila ta shiryata.
Aunty Habi da ke zaune tana kallon tashar Arewa24 ta dago kai hade da kallona sannan ta ce “To ko ke fa, duk da ba ki yi kwalliya ba, amma ai kin yi kyau, kina abu kamar wacce ba ta yarda da kaddara ba, don Allah ki samawa kanki salama, su Sakeena yanzu addu’a suka fi bukata fiye da yawan koke-koken nan”
Murmushi kawai na yi, hade da zama ina ba Baby Nono.
Sai da na tabbatar ta koshi sannan na mikawa Zainab ita, muka fice zuwa asibiti
Don jiya ko baccin kirki ban yi ba, tun da aka ce an cire karafan da aka sanya a bakin Abbansu Khalil na kosa gari ya waye in gan shi.
Muna shiga dakin na hango fuskar Hassan cike da walwala, hakan ya sa na ji gwiwata ta kara karfi.
Shi ma tun da ya hangomu sai ya tashi zaune, hade da zuba mana ido har muka karaso.
Irin wannan kallon tsoro yake ba ni sosai, kashe min jiki yake yi. In ji kamar yana min kallon bankwana ne.
Har yanzu fuskarsa da sauran kumburi, kafarsa ma a kumbure take.
“Ya jikin naka.” abin da na fara fada kenan bayan na je daf da shi.
“Akwai sauki.” ya fada a hankali hade mika hannu yana son daukar Baby
Ya zuba mata ido “Wane suna kuka ba ta ne?”
“Babu” na ba shi amsa
Da sauri ya dago kai yana kallona “Yarinyar fiye da sati biyu amma ba ku yi mata huduba ba, wane irin abu ne haka?”
Wannan karon ranshi a bace ya yi maganar, idonsa ma ya nuna hakan
Dalilin da ya sa kenan na yi shiru.
“Wane suna kike so a sanya mata?”
“Ramla da Sakeena nake so”
“Suna biyu wa ita kadai?”
Shiru nan ma na yi ban ce komai ba.
Shi din ma bai kara magana ba.
Har zuwa lokacin da Abdallah ya shigo.
“yi ma yarinyar nan huduba Abdallah, ka ba ta duk sunan da kake ganin ya dace.” Baban Khalil ya fada
Ba musu Abdallah ya karbeta, mintuna kadan ya maidota hade da cewa “Na sanya mata Sakeena.”
“Allah ya rayata, ya albarkaci rayuwarta, ya sa ta yi koyi da halayen ta kwararta masu kyau” fadin Baban Khalil
“Amin duk mutanen gurin suka fada.”
“Kin ji sunanta ko?”
Kai na daga alamar eh, idona na cika da kwalla.
“Bana son a boye sunan, a kirata da Sakeenanta”
Komai ban ce ba. Shi ne ya kara cewa “Ko ba kya ji?”
“Akwai nauyi a baki, a yi mana afuwa zamu kirata da Maama yallaboi, saboda ita din mamarmu ce, ta yi mana abun da uwa ke wa yaranta. Ba zan daina kukan rashinta ba.”
Bai ce komai ba, da alama zuciyarsa a karye take.
Yau kam sai na dan ji farin ciki, saboda Bashir yana magana, duk da ba da kowa yake yi ba.
Misalin karfe hudu kuma, sai ga Rahma da dukkan yaran har da maigidanta.
Na fahimci Abbansu ya yi farin cikin ganinsu sosai. Sai magriba mu ka taho Rahma ta ajiye mu har kofar gida, ita kuma ta wuce.
Tun daga wannan lokacin duk bayan kwana daya sai na je asibiti, saboda Aunty Habi ta ce fita kullum ga danyen jego ba zai yiwu ba.
Babu wani abu da muka nema muka rasa, daidai gwargwado bamu rasa komai ba, duk da ana ta kashe kudi, amma Abdallah da Hassan suna kokari sosai da abokan Baban Khalil.
Babu abin da zamu ce masu sai godiya, shi ya sa ake cewa ka nema ka aje ko don ciwo ma.
Sannan ka iya mu’amala kuma kada ka raina mutane watarana sai su zama gatanka.
Bayan sati biyu da cirewa Abbansu Khalil karafa a baki, muka nemi sallama da kanmu, saboda gyaran da ake mishi a asibiti babu ya ƙi kyau.
Tun da ya iso kuwa gidanmu bai yanke da mutane ba. Rahma ta kawo yara sun wuni wurin Babansu, Sai magriba mijinta ya zo ya daukarsu. Sun dade da Abbansu Khalil suna tattaunawa a kan kodai fita waje za a yi da shi, amma ya ce za a fara gwada na gidan tukun. Sun jima tare, don sai wajen 9pm ya ta fi.
A lokacin ne kuma na samu damar shiga dakinsa na bangarena.
Zaune yake, yana danna wayarsa, shigowata ya sa shi mayar da hankalinsa a kaina.
“Ba ki yi bacci ba?”
“Eh” na fada hade da zama a gefen katifar da yake. Na gaishe shi, hade da kara yi mishi sannu, sannan na ce
“kana bukatar wani abu ne?”
“Tea kawai idan akwai.”
Mikewa na yi, tare da hado mishi tea din mai kauri na kawo mishi.
Bayan ya sha ne ya bukaci wanka, a kan kekensa na turasa har zuwa toilet,, ni ce na taimaka masa ya yi wankan, har da shaving, bayan ya fito na shafa mishi mai, hade da sanya mishi boxer da vest sannan na yi mishi sai da safe, don su Abdallah ne zasu kwana da shi, ganina ne ya hanasu shigowa.
Haka muka kasance kwana biyu muna, ana tattauna mafita, Rahma, maigidanta da kuma wasu daga cikin abokan Bashir sun fi karkata a kan a tafi da shi Indiya, yayin da ni da danginshi mu ka fi bukatar komawa gida. Ni dai kawai ban gamsu da maganar Indiya din nan ba, aje a kara jagwalgwala kafar, karshe ace dole a yanke ta.
Bangaren Bashir kam, mune muke damuwa da ciwon shi, shi hankalinshi Sam ba a, wurin yake ba. Ya tafi a kan rasa matarshi, na tabbata da za ace ya zaɓi tsakanin Ramla da Sakeena wa yake son a maido mishi, da gudu zai ce Sakeena. Amma yana cikin damuwa sosai a kwanakin fiye da lokacin da yake zaune a asibiti.
Ina yi kamar bana lura da halin da yake ciki ne kawai. Saboda tsayawa tattaunawa ko ba shi hak’uri a kan batun kamar fami ne, shi ya sa nake share shi.
Ranar Asabar da misalin karfe tara na safe muka bar garin Abuja zuwa Ruma, don yi wa Baban Khalil magani. Tafiyar da mutane da yawa basu so ta ba. Kar ma mijin Rahma.
Bamu tafi da su Khalil ba, suna gurin Rahma saboda school, amma ta ce ana yin hutu za ta kawo su.
A gidansu Baban Khalil muka sauka, abu da babban gida, ai nan da nan mutane suka cika kofar Inna, kai har da makota, kun san kauye da kara.
A ranar wasu suka yi kukan mutuwar Maman Khalil, abin da ya kara tayar da hankalin Bashir, mutuwar ta dawo sabuwa dal.
Safiya ma haka mutane suka dasa shigowa, musamman ƴan’uwansu na nesa, da ƴan’uwan Maman Khalil, duk wanda ya zo jimamin mutuwar Maman Khalil yake yi da yaba halayenta.
Wasu kuma su rika tambayar su Affan. Ni dai bukata a tafi wurin gyara, ji nake kamar ana zuwa zai warke.
Amma ba a kira mai gyaran ba sai da mu ka yi kwana uku da zuwa, ana ta shawarwari na wanda ya dace ma a dakko.
Ni dai koda na ji an ce an tafi dakko mai gyara raina fes, har addu’a nake Allah Ya sa su same shi.
Can wajen shabiyu na rana kuwa suka dawo, nan ma aka dora wata shawarar, na rasa abin da ake tattaunawa. Sai wajen uku aka fita da Abbansu Khalil cikin zauren gidan.
Kuryar dakin Inna na shige cike da tashin hankali, yayin da nake fatan a yi wannan gyara cikin nasara.
Ban taɓa tunanin haka gyaran zai kasance ba, kila shi ya sa ake ta tsugune tashi ina jin haushi. A sume aka shigo da Bashir bayan an gama gyaran, zuwa lokacin duk mun ci kuka mun koshi.
Sai la’asar ya farfado, dama yana zagaye ds ƴan’uwa, kowa ji yake kamar ya cire mishi ciwon.
Haka aka ci gaba da kula da shi, ni ba komai nake yi mishi ba, duk ƴan’uwanshi ke yi. Jego kam ga shi nan dai, a watse na yi arba’in. Kwana uku da canjawa Abbansu Khalil gyara dangina suka yo mota guda suka zo duba shi. Sosai na yi farin ciki, kuma na fahimci hakan ya kara kimata a idanun danginshi. Saboda dama dangin Sakeena kullum suna hanya.
Ranar da aka cika sati mai gyaran ya zo, cikin ikon Allah gyara ya yi, farin ciki guna ba a magana. Ba ni kadai ba duk wani masoyinshi ma. Kafar dai ba ta takuwa, Sai dai a kan keken nan, amma yana iya dagata da kanshi, har mikewa ma ya hau keken duk yana iyawa.
Ban san me ya faru ba, na ji dai an ce aje a share mana gidanmu, wai can zamu koma. Cikin kwana biyu kam aka gama gyare shi tsab muka koma. Sai na ji na fi sakewa, musamman wajen kulawa da shi. Saboda a can akwai idanun mutane, ba komai nake iya yi mishi ba.
Sosai na tattara hankalina a kanshi, duk wani abu da na san zai sanya shi farin ciki kokarin yi mishi nake yi.
Auran mijin mamaciya
akwai kalubale sosai, saboda kullum bakinshi a kan radadin yadda yake ji ne game da rashin matarshi, tun abun baya damuna har na rika jin babu dadi, daurewa kawai nake ba na nuna damuwata. Ni kaina ina kewarta, ballantana kuma shi.
Wani lokaci zan dage in yi masa abu, amma sai ya ce “Ina ma Sakeena na da rai na tsinci kaina a wannan halin, na san zan samu kulawa ta musamman”
Idan na ce ni bana kula da shi, sai ya ce wai shi ba haka yake nufi ba.
Kuma iyakar bakin kokarina ina yi, bana barinsa da datti. Yi mishi wanka, kai shi toilet, fitowa da shi, abincinsa, kasancewar ba komai yake ci ba.
Amma a hakan dai korafi yake. Ga ni dai yake da matarsa na da rai za ta fi kulawa da shi a kaina. Ga kafar tana yin wasu baroro kamar ya kone, wai sai aka ce daji ne, haka aka shiga karbo magunguna, amma ni ba na ganin wani ci gaba, kullum ciwon da sabon salo yake zuwa.
Yau Rahma da maigidanta za su kawo su Affan duba jikin Babansu. Shi ya sa tun safe nake ta lilo a tsakar gida, ba ni kitchen ba ni daki, ba na wajensa, ga Maama da rikici, idan ta fara kuka, kamar ana kwakule mata idanu. Ga kiwar tsiya, ba ta yarda da kowa, daga ni sai Jamila da Babanta, su din ma idan tana borinta basu isa su dagata ba.
Jamila na zuwa ta taya ni raino, don Zainab kanwata tuni ta koma gida.
Ina kitchen ina fama da aiki, ga Maama na ta kuka, ashe shi kuma yana kirana, zan kai shi toilet ban ji ba saboda kukan Maama.
Ban fita ba, har sai da na gama hada miya, dakinsa na nufa ba wai don na san yana kirana ba.
Sai don kawai in leka shi.
Ina shiga kuwa sanda tsakar ka.
Tun da na shiga yake bala’i kamar dama Jirana yake, ya hanani ma in yi magana.
Har sai da na jira ya kai aya sannan na ce “Ka yi hakuri, ban ji kiranka ba, Maama na kuka, kuma ina kitchen ba na son su Affan su iso ban kammala abinci ba.”
“Ki yi min shiru, tun da Sakeena ta rasu na tabbata na yi rashin da ba zan iya cike gurbinsa ba, yarinya daya kawai amma kin kasa kula da ita, ki bar ta ta yi ta kuka, aiki ki kasa gamawa da wuri.”