Sarai kam ba ta da aikin yi sai na habaici, ta yi da bakinta ko ta kunna waƙa, da ace ina biye mata da kullum sai mun yi bala'i.
Kwana ya kuma dawowa kaina, na shirya kayataccen abinci hade da gyara part dina, kamshi mai dadi na fita, haka ma ɗakinshi na gyare shi, na kuma kai mai abincin can, saboda so nake mu shirya yau, idan muna dadi da shi, Sarai ba ta faye kauɗi ba, amma da ta fahimci akwai abu tsakaninmu ta fara kauɗi kenan da yin abu da gayya.
Misalin karfe takwas. . .