Skip to content
Part 37 of 66 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Sarai kam ba ta da aikin yi sai na habaici, ta yi da bakinta ko ta kunna waƙa, da ace ina biye mata da kullum sai mun yi bala’i.

Kwana ya kuma dawowa kaina, na shirya kayataccen abinci hade da gyara part dina, kamshi mai dadi na fita, haka ma ɗakinshi na gyare shi, na kuma kai mai abincin can, saboda so nake mu shirya yau, idan muna dadi da shi, Sarai ba ta faye kauɗi ba, amma da ta fahimci akwai abu tsakaninmu ta fara kauɗi kenan da yin abu da gayya.

Misalin karfe takwas da rabi ya shigo, lokacinsu Khalil kallon ball suke yi, koda suka yi mishi sannu da zuwa da gaishe shi bai amsa ba. Ya haura sama abun shi.

Babu dadewa na bi bayan shi, lokacin da na shiga zaune yake gefen gado daure da towel, wayarshi a hannunshi yana daddanawa da alama daga wanka ya fito. Saboda jikinshi akwai alamun damshin ruwa.

Ciki-ciki ya amsa sallamata, stool na janyo hade da zama ina fuskantar shi. A tausashe na ce “Zuwa na yi in ba ka hak’uri”

Komai bai ce ba kamar yadda bai daina taɓa wayarshi ba. Na kuma marairaicewa kamar zan yi kuka na ce “Please”

Maimakon ya amsa min, wayar ya ajiye gefe hade da mikewa tsaye ya nufi inda dress mirror yake.

Boyayyar ajiyar zuciya na sauke hade da lumshe idanuna, a kokarina na tausar zuciyata. Da take fada min kawai in yi tafiyata, saboda ni ya kamata a ba hak’uri.

Tsaye na mike hade da nufar inda yake, na kwanta a bayanshi, hade da sagalo hannayena kan wuyanshi zuwa saman kirjinshi.

Ina jin yadda zuciyar ke harbawa da sauri-sauri, yayin da ya kasa ci gaba da shafa man da yake. Ni kuma na kwanta lamo ba tare da na ce komai ba. Duk yadda ya so sharewa sai ya kasa, dogon numfashi ya sauke, hade juyo da ni zuwa gaban shi.

A ɗan kausashe ya ce min “Ba tun yanzu kike ba ni damuwa ba Khadija, Sam ba kya ji, ban san me ya sa ba, ko don kin ga ina son ki”

Shiru na yi kawai ina wasa da hannuna, kayan kan mirror ya matsar hade da zaunar da ni a kai, shi kuma ya janyo stool din da na tashi a kai ya zauna. Wannan ya bamu damar fuskantar juna.

A nutse ya ce “Khadija don Allah ki yi ko yi da Sakeena mana, ba ta ɓata min gida ba, gyara min shi ta yi, kada ki ɓata rawarki da tsalle mana. Me ye haka kike yi ne? Me ya sa za ki saka yaran nan a zamanmu”

Ajiyar na sauke a hankali kafin na ce “Ni ban saka kowa ba.”

“Me ya sa su Khalil ke yi wa Nana rashin kunya? Kuma kina goya musu baya. Kalli abin da ya faru 4dz back Khadija. A gaban Khalil kike yi min ihu. Sakeena ba ta taɓa yi min haka ba”

A sanyaye na ce “Ka yi hakuri”

“If ma Nana ta daki Khalil, ba ta isa ta dake shi ba ne, idan har zan iya hukunta Khalil ke ma ki hukunta shi, to Nana ma za ta iya”

Hawayen da suka gangaro min na dauke da hannuna. Hannun nawa ya rike, hade da saka idanunshi cikin nawa, a hankali ya ce “I love you so much Khadija”

Ban san lokacin da na lumshe idanuna ba, kafin in bude kuma na ji saukar lips din Shi a kan nawa. Sai kuma muka haura zuwa wata duniyar ta daban.

Da safe haka na taso Khalil ya ba shi hak’uri, daga nan kuma komai ya koma normal tsakanina ni da shi.

Bangaren Sarai kuma abin da na fahimta shi ne, tun da ta tsaga ta ga jini shi kenan ta samu abin yi.

Abin da nake nufi shi ne, tun da ta fahimci idan ta taba yara ina damuwa, shi kenan duk hanyar da za ta bi, ta yi abin da zai taɓa su ita take bi.

Kasancewar yau babu Islamiya karfe daya na rana ake taso su Khalil, ga shi na yi baccin rana shi ya sa har suka dawo ban gama abinci ba.

Yanzu ma Affan na tura kitchen din ya gano min ko ruwa ya shanye. Da yake tun daga ranar da na karɓe key, kitchen din ya dawo karkashin ikon kowa.

Cike da mamaki nake kallon shi, lokacin da ya ce ya samu Sarai na wanke kai a sink din kitchen.

Na mike zuwa kitchen din don gasgata abin da ya ce, Sai ko na iske da morning fresh dina a hannu tana tsiyayawa a kan, ga kuma famfo a bude.

Maimakon abun ya ban haushi kamar yadda ta yi tsammani, Sai na ji ya ba ni dariya, duk da ban yi ta da sautin da za ta ji ba.

Na wuce wurin girkina, ganin ruwan ya shanye,  na kashe electric din, hade da dauke tukunyar zuwa part dina gabadaya.

Ina cin abinci ina dariyar Sarai, da na tuna yadda na iske ta dukar da kai gaban sink sai in ji dariya ta kwace min.

Ranar Juma’a bayan misalin karfe hudu na yamma, yaran na garden, na ji kukan Assidiq, ban damu ba, saboda suna tare da su Affan. Shi kuma akwai raki. Don haka na ci gaba da aikin hada humrata.

Jin kukan ya ƙi karewa ne ya sa na fito zuwa garden din, fitowa ta daidai Sarai na shiga dakinta, su kuma mu ka ci karo da su, Affan dauke da Assidiq.

Duk tambayar da nake musu na me ya faru babu wanda ya ba ni amsa, har sai da muka shiga cikin falo, sannan Affan ya ce “Waccan matar ce, mun ciro guava ta karɓe, wai tata ce, tana jiran ta nuna ne ta ciro”

“To Assidiq kuma kukan me yake yi?”

“Wai saboda ta karbe guava”

Kamar ba zan kara magana ba, Sai kuma na ce “Ku yi hak’uri don Allah, akwai lokaci.”

Babu wanda ya amsa min. Bangarena kuma mamakin Sarai nake yi, yara da gidan ubansu amma ta hana su sake wa. Yanzu me ye ribarta na karbe abu a hannun Assidiq

Kwanaki can ma, da umbrella ta fado Maama ta dauka, ba kunya ta ƙwakule a hannunta, wai a kofar ɗakinta ta fado, ta jira ta fado a kofar dakina.

Safiyar Asabar ta tafi Ruma,  na ji gidan sakayau, daga ni har yaran mun fi sakewa. Ji nake kamar kar ta dawo. Duk da Abbansu Khalil ya ce sati za ta yi.

Amma ko ba komai mun yi tusa mai karfi ta tsawon sati guda, ba tare da takura ko taka-tsan-tsan ba.

Saboda ni ina daga mata kafa ne, saboda Bashir, Inna da kuma Ummata, da kullum suke fada min in yi ta hak’uri, komai yana da lokaci da iyaka.

Idan aka yi hutu na fi shiga damuwa, saboda kullum sai Sarai ta samu abin da za ta yi wa yara don in ji zafi. Sannan mijinta baya taba ganin laifin ta. Zai ce ina bin bayan yara su raina ta.

Kamar yau ma da yamma ina kitchen din waje ina girki, da yake ni ce zan karbi girki. Assidiq, Haidar da Maama suna tsakar gida gaban dakina suna kwallo, don su ma sun koya.

Sarai kuma na kan entrance din ta, tana jin wakokinta. Aiko Assidiq ya daga kwallo, Sai kan entrance din ta. Caraf kuma ta cafke kwallon, sannan ta sakko zuwa inda suke, ta kama kunnen Assidiq ta murza da karfi, har sai da ya yi karar da ta ja hankalina zuwa kansu. Sannan ta jefawa Maama kwallon a kan kirji tare da fadin “Idan kuka kara jefo kwallo ta buge ni, wlh sai na yanka ta da wuka”

Ni dai tsaye na yi a kitchen hannuna rike da spoon din miya Ina kallon su.

Assidiq ya yo kaina yana kuka, Maama ta biyo bayan shi.

Tana ji na na ce, “Me ya sa kuka harba mata ball”

Maama ta ce “Bamu same ta ba Auntynmu”

Tun da Maama ta ce ba su same ta ba, na yarda, saboda tana da wayau sosai, kuma ba ta faye yin karya ba.

“ku je ku ci gaba da wasanku” na fada a dake.

Ita kuma daga can ta ce “To wlh idan suka kara buge ni sai na kwace kwallon nan, tun da dama ke ce ke sanya su suna min rashin kunya.”

Na fito daga kitchen din ina fadin “Ke ma ki haifa ki sanya su su yi min rashin kunyar. Amma yara da gidan ubansu, babu wanda ya isa ya hana su sake wa. Yadda suke so haka za su yi. Abun kin nan ya ishe ni, komai kin bi kin katanta ne.”

“Ni kike yi wa gorin haihuwa?” ta yi maganar hade da nuna kanta da yatsanta

Na ce “An yi miki, idan kin ji haushi ki haihu yanzu ko an jima”

“Zan haihu, duka yaushe daren ya yi bare gari ya waye” daga haka ta shige ɗakinta

Duk da ni ba da zummar gori na yi mata maganar ba, ta juya ta zuwa gorin sai na ji ban ji dadi ba, to amma magana zarar bunu, na riga da na furta yana iya.

Yaran na sakewa ball din su, suka ci gaba da bugawa.

Tun da Bashir ya dawo na fahimci ta gwangwaɗa mishi abin da ya faru, saboda na ga alamar hakan a kan fuskar shi.

Hasashena ya ba ni daidai, saboda kiranta ya yi a waya wai ta zo bangarena.

A falo ta cimmana, dama tuni na kora yara sama, bayan ta zauna ne ya ce mata “Fada min abin da ya faru.”

Ta karkace kai kam ta ce “Su Maama ne ke wasa da kwallo, shi ne suka jefo min, Sai na dauke ina musu da wasa na ce ba zan basu ba. Shi ne ta fito daga kitchen inda take shiga ba nan take fita ba, har ma ta ce min idan haihuwar banza ce ni ma in yi mana”

Ta karashe maganar cikin kuka

Ya kalle ni da kyau kafin ya ce “Haka aka yi?” rasa me zan ce na yi, kamar wacce aka kullewa baki. Ya kara maimaita tambayarshi, na kuma yin shiru.

Ya sauke bayyanan nar ajiyar zuciya tare da fadin “Daga yau na hana ball a gidan nan, tun da ba stadium ba ne”

Duk mu ka yi shiru ya juya kan Sarai ya ce “Tashi ki je, kuma ki yi hak’uri, haihuwa Allah ke bayar da ita. Idan ya ga dama a daren yau ma sai ya ba ki, ita kuma da take ganin ta haifa da yawa ya karɓe na ta”

A zuciyata na ce “Allahumma a’a. Ni dai Allah Ya ga zuciyata ba da niyyar gori na yi mata maganar ba.”

Bayan fitarta ne ya ce “Khadija duk yadda nake son mu zauna lafiya, kin ce a’a, in toshe wannan kafa, ki bude waccan, kin kyauta na gode miki”

Yana kai karshen maganar ya nufi upstairs.

Ajiyar zuciya na sauke a hankali, lokaci daya kuma Ina auna yadda abubuwa ke tafiya. A zahiri tun da Sarai ta zo gidan ni ce mai laifi da kuma yarana. Amma a badini abun ba haka ba ne. Wato har yanzu dai ban iya zama da kishiya ba.

Duk hasashen da nake gami da kishiya ba haka abun yake ba. Na taras abun ba dadi, ta taras da ni ma, abun ba dadi. “Allah Waheed!” na yi maganar hade da mikewa na bi bayan shi.

Time da na shiga kayan jikinsa ya ragewa, shigowa ta ce ta sanya shi dakatawa yana kallo na kafin ya ce “What again?”

Na narke fuska alamar shagwaɓa kafin na ce “Don Allah…”

“In yi hak’uri ko?” ya yi saurin tarar numfashina

Kai na daga alamar eh. Shi kuma ya ce “Ai na yi Khadija, dole ne ma in yi hak’urin, tun da idan ban yi ba, an jima ma za ki kara wani laifin, so ya fi in yi hak’urin, kar ki kara wani zuciyata ta buga”

Ya kai karshen maganar hade da shigewa toilet, murmushi na yi kaɗan kafin na shiga dakin sosai, na gyara inda ya bata, na zauna gefen gado ina jiran fitowarshi.

Bayan ya fito lafiya lau, mu ka ci gaba da sabgoginmu da shi, kamar dai ban yi laifi ba. Abin da ya yi min dadi sosai, ban yi expecting haka daga gare shi ba. Na dauka sai an kai ruwa rana, kafin komai ya daidaita.

Ranar da zan fita aiki ne nuna zaune, muna lissafa wasu kudin kaya da aka turo min, bayan mun gama na ce “Ranka ya dade, ina son zuwa gida don Allah idan ba damuwa”

Ba tare da ya kalle ni ba ya ce “Yaushe kenan?”

“Next idan an yi wa yara hutu” na ba shi amsa.

Sai da ya dauki lokaci kafin ya ce “, Yanzu fa tafiya a wurinki ta kwana gaskiya za ta yi wahala, saboda kin yi nauyi da yawa. Kin ga dai su Affan girma suke ta kara yi, ga shi kin ɓata yaranki, daga ke sai ke, waye zai iya zama dasu?” ya kai karshen maganar cikin tabe baki

Idanuna a kanshi na ce” Ban gane na ɓata su ba? “

Idanunshi ya saka cikin nawa kafin ya ce” Kin bata su mana, a tunaninki bayan ba kya gidan nan, Nana ta isa ta hana su, ko ta sanya su. Ai ko ni kaina su Khalil a kan ki, suna, ganin dama ta. Ke ce kawai suke kiyayewa fushi da ɓacin ranki”

Hannuna a kan haɓa alamun mamaki na ce “Wace irin magana ce kake yi haka?”

“Gaskiya mana Khadija. Kuma ke ma kin san gaskiyar ne ai. Saboda haka babu inda za ki tafi ki bar su. Sai dai idan ranar za ki je ki dawo a ranar. Wannan kam. Idan kuma tattarasu za ki yi ku tafi, to sai kun dawo”

Kallon shi kawai nake yi, saboda with full confidence yake maganar babu alamun wasa a yanayinsa.

“To idan haka ne ya fi in tafi kafin a yi hutun, ka ga time da zan dawo su ma sun dawo daga makaranta”

“Shi kenan ma”

Da wani mamakin nake kallon shi, kafin na ce “Wai don Allah wane kallo kake yi min gami da su Khalil ne?”

Kai tsaye ya ce “Kallon uwa mana, wacce take bin bayan yaranta ko sune da gaskiya ko a’a. Uwar da Sai wanda ta zaɓa yaranta suke girmamawa”

Kai na shiga jinjinawa kafin na ce “Sosai nake mamakinka, amma akwai lokaci, saboda yanzu duk abin da zan fada ma ba yarda za ka yi ba”

“Kin ga shirun shi ya fi”

“Gaskiya kam, yanzu yaushe zan tafi din”

“kafin girki ya zagayo kanki”

Kai na jinjina alamar fahimta, kafin muka koma kan lissafin da muke yi tun farko.

Tsaraba sosai Bashir ya yi min ta zuwa Kano, yara kam duk sun damu, duk da na ce musu a ranar zan dawo amma sun ki sakin jikinsu.

Ita kuwa Madam Sarai tsarabar ce ta tsone mata ido, saboda sai kumbure-kumbure take yi da haibace-haibace.

Sosai nake mamakin haibace-haibacen Sarai, na rasa yadda aka yi ta koyo, duk lokacin da za ta tsiri waka, Sai ta yi daidai da halin da nake ciki.

Yanzu ma zaune take a kan entrance din ta tana danne-dannen wayarta, ta kuma yin wakarta ta, habaici “Wai Allahn ba ta kishiya mai yawo kafin ta dawo ta ci duniya”

Wai “ba kishiya take tsoro ba, kishi da ballagaza abin gudu”

Kalmar ballagazar nan ba karamin kona min rai ta yi ba. Amma tun da ba ta fito kai tsaye ta ce da ni take ba, dole na in yi hak’uri.

<< Hasashena 36Hasashena 38 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×