Skip to content
Part 46 of 49 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Time da na dawo waya take yi, na zauna kan kujera ina sauraron ta, abin da na fahimta kamar case a kan fyade.

Bayan ta idar da wayar mu ka kara gaisawa, sannan na ce “Kamar ba ki ci abincin ba?”

Ta ce “Zan ci yanzu, wani abu ne ya bata min mood dina”

“Ai sai hak’uri Allah Ya kyauta”

“Amin” ta ce amsa lokaci daya kuma tana zuba masa cikin plate ta ce “Ita zan ci”

Murmushi na yi ba tare da na ce komai ba, ita ce ta kuma cewa “Wasu iyayen kamar basu cancanta zama iyaye ba. Case din wata yarinya ne da ba ta wuce 10-11 years ba. A ka yi mata fyade, wai shi ne uwar ke ba wakilanmu labarin, ai yar tun da dadewa ta fada idan aike ta, mutumin yana kiran ta ya cire mata wando. Amma saboda shashanci uwar nan sai ce ma yarinyar ta yi idan ya kara tare ta ce mishi wai tana jin kunyar shi, ita fa uwar ce ma yar ta fada mishi ita uwar tana jin kunyar shi, me ya sa ita ba za ta je ta fada mishi da kanta ba, daga karshe dai ya yi rapping yarinyar “ta karasa maganar cike da bacin rai.

Ni kaina sai na ji kamar in rufe uwar da duka, wane irin sakarci ne haka gami da wawanci, rayuwar yarka mace ka yi wasa da ita. Haka mu ka shiga tattaunawa a kan abun, tana kara ba ni  different cases wadanda akwai sakaci a ciki.

Har Murja ta same mu, aka dora hirar da ita, abun da na fahimta Zarah ba ta da bakunta, kuma tana da wayewa sosai da iya mu’amala. Kuma da alama ta kware wajen cudanya da mutane kala-kala.

Arround 3pm ta ce “Ya kamata in wuce fa, jirgin 7pm na yi booking”

“Ba nan za ki kwana ba?” na tambaye ta ina nuna mamaki a kan fuskata

Ita ma baki bude ta ce “Kwana kuma?”

“Eh mana, na dauka sai kun raka amarya daki ai”

Cikin dariya ta ce “ko damu ko bamu yau amarya dakin ta da za ta kwana”

Duk mu ka yi dariya Murja ta ce “Amma za mu fi jin dadi da ku din”

“Don Allah kira min Oganki, tafiya zan yi” cewar Zarah tana dariya.

Ni ma dariyar nake na shiga lalubar Abbansu Khalil, ba jimawa ya daga “Na ce bakuwarka wai za ta tafi”

Ya ce “Haba tun yai, ba ta wayar”

Wayar na mika mata, kasancewar tana hands free kowa na jin abin da ake fada daga can bangaren ya ce “Ranki yada dade wai za ki tafi?”

Murmushi ta yi kafin ta ce “Ba wai ba ne yallaboi”

Ya dan yi dariya sannan ya ce “Ya yi wuri, ga shi ba mu gaisa ba”

“Bai yi wuri ba, zan dan leka gida mu gaisa, sannan kuma jirgin 7pm na yi booking Kar ya tafi ya bar ni”

“Ko ya tafi zai dawo ya dauke ki koda ke kadai ce kuwa, trust me” ya karasa maganar cikin dariya

Ita cikin dariyar ta ce “I trust to you, amma ka zo zan wuce”

“Shi kenan gani nan zuwa” wayar ya yanke, ita kuma ta miko min ran murmushi.

Sannan ta shiga kintsa jikinta, na ce “Wai ba za ki jira ki yi sallahr la’asar ba”

“Zan yi a gida” duk mu ka yi gajeruwar dariya, daidai lokacin Baban Khaleel ya yi sallama, na mike zuwa kofar saboda na san ba zai shigo ba.

Sai kuma na dawo cikin dakin na ce ta fito, bangaren Inna mu ka je ta gaishe ta hade da yi mata Allah Ya sanya alkairi, sannan ta ciro kudi masu yawa ta ce a siyawa amarya tsintsiya. Kayan biki na hado mata cike da leda, irin su cincin, alkaki, dublan da kuma daƙuwa. Sannan na saka mata robobin da aka raba, da take away minerals da kuma ruwa.

Bashir ya ce ya kamata ta je gidan kanenshi Salisu su gaisa da amarya. A kan hanyar zuwanmu gidan ne mu ka hadu da su Khalil, yana dauke da Haidar sai kuma Mama da Assidiq da suke biye da shi.

Zahra ya fara gaisawar, kafin mu, na amsa mishi ina karbar Haidar daga hannun shi. Abbansu kuma ya ce “wannan sune yarana, wannan Khaleel kenan, Yayan Affan ne, mai issue din kunne da kika gani a cikin jirgi”

Kai ta jinjina alamar fahimta lokaci daya kuma tana shafa kan Khaleel

“And this is Sakeena (Maama) Assidiq and Haidar”

“Ma Sha Allah. Nice family Allah ya albarkace su”

Muka amsa da amin gabadayanmu, sannan ta ce “Big brother ina yake makarantar Shi yanzu?” ta yi maganar idanunta a kan Khalil

Cikin halin ko in kula Bashir ya ce “JSCE ya yi, amma wai yanzu boarding yake so Kuma airforce comprehensive Abuja.”

“To me ye ba school ba ce?”

“Haba ta yi nisa” ya amsa ta

Ta ce “Ni da na kai nawa India fa”

“Ai naki sun yi girma” ya ba ta amsa

Ta ce “No! No!! Please Yallaboi, don Allah mu rika ba yaranmu dama, makarantar ai mai kyau ce, suna kula da yara, tun da can yake so a kai shi don Allah sai dai ko idan akwai matsalar kudi”

“Babu ma, kawai dai ta yi nisa sosai”

Ta juya kan Khalil ta ce “Big bros kana son makarantar?”

Kai ya jinjina alamar eh

Ta ce “Sha kuruminka, zan siya ma form, kuma In Sha za ka samu damar zuwa interview har ka tsallake”

Khalil ya shiga murna, yadda yake ta shauki ne ya sanya ni yin dariya har da kai mishi dukan wasa. Ya yi saurin gocewa yana dariya. A haka muka isa gidan amarya take Zahra na ta convincing Bashir a kan batun Khalil

Still Sai da ta kara yi wa amarya ihsani kafin ta tafi.

Bayan na dawo bangaren Murja na zarce na yi sallahr la’asar, ina tsaka da cin abincin da Zarah ta rage Murja ta shigo, ita ma sai ta zauna mu ka fara ci tare.

Ta katse shirun namu da fadin “Wai a ina Yayanmu ya samo wannan matar?”

Hannayena na watsa kafin na ce,” ina  na sani, kin san shi namamajo ne sarkin mata”

Dariya ta yi mai sauti kafin ta ce “Yayanmun?”

Ni ma dariyar na yi sannan na ce “Ba ga shi kin gani ba”

Ta ce “Amma fa wannan matar kamar ta fi karfin shi, ke kina ganin ta ƙyar da ita.  Ina! zaren ba kalar yadin ba ne”

Cike da mamaki na ce “Aiko kalar yadin ne, me matan suke so? Ba kudi ba? To kin san dai Bashir yana da su”

Kai ta jinjina kafin ta ce “Gaskiya kam, Yayanmu akwai naira, ba ki ji sunan shi ba ma, mai ɗangyashin kudi”

Duk mu ka yi dariya a tare, ta dakata da dariyar da take yi sannan ta ce “Amma duka yaushe aka gama da batun Sarai, har zai kara jajubo wata?”

“Ke fa kika ce namijin da ya saba zama da mace biyu, baya iya zama daya”

Ta ce “Gaskiya kam, kuma akwai kudin auran, Allah Ya zaba ma fi alkairi”

Ina shan coke na ce “Kin ji addu’a, ni yanzu ba ni da zabi a kishiya, kawai batun Maman Aiman in ta so zaman lafiya shi kenan, idan kuma ta ce bala’i, a yi ta yi daga nan har birnin Sin”

Murja ta kwashe da dariya sannan ta ce “Wato kin kara gogewa”

Na mike tsaye ina daukar gyale na, na ce “Sosai, ai tun da na zauna da Sarai, to ko kura ce a yanzu zan iya zama da ita. Ai na ga bala’i Murja, kai subhnallah yarinya kamar ta hada iri da dage, fadan yanzu daban na an jima daban. Allah Ya kyauta”

Ita ma mikewa ta yi tsaye tana dariya tare da fadin “To amin”

Haka muka karasa cikin gida muna tattaunawa.

Bayan biki a nan Ruma muka gama hutunmu sannan mu ka koma Katsina cike da tsarabar kauye.

Tare da Bashir mu ka yi gyaran, ko ina fes, glass din windows tuni an canja wani.

Ranar Asabar Bashir ya zo min da maganar wai su Khaleel za su yi interview ranar Laraba, don haka ana son ganin daga gobe Sunday zuwa Monday. Khalil dai murna Kamar an ce gobe Affan zai dawo, haka ma ya dame ni sai in kira Affan video call ya fada mishi, na kira shi kam, suka yi ta shirmensu da su Farhan.

Ranar ba mu kwanta bacci ba sai da mu ka shiryawa Khalil kayan tafiya, a cikin daren na yi mishi cincin da dambun nama, na loda mishi biscuit da kananun drinks.

Safe kam suka dau hanya shi da Babanshi, wai Kaduna zai kai shi wajen Zahra ita ce za ta wuce da shi Abujar.

<< Hasashena 45Hasashena 47 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×