Skip to content
Part 58 of 58 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Daga lokacin da aka kai kudin auran Salman Ruma, daga wannan lokacin gidan ya koma babu wata magana sai ta bikin Salman da Maama, babu wani shiri sai na bikin Salman da Maama, kullum maganar kenan kamar hanyar daka, ni kaina duk na faɗawa ƴan’uwa, kowa sai Sam-barka, ban ji wani wanda ya kawo min rashin dacewar hadin ba. Wata hudu aka tsayar, wannan ya kama da Maama ta gama exam din 2nd semester year 2.

A cikin watanni hudun nan kowa hidimominshi sun ishe shi. Ga Zahra ta ce ita sulaibiyar ba za ta saka a hidimar bikin Salman ba, ita ma tata hidimar ta ishe ta, wai kowa ya ci tuwon gidansu.

Duk lokacin da aka yi hirar bikin haka take maimaitawa.

Ranar da dare Bashir na dakina muna hira, har mu ka sako hirar bikin, wacce dama zai wahala mu zauna ba tare da hirar ta shigo cikin hirarrakinmu ba.

Zama ya gyara hade da fuskantata ya ce “Khadija zan saka gidan nan a kasuwa fa”

Da sauri na ce “Me ya sa?”

“Saboda hidimar bikin yaran nan”

A sanyaye na ce “Shi ne kuma har da siyar da gida, to mu ina za mu koma kenan? Idan babu damar yin bikin yanzu a jira ta kare karatun mana kamar yadda Barrister ta bukata”

Kai ya girgiza tare da fadin “Ba bukata, zamu tare a sabon gidanmu karshen month din nan, kuma zan bude companyn magunguna kwari, upper month, Ga bikin yaran nan, kuma gidan nan babu abun da zan yi da shi, don haka zan siyar kudin su shiga cikin wata hidimar”

Kai na jinjina, saboda yanzu kam na gamsu da maganar sayarwar sabanin baya. A nutse ya ce “Ki zauna ke da Salman ku lissafa nawa za a kashe a lefe, sannan me ya rage a ginin gidan shi”

Kai na jinjina alamar fahimta, haka dai mu ka rika tattaunawa da tsara abubuwa yadda za su tafi babu takura.

Da safe misalin 10am na kira Salman a waya, na ce ya same ni daki, ba jimawa kuwa ya hauro, bayan mun kara gaisawa ne na ce “Abbanku ya ce a tambaye ka menene ya rage a gininka?”

Shiru ya dan yi kafin ya ce “Auntynmu zan yi, ina da kudi fa”

“Ni fa kawai sako aka ba ni. Don haka ka shirya an jima mu je gidan in gani”

Bai kai da ba ni amsa ba, Barrister ta turo kofar ta shigo, cikin kwalliyar doguwar rigar atamfa, da ta sha stone work, kafadarta ɗaya sagale da gyalen da ya dace da shigar tata, kamshinta ya cika dakin, bayanta kuma Maama ce ita ma sanye cikin Egypt Abaya, baka ta yi rolling veil din, sosai ta yi kyau.

Ta bi mu da kallo, kafin ta ce “Me kuke cewa?”

Murmushi na yi kafin na ce “Shawara muke yi, ko sai kin ji?”

Ita ma murmushin ta yi kafin ta ce “Ni ban ce ba, zuwa na yi in fada miki za mu je Ruma”

Mamaki shimfide a kan fuskata na ce “Me ake yi?”

Cikin dariya ta ce “Sirrinmu ne” ta juya tana kallon Maama cikin dariya

Zama na gyara tare da fadin “Ba dai kararmu za ki kai ba Barrister”

Dariya ta yi kafin ta ce “Ai kin san dai Inna ba za ta goyi bayana ba, za ta ce Maama ta girma dama”

“Na sani ko ki baje mata hujjoji, da za ki yi convincing din ta”

Na kai karshen maganar ina kallon Salman da ya kike zuwa kafor fita, Maama ta bi bayan shi

Barrister ta ce “Yaran nan basu da kunya wlh. Ai gara ma dai a yi auran mu huta”

Mikewa na yi ina dariya kafin na ce “Au! Yanzu kuma kin sakko”

“To yana iya kun fi karfina. Amma ai sai an yi agreement Maama za ta ji gaba da karatunta”

“Wannan kuma ban sani ba, mu je in ba ki turare ki kai wa Inna”

Tare muka sauka, na hada mata tsarabar Inna, sannan na mu ka wuce parking space, ita da Adnan da kuma Affan za su tafi, Sai Ramla.

Bayan sun tafi ne Salman ya ce in shirya mu je gidan “

Aikin abincin mu ka bar wa Maman Usi da yar aikin Zahra mu ka tafi.

Na rika mamakin ginin Salman din, gini ne mai kyau na zamani, bai faye girma ba kuma bai yi kankanta ba, zaman mutum daya ne, amma tsarin ginin ya burgeni. Abin da ya rage ba a yi ba, pop fenti, da wearing. Amma har tiles an saka, interlock. Na rika yaba gidan abin da ya rika yi wa Salman dadi.

Time da na dawo su Maman Usi har sun gama abinci rana, don haka sallahr azhur na yi, mu ka hau ci.

Da yamma misalin karfe biyar su Zahra suka dawo, kai tsaye kuma dakina ta yo wa tsinke.

Ledar karas din da ke hannunta ta ajiye kan mirror tana fadin “Auntymu gulma na kunso miki da zafin ta” ta kai karshen maganar tana janyo stool din mirror

Karas din na dauka guda daya ina dariya kafin na ce “Fesa min”

Cikin salon gulmar kuwa ta ce “Yau dai na ga Nana Saran ki”

Ido na fitar waje alamun mamaki kafin na ce “Don Allah fa? Yar bala’i za ki ce min, wannan mata yar tijara  ce , a ina kika ganta?”

Dariya ta ɗan yi kafin ta ce “A Ruma har da cikin ta tsoho”

Haba na rike kafin na ce “Ko ina aka sauka oho, wanda ya dauka yana fama, idan tana da abokiyar zama har na tausaya mata”

 Zahra ta ce  “Allah na dauka wata babba ce, na ganta yar karama”

Baki na bude hade da zaro ido kafin na ce “small pepe kenan, kananun barkono ba girma sai bala’i”

“Haka aka ce wai mijin ta yi wa duka, da tsohon cikin nata fa, wai yana bayi yana wanka, haka ta rufe shi da duka ta janyo shi waje” ta karasa maganar cike da mamaki

Ni kaina da mamakin a fuskata nake kallon Zahra ,  ta dora da “Na rasa wane irin kalar miji ne ma ta aura, ace mace ta yi ma duka”

Ina tauna Karas din da na balla tun dazu na ce “Wlh za ta iya, ke yar bala’i ce ta gidan gaba, ni komai aka ce ta yi zan yarda, ta ba ni wahala wannan matar, Sai dai Allah Ya sa kaffara ne”

Wata irin dariya Zahra ke yi ta ce “Allah sosai kike ba ni dariya, amma Auntynmu fisabilillahi wane irin sokon miji ne, har ya zauna yarinyar nan ta buge shi”

“Saboda ba ki san bala’inta ba ne, to in fada miki ranar da mu ka yi fadan karshe wlh mu uku dakyar mu ka iya da ita”

Daga kan stool din Zarah ta sakko saboda dariya, sannan ta ce “Wai har da honorable din”

“Har da shi in fada miki, kin san Allah gaban shi ta kama ta murde sai ni ce na kwace shi”

Wata irin dariya mai sauti ta kuma saki, ni ma ina taya ta, daidai nan Bashir ya turo kofar ya shigo, tsaye ya yi yana kallon yadda muke dariya kamar mahaukata.

Ya yi ta kallon mu komai bai ce ba, mu ma kuma ba mu fasa dariyar da muke yi ba, Sai volume da Zahra ta kara.

Baki ya tabe kafin ya ce “Allah Ya ba ku lafiya”

Na amsa da amin, kafin na ce “Barrister ke fada min ta hadu da Nanarka”

“Wacece haka?” cikin rashin fahimta ya yi tambayar

Na ce “Nana Saratu babbar masoyiyarka” fuska ya hade, kafin ya juya ba tare da ya rufe mana kofar ba.

Zahra kam sai ta kuma kwashewa da dariya, ni kuma ina taya ta, a haka ta bi bayan mijinta tana dariyar mugunta.

Yanzu kam hankalinmu ya fi karkata ne a kan komawa sabon gida, Bashir ya yi iya kokarin shi, daga nan ya ce wanda yake bukatar karin wani abu sai ya yi da kanshi. Ban hare kain ba, abin da na ga ina bukata kuma bai fi karfina ba shi na yi.

Karshen wata mu ka tare a sabon gidan, duk yadda Bashir ya so a tare da Innar Ruma saboda akwai part din ta kin yarda ta yi, wai ita ba za ta iya barin garin ta ba.

Daga yadda na ga Bashir ya yi gini na fahimci ya kazance da kudi, tangamen man gida mai dauke da part hudu, na shi da Inna a jere, Sai nawa da Zahra ma a jere. Kafin isowa part namu, Sai ka wuce dakuna guda goma, biyar a jere, biyar a jere suna fuskantar juna, Sai doguwar farfajiya mai dauke da furanni masu kyau da suka kawata gefen entrance din.

Akwai parking space na samarin gidan, daga nan kuma sai gate din da zai kawo ka cikin namu part din, shi ma akwai farfajiya mai matukar girma, sai kuma wata kofa wacce za ta kai kalambu mai dauke da swimming pool a tsakiya. Ku san akwai ko wace bishiya da ake yi akwai ta. Still akwai wata siririyar hanya wacce shuke-shuke suka kayata, idan ka bi ta, za ta kai ka katon ɗakin taro ne hall, mai dauke da kujeru masu yawa. An kashe kudi wajen kawata gidan kuma an samu abin da ake so.

Lokacin da ƴan’uwana suka zo yi min fatan alkairi, Ummata har da kukanta, wai ko mafarkinta bai taba ba ta zan rayu a irin wannan gidan ba, ba ita kadai ba, ni kaina ban yi tunanin in rayu a irin wannan gidan ba, Allah kenan mai azurta wanda ya so a kuma lokacin da ya so.

Bayan tarewarmu sabon gida sai kuma bikin bude kamfanin maganin kwari na Bashir, nan ma shagali aka yi hade da nuna capacity iya capacity, Har shugaban kasa sai da ya zo.

Zuwa lokacin bikin Maama da Salman saura wata daya, don a lokacin Maama ta fara Exam, don haka ni da Zahra da Bashir din kowa ba zama, ita tana ta fama da siyayyar kayan kitchen ni kuma hada lefe.

Duk wanda ya kawo gudunmuwar bikin Maama a ƴan’uwana zan ce a ba Zahra, ita ce uwar ƴa, hakan kuma ba karamin dadi yake yi mata, ita duk abin da ya shafi Salman za ta ce a zo wurina, ni ce uwar ango.

Yanzu ma zaune nake a falo ina kallon Khaleel da ke shirya kaya a cikin akwati, Zahra ta shigo idanunta a kan akwatunan, kafin ta dan bata fuska tana fadin “Auntynmu akwatuna fa set biyu za ku yi mana.”

Ina miƙawa Khaleel wasu atamfofi na ce “Idan mun kawo maku wadannan ku maido mana don Allah, daga haka mun yi kenan auran wani da wata”

“Aiko kararku zan kai wajen Honor, ko kuma mu rage kayan da mu ma mu ka saya”

Cikin ido nake kallon ta kafin na ce “Me kuka siya ba fridges ba ne da tukwane, ku rike abun ku, ya zo nan ya dauki nawa, dariya hade da zama kusa da Khaleel da shi ma dariyar yake yi, sannan ta ce” Ka ji mugun abu. Amma maganar gaskiya ku karo mana guda hudu zu zama goma “

Komai ban ce ba, Khaleel ne ya ce” Shakurumin ki Momy set biyu, dayan set din na Abuja, idan su Adnan za su zo, za su taho da shi”

“Yanzu na ji batu, ƴar tawa rangadediya, ace da akwati shida, abunta reps uwarta Barrister” ta yi maganar tana zundena, Khaleel ya kuma yin dariya. Zama na gyara sannan na ce

“Ke kin san a zube faifai wlh Salman ba sa a Maama ba ne, ta ko wane bangare ba sai na lissafo miki ba. Ita ce da godiya.”

Khaleel ya mike lokacin da ya gama rufe akwatunan, yana fadin “Ni ma fa Abujan nan zan bi su Affan, wlh na gaji da zirga-zirga, kamar ni ne Angon”

“Ka yi tafiyarka ka kyale su, su yi abun su” cewar Zahra tana kallon Khaleel

“Madame ba ki fa bamu gudunmuwa ba har yanzu” na yi maganar ina kallon ta

“In ba ku ƴa, in zo kuma in yi muku gudunmuwa, lallai ma Auntynmu”

Kasancewar ina wani lissafi shi ya sa ban ba ta amsa ba, Sai bayan na gama ne na ce “Salman ya ce kin hana pre wedding pictures Wai?”

Kai tsaye ta ce “Eh”

“Me ya sa?” na kuma tambayar ta

“Ba na son wannan watsewar da rashin kunya ta ƴaƴan zamani, fisabilillahi sai Salman ta je da Maama su yi hoton banza su sake a media kamar basu da iyaye, ba su jin kunya”

Zama na gyara kafin na ce “Wa ya ce miki na banza za su yi?”

“Akwai ba kirki ne Auntynmu?”

“Sosai ma, za a fara daga kansu idan ma babu, amma ki kyale su su yi tun da suna so, Sai ki fadi sharuddanki”

Kallo na kawai take yi, murmushi na yi kafin na ce “Ko hakan bai yi miki ba?”

“Kina daurewa yaran nan fa, komai suka ce sai ki ce to.”

Wata dariyar na kara yi ina fadin “Na ce ki fadi sharuddanki”

“Ba na son ko hannunta ya rike” ta yi maganar hade da tamke fuskarta.

“An gama ranki ya dade”

Siririn tsoki ta ja kafin ta ce “Allah don dai kin san baki, amma bana son wancan shafe-shafe da rungume-rungumen nan, tsakani ga Allah ya yi kama da tarbiyyar musulunci da al’adar Hausawa”

Kai na shiga girgizawa alamar a’a, kafin na ce “Gaskiya kam basu dace ba, wani abun babu alkunya a ciki, amma ba zan bari su yi hakan ba, ke ma kin sani”

“Allah Ya sa”

Na amsa da amin, kafin mu ka ci gaba da tattauna yadda bikin zai kasance.

Lokaci na kara matsowa, hidima na kara karuwa. Ita kanta amaryar ba ta zauna, ga jarabawa ga zuwa gyaran jiki, ga wancan ga wancan. Har ta zube.

Satin da ta gama exam din ya kama saura 2weeks biki, a wannan lokacin hankalinmu yana kan gyaran gidan Salman, duk yadda Zahra ke waskewa sai da ta shiga, saboda miliyan biyar ta turo min a account wai ba don halinmu ba. Ni dai dariya kawai na yi. Ni dama store dina na kayan kitchen suka je, suka hado duk abin da suke so na kitchen, wai shi ne gudunmuwa ta.

Ya kama saura sati daurin aure su Maama suka tafi pre wedding picture, bayan na lissafa masu sharuddan da Zahra ta gindaya masu, ni ma na dora da na wa.

<< Hasashena 57

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×