Da dare sai da Bashir ya kori su Khaleel zuwa gida, wai ba su son tafiya su bar ni. Tun safe kam sai ga su, don karfe bakwai a gidan ta yi masu.
Kuma duk yadda nai ta korarsu su tafi na ji sauki, kin tafiyar su ka yi, har zuwa lokacin da Zahra da Maman Usi suka gama abincin breakfast, bayan sun karya ne suka dauki na matansu.
Ba jimawa suka kuma dawowa, Zahra ta ce “Wai a hanya za ku gama naku angoncin ne?”
Affan ya ce Auntynmu “Momy ko mun zauna hankalinmu yana nan, kuma gidan ma duk baƙi”
Ni dai murmushin jin dadi kawai nake yi, ko yanzu na mutu Alhamdulillah, bare ma sosai na warware.
Zahra dai duk kin jininta da girki haka nan, take shiga ta yi shi, gidanmu ya fi karfin take away yanzu, zuriya ta kara karuwa. Ni kuma ina sane nake langabewa in ki shiga kitchen din.
Bayan sallahr isha’i sai ga su Khaleel ko wanne da matarshi, wai sun zo, yi min sannu, ko waccensu a lullube wai kunya, ni kuma wani dadi nake ji, yau ga ni ga matansu Khaleel. Bayan mun gaisa suka tafi bangaren Zahra, a can suka ci abinci, don sun fi sakewa da Zahra ni sosai ake surukatar da ni.
Around 9pm suka shigo yi min sai da safe.
Haka kullum su Khaleel ke zuwa da safe su, gaishe mu, da dare kuma su dawo yi mana sai da safe.
Sati biyu da biki Khalil ya koma wurin aiki, amma Hana na Katsina, shi ya sa ta dauke Hassana tana ta ya ta zama, idan Khaleel ya dawo kuma ta dawo gida.
Bayan bikinsu Affan abubuwa biyu mu ka mayar da hankali a kai, ginin asibiti wasu Affan, Baffa da kuma Salman. Sai kuma ginin masallaci mai hade da Islamiya, wanda zai zama sadakatul-jariya wa Sakeena. Aikin zai kasance a Ruma da kuma cikin garin Katsina. Shi ya sa kowa a cikinmu aljihunshi na fada mishi, aiki bai bar kowa ba, abu ne da za a yi wa taro dangi a samu a fitar da jaki daga duma.
Duk Lahadi su Maama Hana, da Maama matar Baffa, Maryam matar Affan a gidanmu suke wuni, su suka tsarawa kansu haka, ba mu ne mu ka tsara musu hakan ba. Kuma ko waccensu ta kan yo abun kusa da baki ta taho da shi. Hakan sosai yake min dadi da sanya ni farin ciki, kansu a hade yake babu wani kishin balbali, duk da dai tafiyar yanzu aka fara ta, amma ba na jin ko nan gaba hakan zai faru, kullum ina addu’a Allah Ya hade kawunansu, ya zaunar da su lafiya, su da wadanda za a auro daga baya.
Yanzu ma duk sun baje a falona suna cin abincin rana, lokaci daya kuma suna video call da Ramla, wacce kullum ke cin begen gida, wani lokaci idan ta botsare sai na kira ta, na yi mata na ƴan garinsu (Ta katsinawa) sannan take sakkowa.
Bayan sun yanke kiran ne Maama babba ta ce “Ramla ta ki sakin jiki ta yi Kiba, kalle ta kullum kamar figaggiyar kaza”
Hana ta yi dariya kafin ta ce “Nesa da guda fa babu dadi, ta ce min ku san kullum sai ta yi kuka, musamman idan ta gan mu haka din nan, ta ji Ina ma tana tare da mu”
“Eyyah! Baiwar Allah, haka ni ma take ce min” cewar Maama karama.
Hassana ta ce “Ai Ramla ba ta da wayau, ni me zai dame ni na haura kasa, kwantar da hankalina zan yi in yi ta cin biryani da yaji. Ke kellon kyawawan indiyawa din nan ma kadai ya isa ya sanya ni kina. Ga wuraren shakatawa da zan rin ka fita, kafin kun an kara na canja, ba za ku gane ni ba”
Haidar ya ce “Ana maganar masu hankali wa ke saka ki Hassana, ke idan dai da abinci ai labari ya kare.”
Husaini ya ce “Ashe kowa ya santa, komai ta ci abinci dai, kamar ba ta samu a gida”
“Lafiya ke ci” cewar Hassana hade da jefa loma a bakinta. Duk da ba na cikin hirar tasu sai da na yi dariya
Salman ya shigo saɓe da Khairiyya ta sha kuka, amma fuskar nan raɗau, kitso suka kai ta shi da Maman Usi.
Hana ta ce “Wayyyo Allah yarinyata, haka kika koma daga yin kitso” duk mu ka yi dariya, yayin da kowa ke nuna kulawarshi a kanta.
Maama ta ce “Auntynmu ni dai don Allah a yaye yarinyar nan yau, ni kadai na san azabar da nake sha cikin dare wajen tsotso”
Ina kallon ta na ce “Ba ni da matsala, amma ki jira mamaki ta dawo, ni dai ba zan dauki yaye ba. Haka kawai a hana ni bacci”
Maryam ta yi dariya tana fadin “Aunty Maama ki kawo ni in yaye ta”
Da sauri Maama ta ce “Rufa min asiri, cikin dare Ya Affan zai kira ni, yana fadin” Don ubanki ki zo ki dauke ta, kin san ai ba za ta zauna ba kika kawo ta. Idan ba ki zo kin dauke ta yanzu ba sai na ci uban ki”
Duk falon kowa ya yi dariya har da Salman da ke cin abinci. Maama ta kuma cewa “idan kuma ya Khaleel sai ki ji, Maama ba za ki yi hankali ba ko? , wannan yarinyar yaushe ta isa yaye, kin kawo ta ga shi sai kuka take yi ta ki yin bacci. Idan dai ba ta yi shiru ba, har zuwa gobe zan kawo maido miki ita”
Mu ka kuma yin dariya Hassana ta ce “Ya Baffa kuma sai dai ki ji ana buga miki kofa, idan kin bude ya dire ta, ya ce ni ba mahaukaci ba ne, da hankalina, ba za ki hada kai da ni ki yi kisan kai ba”
Mu ka kuma yin dariya Hassan ya ce “Idan kuma Auntynmu aka kawo ma wa, Sai ki ji Ya Assidiq yana fada, me ya sa ma za ki amshe ta, ga shi nan ta hana mutane bacci, ta cika masu kunnuwa da kuka, ita Maaman tana can tana baccinta ke kina wahala, to wlh gobe da sassafe zan kai mata yarinyarta don uban ta, ba za ta hana ki bacci ba. Sai ya juya kan Khairiyya ya ce ke don uwarki rufewa mutane baki, ba uwarki ce ta kawo ki ba”
Na mike tsaye cikin dariya da zummar barin falon, yayin da Salman ke fadin “Duk ku sha kurumin ku, mu zamu yaye abun mu da kanmu, tun da yau duk kun fallasa kanku”
Ni dai nan na bar su suna ta hayaniyarsu.
*BAYAN SHEKARA DAYA*
A cikin shekara ɗayar nan abubuwa da yawa sun faru, daga ciki akwai haihuwar Hana da kuma Maama karama, dukkansu maza suka haifa. Na Hana Abdallah, na Maama karama Kabir ana kiranshi da Abie. Maama babba Maryam kuma ana ja, Ramla kuma ta samu miscarriage.
Assidiq an sanya bikinshi da siyar Umaima kawar Maman Hana mai suna Jidda. Sai Ziyad yaron Maman Hana na biyu, da Hassana. Yusuf yaron Rahma da Ihsan, ita kuma diyar kishiyar Maman Hana ce. Gaba ma muna da shan shagali
Yanzu dai shagalin da ke gabanmu na bude sabon asibiti ne mai suna Sakeena Memorial Hospital. Babban asibiti ne da aka yi wa ginin zamani, aka kuma tanadi kayan aiki na zamani. Ya samu amincewar kungiyoyi da hukumomin lafiya.
Satin da za a bude asibitin Rahma da tawagarta suka diro nigeria, amma ana saura kwana uku bikin budewar ta iso Katsina har da Ramla. Farin ciki a wurin Ramla da ƴan’uwanta ba a magana, ni kaina dai ina cikin farin cikin, ana saura kwana biyu bikin budewar kuma Zahra ta diro ita ma. Ranar kuma da dare matar Affan ta haihu budurwa, farin ciki da murna suka kuma cika zukatanmu.
Ranar bikin bude asibitin duk wanda yake cikin garin Katsina ya san akwai wani abu muhimmi da yake faruwa, saboda yadda motoci da jirage suke sauka, na rika ji na kamar ba ni ba, duk da ba ni ce na haifi su Khaleel ba, amma na yi farin ciki saboda ta dalilinsu mutanen da ban taba tsammani ba sun taru, haka aka bude asibitin cikin farin ciki, sannan aka shiga zagayawa da mutane a cikinshi. Duk suna yabawa, hade da daukar alkawuran kawo nasu tallafin, musamman ingina da suka shafi ayyukan asibitin.
Karfe hudu taron ya tashi, dukkanmu mu ka dawo gida a ajiye, still a daren Maama ta haihu, a wannan karon ma mace. Wannan ya sa aka daga bikin sunan Maryam din Affan aka hada shi da na Maama. Rahma ba ta koma Abuja ba sai da aka yi sunan matar Affan, ni ce na matsa lallai Sakeena za a sanya, amma da cewa ya yi sunana za a sanya. Yarinya ta ci sunan Sakeena, ana kiran ta Khairat. Yarinyar Maama kuma Zahra aka yi wa takwara, ana kiran ta da Ummie.
Bayan bikin bude asibiti aka koma shirin bude Islamiyar Sakeena Memorial Islamiya wat-tahfizul Qur’an
Su Salman kuma sun kama aiki gadan-gadan a sabon asibitin da aka bude masu, cikin kankanen lokaci asibitin ya yi suna gami da yin fice, saboda suna da kwararrun likitoci, Hana Gynecologist, Maama professional nursing, Salman medicine, Affan ENT, Baffa likitan zuciya, sai kuma sauran ma’aikatan, wanda basu dauka karabiti sai kwararrru.
Bayan arba’in din su Maama aka yi bikin bude Sakeena memorial Islamiya. Babbar makaranta ce ginin zamani, akwai masallaci da kuma borehole, har da tuka-tuka da kuma rijiya. Akwai bishiyoyi masu yelwar inuwa da suka kawata ciki da wajen makarantar.
Ta katsina aka fara budewa, bayan kwana biyu kuma muka nufi Ruma don bikin bude waccan Islamiyar.
A can muka kwana, da yamma mu ka iso gida, kuma kaf tawagar a falona suka yada Zango Maama babba da yaranta biyu, Maama karama, Hana, Ramla da yake basu koma ba, tana nan har ta haihu. Hassana, Maryam, Khaleel, Affan, Baffa, Salman, Assidiq, Haidar Husaini. Sai Yusuf da ya tsaya soyayya, shi ma bai koma ba.
Misalin karfe takwas ina bangaren Zahra muna tattauna yadda bikin bude Islamiyar ya kasance Bashir ya shigo, ni da ita duk muka zuba mishi ido. Cikin alamun gajiya ya ce “Sosai na gaji ga shi gobe dole zan je Abuja”
“Ai aikinku kenan, Allah dai ya tsare” cewa ta, ya amsa da amin, kafin ya ce “Na shirya mana tafiya umra, mu dan je mu huta, kwanakin nan an sha hidima”
Zahra ta ce “Kai ma Sha Allah! Ai gaishe da miji na gari abun alfahari”
Murmushi ya yi kafin ya ce “Kun abun alfaharin ai, kun kwantar min da hankali, wannan yake ba ni damar aiwatar da ayyukana cikin kwanciyar hankali. Zuwa yanzu na kara gasgata magana fiyayyyen halitta, duniya gidan jin dadi ce, ma fi girman jin dadin duniya shi ne mace ta gari Alhamdulillah na same ku “
Zahra ta yi murmushin jin dadi kafin ta ce” Ai, miji shi ke gyara gidanshi, ka tsayar da adalci a tsakaninmu, ban taba tunanin zan kara rayuwar aure mai cike da farin ciki bayan wacce na yi ba. Musamman da ya kasance ina da abokiyar zama, amma Khadija ƴar’uwar ce, a zamana da ita ba ta yi min komai na cutarwa ba. Sai dai in yi mata addu’ar gamawa da duniya lafiya “
Kafin in yi magana Bashir ya ce” Khadija bango ce, ni kaina na sani, kuma ni zan bayar da labari, ta zama uwar kowa, zo mu je falonta ki gani “ya yi maganar yana jan hannun Zahra. Ni ma sai na bi bayan ina jin dadin yabon da suka yi min.
Bashir ya ja birki ba tare da ya shiga falon, saboda hayaniyar da yaran suke yi cikin Nishadi. Irin wadannan suke yi. Wai Auntynmu once said, aka tambayi Khaleel, zamanshi ya gyara yana fadin “Khaleel wai sau nawa zan fada ma ka daina daukar min abu idan na ajiye, ka yi auranka amma ban huta ba. Da zarar ka zo gidan nan sai na ga ban ga abu ba. Na ajiye fura a fridge kuma ban ganta ba. Na san kuma kai ne ka dauke ta. To ka tabbatar an jima ka zo min da fura ta”
Duk suka yi dariya aka juya kan Maama babba ta ce “Zo Maama, ina za, ki je? Zo dauki yarinyarki mai shegen kukan nan, kin san ban son damuwa”
Suka kuma yin dariya Ramla ta ce “Ke ga ki ba ke kaɗai ba, amma sai I ce za ki yi ta yin abin da an jima za ki zo ki hana kunnena sakat da wash-wash”
Affan ya amshe da “Affan tashi ka ba ni wuri, na ce ma ban da kudi, na san dai wannan ladabin kudi kake so, to tashi ba ni da su.”
Baffa ya karbe “Wai lafiya kake ta kwamo mana sammako Baffa? Jiya tun safe ka zo, yau ma ka zo tun safe. Hala fadan naku kuka yi, tun da ku ba ku zaman ƙalau, to abinci ne dai babu kason ka”
Cikin dariya Salman ma ya ce “Salman ka daina buyewa Maama, komai Idan ta ce sai ka ce za ka yi. To ka zauna ka zama mijin tace, ina ma amfanin irin wannan, tashi fita ba ni wuri ni ba na son kayan takaici, tun da a kanta za ka kare”
“Assidiq kana kwance har yanzu kamar mai, a haka Abbbanku ya dauki managern company guda ya ba ka? To tashi don ubanka, ma’aikatan kirki suna ta tafiya wurin aiki kai kana kwance”cewar Assidiq
Aka juyo kan Hassana” Hassana me ya kawo hijabina da takalmina dakinku, wato dai ni ban isa in ya kayana ni kadai ba, Sai dai mu raba su da ke. To miko min abu na, kuma ki tashi ki gyara wannan ɗakin naku.” ta kuma cewa idan kuma Ina waya sai ta ce” Ke tashi ba ni wuri, ki zo kina min uh, uh-uh, hmm, Sai ka ce dole, je ki can ku yi yaren kuramenku” duk suka saki dariya
Lokacin da aka tambayi Hana sai ta ki magana, ta kife kanta a kan cinya tana dariya, Maama karama ma ba ta ce komai ba, haka Maryam ma. Duk sai dariya kawai da suke yi. Haidar ya ce” Ah! Ah! Haidar waye ya yi ma wannan askin? Ba ka biya shi kudinshi ba ne duka, ya aske ma rabi ya bar rabi.To zo karbi kudi ka je ya karasa aske shi, ni ba na son wannan dan’iskan askin”
Hussain ma ya ce “Kai Husaini tashi ka tafi makaranta, kullum ne ba ka da lecture da safe, to yau ko ba ka da lecture din safe sai ka fita”
Suka kuma yin dariya, daidai lokacin na shiga falon, ina fadin “Sannunku na gode da gulma ta da kuke yi”
Suka kuma cika falon da hayaniya, nan na bar su da Zahra na haye sama, Bashir da yake biye da bayana, ya, rungo ni, daidai muna shiga daki, ya ce “Ki ce Alhamdulillah!”
Ina murmushi na ce “Alhamdulillah!!!”
Karshe