Skip to content
Part 1 of 50 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Godiya 

Godiya ga Ubangiji da ya yarda har ya bani ikon dawo da sabon littafi na Mai suna HAWAYE Ubangiji ka amfanar damu Darasin dake ciki ka yafe laifukan da zasu faru. Salati da Aminci ga uban dakina manzon da y zamo Rahama agare mu Allah ka linka salati da Aminci a gareshi da sahaban sa da ahalin gidan sa masu tsarki da masu bin hanyar sa da kyautatawa.

Sadaukarwa

Sadaukarwar littafin gabadaya ga haj Saliha Abubakar Abdullahi Zaria ce ita da ZURIA da masoyan ta Allah Ubangiji yayi Ruko da hannayen ki hajiya.

“Safiyya”? “Safiyya? Safiyya? Ta kwalawa Yar yarinyar Yar tata da shekarun ta duka hudu kira har sau uku amma bata jiyo motsin ta ba bare tajiyo ta rugo kamar yadda take yi idan tajiyo kiran.

Ta fito tana lekawa kusfa kusfa na gidan Amma bata jiyo motsin yarinyar ba. Ta karade ko ina na gidan amma batajiyo motsin ta ba

A Rikice ta koma daki ta jawo hijabinta ta doshi kofar gida inda sukayi taho mu gama da makociyar ta tana shigowa kamar wadda aka Koro don gyalen da ta yafo ma a jirge yake gefe Alamar ba a tsaya nutsuwar sakawa ba.

“Ina Safiyya take lubabatu?

“Nima ita nake nema shamsiyya basa tare da Aziza?

“Basa tare ganin ban gansu tare ba yasa na tambayi Azizar sai take fada min wai wani mai mota ne ya dauki safiyyar ya gudu da gudu.

“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un” lubabatu ta fada inda suka yi waje da gudu suna baza idanu ko zasu ga Safiyya Amma shiru.

“Can hanyar fa suka bi,” Aziza ta nuna da hannunta.

Kuka ya kubcewa lubabatu inda ta koma aguje gida ta jawo ta dokawa Mai gidan ta Kira

“Bello kazo gida babu lafiya wani ya dauke Safiyya ya gudu.

Ta fada tana Rushewa da kuka. Bata tsaya Jin abinda Bellon zai fada ba ta saki wayar ta fice aguje tana bin gidaje ko zata Dace da ganin yarta. Amma labarin guda ne babu Amo bare Labari

Bello ya karaso a rude aka shiga nema amma shiru, babu inda baije ba har caji office yaje da gidajen radio yaba da Cigiya. Yayi yawo har ya godewa Allah kafin ya dawo gida Yana neman ba Asin yadda Luba ta bar safiyyar ta fita.

Idanunta jajir taci kuka har ta Gode ta soma sanar dashi

“Ina daki Ina shara Aziza ta shigo nan suna wasa ban San ta fita ba sai da naji shirun su na fito Naga babu su.

“Ki dai ce kin shige daki kin shanya Baki kina bacci har ta fita Baki sani ba… “Wallahi ba bacci nake ba…

Kayi hakuri ka barni naji da abinda ya dameni ba wannan ne abinda ya kamata mu tauna a yanzu ba. Aziza tace min wai wani Mai mota ne ya dauki safiyyar inaji ajikina maganar aziza gaskiya ce idan aka dubi yadda Rayuwa ta koma.. ta fada da santin kuka.

Idan yace baiji batun ba yayi karya komai zai iya faruwa to Amma sakaci yasa babu yadda zasuyi sai sauraren kudurar Ubangiji.

Zaune yake Akan dakalin kofar gida ya dafe kanshi da hannu ya na rufe da idon shi tamkar Mai bacci Amma ba baccin yake ba tunanin halin da Safiyya ke ciki yake duk da duhun magaruba ga Kuma sauro na faman Yan yame shi da son ya yagi Rabon shi ajinin jikin shi Amma Bai damu ba inda zukatan shi ke ta gware da son canko mishi tilon Yar shi wadda ya shafe shekaru kafin ya sameta. Kuma bayan samun ta ma shekaru hudu babu labarin zuwan kanenta ko kanwar ta.

Kamar a mafarki ya Soma jiyo sautin kuka, kuka kuma me irin sautin safiyyar shi da sauri ya bude idon shi inda yaji kukan kamar Yana tun karo shi, zimbur ya Mike Yana waige waige kafin yaga fitowar Luba…

“Bello inajin sautin kukan Safiyya kusa dani…”

“Nima kamar haka nake ji…”

Hasken katuwar motar dake bayan gidan su ya Ankarar dasu can ne sautin ke fitowa

Aguje har suna rigr-rige suka nufi bayan gidan daidai da jefo yarinyar dake Rara kuka har muryar ta ta dashe…

Da gudu suka Isa gareta inda motar ta auna aguje. Luba ta kankame yarta Safiyya wadda taji jikinta zafi zau alamar zazzabi.

Bello ya daukota daga jikin Luba inda Luba ke haskawa Jin wani damshi na bin hannunta inda tayi arba da jini. Da sauri ta daga rigar Safiyya inda tayi arba da gaban yarinyar babu kyan gani…

“Na shiga uku na lalace Bello an kassara min rayuwar Safiyya…

Aguje Bello ya bi bayan motar dake kokarin bacewa acikin duhun daren yana falfala gudu tamkar zai tashi sama.

Sannu a hankali danjojin motar suka fara yiwa idanun shi nisa cikin sa a kuma ya hangi wani me mashi ya tsayar dashi yace yabi bayan motar dake kokarin bacewa ganin shi. Ai kuwa Dan acabar ya auna aguje dama Abu ga Dan arufta

“Bi shi a sannu don ba na son su gane ina biye dasu.

A can cikin unguwar Sardauna Estes suka luluka har zuwa wani katafaren gidan inda motar ta danna horn aka bude get din motar ta danna aguje, shima ya sauko mashin din aguje da nufin marawa motar baya Amma kafin ya karaso motar ta shige har an maido kyauren gate din an datse

Ya Soma dukan kyauren Amma shi da kanshi yasan kyauren ba me amsa Amon dukan bane ko har sashi baya huda shi bare hannun shi na kashi da tsoka.

Ya juyo ya hawo mashin din ya dawo gida da kudirin dawowa gobe, don Allah shine guda daya ba zai yarda da wannan cin zarafin ba.

Ya iso gida inda ya taras da gidan a kulle, ya kira wayar matar shi Luba take fada mishi gata Nan Asibiti Amma ance ba za a karbi Safiyya ba sai da yan sanda ta karashe da kuka mai cin rai.

Dole ya nufi Asibitin inda aka tabbatar mishi fyade aka yiwa yarinya Safiyya kuma dole hukuma ta shigo ciki. Shima ganin halin da Yar tashi Safiyya take ciki yasa shi zubar da Hawaye. Har yanzu kuka take me ban tausayi wanda duk me imani idan ya kalleta dole ya zubar mata da hawaye musamman idan akaji wai wani marar tsoron Allah ya haike mata yarinya Yar shekara Hudu.

Ya daga waya ya kira makocin shi hamis baban Aziza ya sanar dashi halin da ake ciki game da Safiyya wai likitoci sunce lallai sai hukuma ta shigo cikin case din don Allah ya yiwa kanin shi Aminu magana a taimaka musu. Hamis yace babu matsala yanzu ma zai sanar dashi. Ai kuwa sai gashi har an samu nasarar karbar Safiyya an bata agajin gaugawa inda Luba ke sharar HAWAYE Bello Kuma da kuka zuciya musamman da suka ji kukan na Safiyya yayi yawa har muryar ta ida dusashewa.

Sai misalin Sha daya na Dare aka fito da Safiyya wadda ke firgita tana kakkafewa. Idanunta kumbure saboda kuka. Bello da Luba suka rufu akanta suna zubar mata da HAWAYE saboda tausayi. Ta bude idonta da kyar akan Bello…

“Abba…ta furta da kyar. Sai Kuma tayi mishi nuni da gabanta…

“Abba nan…Ya daukota ya rungume yana tsiyayar HAWAYE…

“Allah yayi miki Sakayya Safiyya. Ubangiji ya dubi raunin ki ya Azurta ki da sauki da afuwa… Sai kuma ya rushe da kuka Yana Kara kankame ta inda Luba dama tunda ta tsinci Al amarin idonta bai kafe da HAWAYE ba…

Ta dubi Luba da take faman share HAWAYE…

“Mami Ruwa…

Ta jawo ledar fiyo wota ta soma bata ya fita ya siyo mata Maltina da Madara amma bata sha ba ruwa kawai take cewa a bata kafin wani wahalallen barci ya dauketa. Wanda tayi ta firgita inda Bello ke ta tofeta da ADDU A Yana HAWAYE har dare ya raba basu fargaba. Safiyya Kuma bata samu afuwa ko ta sisi ba har gari ya waye. Duk wani abu da suka san tana so an siyo amma bata karbi komai ba. Sai faman kiran sunan iyayenta take yi inda kuma likita ya dibata ya rubuta kalar maganin da za a siyo Bello ya fita siyo maganin, kafin ya dawo kuma Allah yayi ikon shi akan yarinya Safiyya…

Allah ka Kare ya’yan musulmi daga irin wannan sharrin na fyade don Alfarmar ANNABI da Alkur an.

Hawaye 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×