Skip to content
Part 10 of 48 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Kowa ya daukewa kowa wuta tsakanin haj wasila da Alh Aminu. Ita dai damuwar ta shigowar Halima gidan ta don tafi kowa sanin Alh Aminu yafita duk wata hauka da iya kulla tsiya . Son shi take tamkar tayi hauka shi yasa Bata son wata mace ta shigo da sunan kishiyar ta . Musamman da ta tabbatar Halima tafi ta komai da mace tun kahon ita mace ce.

Yayin da shi Kuma Alh Aminu yake shakkar tunkarar mahaifiyar Halima din don Yana ganin kamar itama ba zata bashi goyon bayan Auren Halimar ba tunda su mata da manyan su da yaran su tunanin su iri Daya ne musamman idan Abu ya hado da dangantakar Aure. Shiyasa Yake shakkar zuwa masanawar.

Sai dai kwanakin Nan ya Faye damuwa da Al amarin Halima komai yakeyi itace makale aranshi kamar dai yanzu da ya kirayi wasila da sunan Halima.

“Halima da Allah Miko min Ruwa a fridge din Nan…

Haj wasila ta juyo a tsorace tana duban shi Baki sake cikin mamaki…

“Duk acikin cin fuskata ne kake kirana da sunan Halima Aminu? Me kake jira ne Wai da ba zaka Auro Halimar Nan ba ko don ka bar Ni na huta da kiraye kirayen sunanta da kake cika min kunne a cikin talatainin Dare? Har an Kai jallin da sunana ma Yana bacewa a bakin ka sai Halima itace Akan harshen ka?.

“To na gaji da wannan wulakancin na rantse maka sai ka zabi Daya ko Ni ko Halima.
Ta fada tana nufo inda yake da nufin Kai hannu jikin shi.

“Kar ki kuskura ki karaso inda nake don zanyi Miki barin makauniya ne kawai. Ku duka ke da Halima Ina son ku bayan Halima ma Ina da sauran dama ta wasu Matan har Biyu. Idan Kuma kina son Jin lallai sai na zaba tsakanin ke da Halima to kunya kawai Zaki Sha gara ki zuba ido kawai kiyi kallo.

“Zan tafi na baka filin gidan ka idan ka Isa don Allah bayan Halima abiyo maka da Uwar ta da kakarta da dangin su ka Aura. Sai na tabbatar Kai din namiji ne.

Ta wuce a fusace ta shiga daki sai gata da yafe da gyale ta fice sai dai Jin tashin motar ta yayi .

Wannan abin da tayi ya bashi damar ziyartar Halima Kai da Kai wani lokacin ma yaje yace ta bashi abinci ko yayi Mata firar da Bata bukata har dai ta fito fill ta fada mishi.

“Zan Roke ka da girman Allah kayi hakuri da bibiyata Aminu Aure tsakanin mu ba zai yuwu ba na gode da Alherin ka gareni Amma don Allah ka yi hakuri da zuwa inda nake Kar kaja mutane so Dora zargi a kaina.

“Ba zan iya rabuwa dake ba Halima sai dai kiyi hakuri. Ni fa ban taba ganin inda masoyi ya Zama makiyi ba. Na fada Miki wallahi indai wasila matsalar mu to ta kusa barin gidana Akan ki idan Kuma har Amincin da kike fada gaskiya ne to ki Amince min kawai. Don yanzu Haka Wallahi wasila Bata gidana tana gidan su Kuma Ina me tabbatar Miki da Zan bita da takardar sakin Auren ta.

Wani dukan kirji da taji yasa ta tabbatar wannan mutumin bashi da ta ido.

“Na roke ka don girman Allah kar ka saki matarka akaina idan kuwa kayi haka to wallahi biyu babu zaka yi baka ga wasila Ni Kuma din ba samuwa zanyi ba.

“Zan maido ta ko don bakin da kika saaAmma fa ni din karfen kafan ki ne Halima.

“Haj kulu mahaifiyar Halima ta shigo gidan inda tazo duba sulaiman da yayi zazzabi inda suka hade da Alhaji Aminu.

Cikin mutunci ya gaishe da hajiyar har Yana Mata ALHERI me yawa ya Mike da Shirin ficewa Yana fadin sai na ji abinda Kika yanke Halima akaina Ni nafi kowa cancantar na Aure ki ko don na Rike yaran Nan .
Yayiwa hajiyar bankwana ya fice.

“Kai wannan mutum yasan mutunci Wallahi. Yanzu wannan Rayuwar irinshi kuwa suna da yawa? Dama tuni aka isheni da maganar kinki Aure kin ki Aure to ga lokaci Ubangiji ya kawo wani Abun inba Rabon ba yaushe akeyin shi? Ba ga murjan sani Nan ba haihuwar ta biyar agidan sani Ashe Rabo ne ya kashe tsohon mijin ta.

Wannan maganar ta hajiya tafi Ruwan zafi Kuna ga Halima. “Hajiya kin manta haj wasila ko? Ya za ayi na manta wasila matar da har Azumin bara sai da ta aika min da suga? To matar Alh Aminu ce fa saboda Allah Kuma ace na Auri mijinta? “Mtss hajiyar taja tsaki.

“Yo Ina Ruwan Allah da wata wasila? Idan fa akwai Rabo tsakanin ki da Aminu Halima sai kin Aure shi har ki haife.

“Zan Roki Allah ya kawo min wannan Rabon ta wani wurin ba dai daga gareshi ba. Hajiya ana barin halak ko don kunya.

Hajiyar tabita da kallon takaici ta kasa tankawa sai kwafa takeyi. “Yaya sulaiman din da jikin?

“Yaji sauki har ma ya tafi makaranta. To Allah ya Kara lafiya ta Mike ta wuce inda Halima ta Rako ta har kofar gida inda ta Gane hajiya Ranta ya baci. Amma dai zataje gidan ta kwatantawa hajiyar da Haka suka Rabu.

Satin haj wasila uku a gida Aminu baije ba Bai aika ba. Inda ita Kuma wasila ta kasa Zama lafiya don ko da ta taho tana tunanin hutawa sai ta Gane yanzu ne ma take cikin zullumi don bata San a wane matsayi Aminu ya ajeta ba me yuwa Kuma Yana can ya samu yadda yake so wata Kil ma Auren ya kusa tabbata.

Ganin dai ba zai biyo sawunta ba yasa yayan nata ya maido ta inda Alh Aminu yace dama bashi ya koreta ba ita ta taho to ana me ya biyo bayan ta? Karshe ma shi aka bawa hakuri ita Kuma aka yi Mata fada. Da Haka aka bar su tana sharar HAWAYE shi Kuma Yana gasa Mata magana.

“In mutum ya wuce Abu ai yasan ya wuce shi godai godai da mutum ya kwasa yaje gida Wai yayo yaji Bai San gidan ma an gaji dashi ba.

“Ka Rubuto min takardar ne kaga an kasa Dani ne? Dattako ne irin na mazan kwarai Amma yaushe saniya ke gazawa da kahonta?

Haka dai ake tafe zaman baya yiwa kowa Dadi. Inda Kuma Alh Aminu ya tsiri Kiran wayar Halima a tsakiyar Dare wani lokacin ma sai tayi nisa da barci zai saci jiki yayi wayar shi don kar haj wasila ta ji shi. Inda Kuma yau din ta farka ta jiyo shi Yana zuba Kalama kauna ga Halimar ba tare da ya San wasila ta farka ba.

“Wai masoyiya najiki shiru Baki kirani kin sanar Dani abinda Kika yanke ba. “Haba Halima ai mun Dade da Rufe wannan maganar wallahi kullum dake nake kwana dake nake tashi a Raina bana ganin kowace mace a idona sai ke don Haka ki daure ki bani dama ke da kanki Zaki tabbatar da Ina kaunar ki motar ki ma ta iso gobe Zan kawo Miki makullin.

Yayi saurin katse Kiran saboda ganin wasila ta tashi zaune tana kallon shi fuskar ta murtuk da son ayi Uwar watsi.

<< Hawaye 9Hawaye 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×