Skip to content
Part 11 of 32 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Ba ta zaci da gaske yake ya siyawa Halima mota ba sai da Husna tazo tana fadin Mami an kawo sabuwar mota Taki ce ko Yaya muhsin Daddy ya siyawa? Ta bi Husna da ido ta na laluben amsar da zata Bata.

Taja kwafa tare da Jan tsaki inda husna tabita da kallo. Me gadin gidan ne ya shigo Yana Miko Mata key din sabuwar motar Wai a ajewa Alh Aminu inji direban da ya kawo motar. Ta karbi key din tana juyawa cikin mamaki da takaici

Halima ce da motar milyoyin kudi? Halima ce da motar da ta linka Tata kudi?

Zuciyoyin ta sukayi ta kawo Mata shawarwari akan ta bankawa motar wuta. Amma dai ya shanye har ya dawo ta kawo mishi key din motar.

“Gashi dazu Sadi ya kawo ya ce a aje maka Ina fatan na motar Halimar ne ta karaso? Ya kirci kasumbar shi Yana murmushi yake Bata amsa. “Shine kuwa wasila kije ki duba ki gani tayi ko a canza ta?

“Ba sai na gani ba Allah yasa gidan ta ne. Ta fada tare da jefa mishi key din cikin kulewa da sikewa.

“To ai ke ya kamata ki Kai Mata key din motar don ke yafi kamata kiyi Mata albishir din don kuyi Dan kus kus din ku na Mata don nasan dai Dole ku kashe ku Rufe a tare Kinga sai ki Kara Rarrasar min ita akan Auren mu. Ya fada Yana Miko mata key din ta bishi da harara don ya gama kasheta da takaici. Ita kuwa wane suna Mata zasu kirata idan ta karbi makullin ta kaiwa Halima? Wadda ta rako mata duniya ko wadda kare ya dauke zuciyar ta.

“Ni bari na tashi na kai mata don na kula kamar kina bakin ciki da soyayyar nan tamu da Halima ashe duk karya ce da kike cewa aminiyar ki ce.

Ya mike ya fice don ya gama kasheta da maganar shi dole tabi shi da kallo har ya fice.

Ta Soma safa da marwa a falon. Matukar fa ba kwanji ta ware ba Akan Aminu da Halima to zasu nuna Mata itace karamar tantiriya. To Wai ita Halimar ta yarda da Auren Aminun? Ta yiwa kanta tambayar inda Kuma zuciyar ta ta sanar da ita yo me zai Hana tunda Halima Bata da miji a yanzu? Kuma wace macece zata ce bata son Aminun? In ba aso shi don kwarjinin shi ba to za a soshi don kudin shi. Haka dai tayi ta tufka da warwara har ta canko bakin zaren akan zuwa taja kunnen Halima Akan mijin ta matukar tana son kanta da Arziki.

Ya aje Mata key din Wai na motar da ya Bata kyauta ne. Ta dubeshi da wani fushi a fuskar ta Wai ita yake tunanin zai yaudara da mota.”Ina Jin kunyar ka Alh Aminu. Don Allah ka fita sabgata. Don Allah na Roke ka gidan Nan ma ka Daina zuwa wallahi bana son na yi maka abinda zai sa kayi nadamar sani na saboda Ina girmama ka saboda Amincin dake tsakanin ka da mu azu. Don bana ganin Amincin dake tsakani mu da matar ka don nasan idan ta samu labarin Nan ba zata tsaya ta binciki abin ba . To na kuma Rokon ka ka fita hanyata Wallahi bana muradin ka bana kamar inayi . Ina me tabbatar maka da idan Kai kadai kayi saura aduniya ba Zan Aure ka ba.

“Halima kenan nifa karfen kafar ki ne kowa zai tabbata akan bakan shi kenan Ni da ke. Ni dai sai Naga abinda ya turewa buxu nadi ke ma haka . To Bari mugani waye zai sallama. Ya Mike ya na aje Mata makullin ya fice tana binshi da kallo. Ta dauki makullin tana juyawa a hannun ta. Fitar shi Babu jimawa sai ga haj wasila ta shigo tamkar an wurgota.

Halima tayi yake Wai murmushi inda takeyiwa haj wasila marhabin lale sai dai ganin fuskar haj wasilar yasa ta gama hasaso abinda ke faruwa.

Haj wasila ta shiga karewa Halima kallo cikin kaskanci da son ta hango abinda ya Ruda alh Aminu akanta inda Halima taji ta muzanta da kallon da wasilar ke Mata.

“Halima kin San ko Yaya nake kallon ki? Kin mance ko wacece ke a gareni? Har kece ke kebewa da Aminu Kuna zancen Aure? Kin manta ko wacece Ni? To ki tsaya matsayin ki na wacce na Saba taimakawa idan Kuma kin shirya gugar jigida Dani to Bismillah ai nayi zaton ko mazan Duniya sun kare sai Aminu Kya kauda kanki. Amma idan kinajin kin shirya to Ni na Dade ashirye. Meye banyi Miki ba? Na taimakeki da zanen daurawa na gama fayyace Miki sirrina Babu abinda Baki sani ba Amma da Yake ke ba Yar halak bace kice babu mijin da kike so sai mijina.

“Ya isheki haka wasila karki wuce hurumin da Baki dashi a kaina. Idan da Ina son Auren mijin ki da Baki samu bakin fada min Haka ba.

“Don Allah Halima ki Auri Aminu kiga yadda ake iske matar Mai gida. ni ban fidda ran ma ke kika kashe mijinki don ki Auri Aminu ba. Ta fada tana ficewa daga gidan. Inda tabar Halima cikin zubar hawaye wannan maganar itace Abu mafi daci da zata ce ta hadiya bayan mutuwar Muazu.

Wai ta kashe mijinta sai kawai ta Rushe da kuka me tsuma Rai. Amma babu komai watan bakwai shi ke jawa shamuwa.

Alhaji Aminu kuwa Yana fitowa daga gidan Halima Kai tsaye ya tunkari masanawa gidan su Halimar wurin hajiyar ta. Ya kuwa yi sa’ar samun hajiyar ta Kuma karbeshi da karamci.

“Hajiya dama nazo ne in nemi wata Alfarma wurinku don Allah ku saka baki akan lamari na da Halima domin kuwa ta kafe akan wai ba tayi . Ni kuma ina ganin tamkar alhaki ne a gareni wurin auren ta darRike yaran mu azu. Na kada na Kuma Raya hajiya Amma Taki wata Kil idan kuka SA Baki ta aminta

Hajiya ta fusata kwarai da gaske don har ga Allah Aminu yayi Mata dari bisa dari Kuma irin shi takewa Halima kwadayi ko don itama ta Rika samun na shiga.

“Kayi hakuri Aminu Zan kirata inji dalilin ta na yin hakan. Tunda ka kawo maganar a gabana ai kamar anyi an gama ne ai ba wuce Auren tayi ba bare tace zaman Ya’ya zatayi ba. Kuma a wannan duniyar ana samun irinka kuwa me Rike Amanar Aminci? Kai Halima dai sakarai ce wallahi marar sanin makama

Ganin yadda hajiyar ta hau sama yasa yayi murmushi Yana Bata hakuri Wai tabi Halimar a sannu.

“Ai Halima da kake gani Aminu Allah yayi Mata kafiya da taurin Kai yadda kasan Zuma Haka take sai da wuta barni da ita tunda har yanzu batayi hankali ba.

Ya zubewa hajiyar kudi masu afki ya wuce Yana murmushi ita Kuma dama tamkar kaza da hatsi take indai kudine yanzu zata Rikice tamkar sarki.

Ya koma gida ya samu wasila ba tare da ya San Rashin mutuncin da taje har gida ta girbawa Halima.

Tun daga kofar gida Halima tajiyo sowar Husna tana ambaton sunanYaya Mai Kano

Sai gasu tare sun shigo sulaiman da Husna na dauke da manyan jukkuna.

<< Hawaye 10Hawaye 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×