Skip to content
Part 12 of 32 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Mai Kano ya zube Agaban Halima cikin girmama wa Yana gaishe ta.

Bakinta washe cikin farin ciki take amsawa inda kamshin mai kanon duk ya karade gidan. Duban shi take cikin kauna irin ta da da mahaifiya ganin zatin shi ya Kara fitowa ga haiba tamkar ya wuce shekarun shi girma na ban mamaki lallai Allah shi kadai yasan abinda ya ajewa mai kanon har ya ki karatu ya zabi kasuwanci.

Ya zuba Mata ido ganin yadda tayi rama.

“Mama me ke damunki kikayi irin wannan rama haka? Tayi murmushi har ga Allah alh Aminu ya zame Mata karfen kafar kamar yadda yace sai dai tana ganin Bai kamata ta boyewa Mai Kano ba don ko a cikin Ya’yan nata shi din yafi sauran damuwa da damuwar ta don Haka take Jin ba zata rufe mishi ba.

“Mai Kano ina cikin damuwa wadda har Ashe ta fito a fuska ta ban sani ba.

“Mama sanar dani damuwar ki in Sha Allah ba zata Fi karfina ba. Ya fada idon shi a fuskar Halima.
“Alh Aminu abokin mahaifin ku shine ya Zo min da maganar Yana son Aure na Wai duk Bai dubi Amincin dake tsakani na da matar shi ba. Kuma Ni har ga Allah baiyi min ba ba Kuma zaiyi min ba shine fa abin ya Soma damuwa ta tunda har ta Kai matar shi tana wanko kafar ta ta iskeni har gida taci min mutunci.

Hajiya kulu ta Raro sallama a fusace inda Halima da Mai Kano suka amsa suna Mata sannu da Zuwa.

Halima ta shiga daki ta daukowa hajiyar tabarma ta shinfida mata ta zauna Mai Kano na gaishe ta tana amsawa tana cin magani. Halima ta gaishe ta tana zuba mata zobo a Kofi ta Mika mata….

“Nasha Ruwa kafin nazo Nan. Halima tasan ba lafiya ba duk yadda hajiyar ke son zobon yau taki.

“Alhaji Aminu ya sameni jiya yake fada min wai Baki yarda da batun Auren shi ba Haka ne? Mai Kano ya tashi ya basu wuri ya shiga dakin Halima, amma kunnen shi na sauraren abinda suke taunawa.

“Haka ne hajiya gaskiya bana muradin shi don Allah ki fahimce Ni matar shi fa har ta fara zuwa gidan Nan tana zagina. Kuma ma Ni wallahi bana son shi hajiya. Hajiyar ta wurgo Mata harara.

“Anki a fahimce kin. Kuma da kike maganar matar shi tazo ta zageki zagi Yana Kari ne? Ai da Yana Kari da uwar barawo Bata kallu ba. Wace mace ce ake yiwa kishiya da yardar ta? Kuma ke baki da kunya Wallahi har kike bude Baki kice wai baki son Alhaji Aminu? To naji Baki son shi sai wa kike so? Ko ko kina nufin tunda mijinki ya mutu aure ma ya kare kenan? Zaman kai zaki yi kenan? Kamar tacewa Hajiyar to ai kema Hajiya da Baban mu ya mutu ai baki yi wani auren ba sai kuma ta tuna kowace ce uwar tace.

Halima ta dubi hajiyar cikin rarrashi da karya wuya. “Ki fahimce ni don Allah Hajiya a cire matar shi da take shamaki ko Babu ita hajiya Alhaji Aminu baiyi min ba ajira wani ya fito tunda so kuke nayi auren Hajiya wallahi zanyi ko don na faranta muku.

“In faranta min kike sonyi to ga Aminu nan ki Aure shi in ba so kike raina ya baci akanki ba.

“Ki yafe Ni hajiya bana fatan ko kadan na Zama silar damuwar ki abinda Baki Gane ba ba tsoron matar shi ne jigon kiyawa ta ba sai don wasu abubuwa na shi kanshi haj don Allah kiyi hakuri ki Kuma fahimce Ni.

Mai Kano ya fito ya sunkuya gaban hajiyar Yana zare idanu don haushin hajiyar ne fal a Ran shi na yadda ake kokarin nuna Mata tana kasa fahimta.

“Hajiya ! Ya Kira sunan da wani Amon murya. “Tunda Bata son shi ana Dole ne? “A matsayin da take yanzu musulunci ma ya Bata damar ta zabi mijin da take so. Idan Aure kike so tayi ki bar shi baba Aminun ki kawo Mata wani na San zata karba tunda tace Miki shi baba Aminun ne Bata muradi. Tatsss! Ta gaurawa Mai Kano Mari. “Ba Zan kawo Mata wanin ba marar kunya har Kaine ke kokarin nuna min uwar kace nice bare a cikin ku? “Tashi kaje Mai Kano kar ka kuma sako bakin ka acikin maganar nan cewar Halima.

Hajiya ta mike tana yafa gyalenta kafin ta juyo ta dubi Halima. “Idan kina son Zama lafiya Dani ki amsawa Alh Aminu idon kuwa kina Jin kinyi girman da Kika Fi karfi na Zan tsame hannu na akanki ko a hanya Kuma Kar ki taba tunanin kin sanni bare kiyi tunanin mun hada jini Kuma ko a LAHIRA hakan take babu Ni babu ke ! Da Haka hajiya ta fice tana kumfar Baki. Wani kuka ya kwacewa Halima mai ban tausayi taci gaba da Rerawa Mai Kano Yana Duke gabanta ya kasa cewa da ita ko uffan.

Sai da tayi kukan ta Mai yawa kafin tayi shiru”. Zan bi abinda hajiya take so ko don nasamu gamawa lafiya da ita. Zanyi aure da Alhaji Aminu ba don muradin raina ba sai don haka Hajiya take so. “Wallahi Mama ba Zaki Aure shi ba tunda Baki son shi ! “Ku yi hakuri Mai Kano Ina son mu Rabu lafiya da mahaifiya ta Wallahi na yarda zan aure shi Allah yasa haka shine ALHERI gareni.

Mai Kano yaja ya kafe akan uwar shi ba zatayi Auren da Bata so ba itama ta kafe da tunda haka hajiya take so ta aje Ra ayin ta ta dauki na mahaifiyar ta. A Ranar Mai Kano Bai Kara kwana guda a garin katsina ba Wai yayi fushi ya Bata kudin da ya kawo Mata da suturun da ya kawo musu yayi tafiyar shi Legos. Tayi murmushi

“Sarkin zuciya zaka huce ne. Yadda kake kishina nima haka nake kishin tawa tsohuwar. Kwanaki da yawa Alhaji Aminu Bai waiwaye ta ba har tayi fatan ace yayi zuciya ya bar maganar. Sai gashi ya iso da tarin siyayyar da ya Saba ko da yaushe.

“Kiyi hakuri dani Halima Ni din karfen kafan ki ne kwana Biyu nayi fama da zazzabin begen ki ne shi yasa Kika jini shiru. Halima nayi zaton masoyi baya Zama makiyi duk Wanda ya furta maka kalmar so ya gama maka komai. Ban San irin aibun da ke gareni ba da har nayi Rashin sa a Kika kasa karba ta. Ni dai na San Babu abinda mu azu yafi Ni sai Babu.

Wani matsiyacin fushi ya bayyana a fuskar ta. “Abubuwan da mu azu yafi ka suna da yawa. Ko ba komai shine mutum Daya Tak da yayi nasarar budewa da Rufewa na zuciya ta abinda bakayi nasarar samu ba. Kuma Zan gargadeka da in har ba ADDU A zakayiwa mu azu ba to sunan shi ya fita a Bakin ka. Kuma Kar ka Kuma tunkarar mahaifiya ta da wata magana don mu azu ka sani bani da ahalina ba. Tun da mahaifiya ta kawo Ni Duniya ko Allah wadai Bata taba ce min ba Amma a dalilin ka Ranta na neman baci a kaina to Babu Ruwan ka da ahalina.

“Ai kuwa Halima ahalinki ai na wane tunda mun kusa zama daya.

“Har abada ahalina ahalina ne naka kuma naka ne don haka kayi nasara akaina sai kaje ka samu Hajiya ku tsara duk yadda zaku yi . Ni kam ba zan daina rokon Ubangiji ya yi min zabin ALHERI ba idan har ba zaka zamo min ALHERI ba Ubangiji ya kassara lamarin nan…

“Ba Amin ba Halima in Sha Allah sai kin haifo min Yan beautifull baby masu kama da ke na kuma godewa Hajiya da tayi min wannan kokarin in Sha Allah bana da ita cikin mahajjata don haka daga nan ma wurin Hajiya zan wuce mu tsara komai tunda ke amarya kin fara shan kamshin Amarci. Ya fada da murmushi a fuskar shi ya fice ya barta da dukan kirji.

Kai tsaye kuwa ya zarce gidan hajiya kulu mahaifiyar Halima inda Suma tsayar da Rana kwana talatin wato wata Daya. Ya kuwa zube Mata kudi tamkar yayi a bola ya kuma yi Mata albishir din kujerar makka bana inda hajiyar ta gigice ta kuma Rude har takejin tamkar kwanakin sunyi yawa amma dai aka bar su wata guda.

Kamar da wasa haj wasila ta tsinci zancen a can gari wurin shanun yawo Wai Auren Aminu da Halima kwana talatin Rak abinda ya firgitata har tayi nufin zuwa gidan Halima suyi mutuwar kasko. Ai kuwa mota a sukwane ta fafareta tamkar zata tashi sama ta Isa gidan Halima tana cin uban burki har tana tada kura.

<< Hawaye 11Hawaye 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×