Skip to content
Part 13 of 32 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Karar cin tayar da Hajiya Wasila tayi shi ya sanya Halima juyowa ta yiwa kofar gidan zuru da ido don taji ajikin ta nan za a shigo.

Hajiya Wasila ta shigo tana huci gyalenta ma a hannu ta ruko shi tsabar musifa na cinta. Babu ko sallama ta shigo Halima ta bita da kallo

“Ashe kuwa da gaske kike Halima? Don Allah sanar dani gaskiya na jiyo wata magana me kama da Almara wai Aure ke da Aminu.

“Nima fa kamar hakan na jiyo, Hajiya wasila ta kyalkyale da dariyar rainin wayo tana tafa hannuwa.

“Allah na dawo inji kishiyar Mai yaji tace Annabi Kya koma.? Wai Halima a ido biyu hakan ke tabbata Koko mafarkin sanyi? Da wace kamar kike kokarin Auren mijina? Kin mance ko wacece ke na tuna Miki? To tun wuri ki fidda Aminu daga zuciyar ki don na rantse Miki nawa ne Ni Daya idan kuwa kince A a to zakice na fada Miki wallahi Babu wani sauran gurbi da wata mace zata shigo gidan Aminu da sunan matar Aure. Bare ke da na bawa zanin daurawa na gama kwance Miki jakar sirrina ko Zan karbi wata mace da sunan kishiya to ba dai ke ba sai macen da ta Isa Wallahi ke Baki Kai ba ba Kuma Zaki Kai ba.

“Kamar kin gama makara Wasila don Ni na Raina matar da mijin ta ke kokarin yi mata kishiya alhalin da kuruciyar ta irinki. Ba nice ya kamata na Fadi na kai mace ba mijinki ne ya kuma fada sai kuma me? Wai duk wannan hargagin da kike don na bar miki mijin ki ko kuwa hauka? Wasila sai na Auri mijin ki ko don inga iyakar ki in da nice ke wallahi da na hakura tunda naci yayi na har miji ya nemi wata don na tabbata yadda sakaran mijinki ya gaji dake akan auren Nan zai iya sallama ki.

“Aminun kike cewa sakarai? “Karshe ma kuwa in kinje ki kara jaddada mishi daga gareni don ni ba tsiyar komai yake a gareni ba. Ni ba kaza bace bare idona ya rufe akan abin duniya kamar ke. “Naci ne kawai da son na tura Miki haushi zai sa na Aure shi da kinji yadda nake kallon Aminu da baki wahalar da kanki wurin zuwa kina gwama numfashi ba don mijin ki baiyi min ba wallahi bai yi min ba zan aure shi ne don naga irin isar dake gareki wurin shi.

Wasila ta kyalkyale da dariyar takaici tana fadin, “za kuwa kiga irin isar dake gareni Allah Yasa gidan ki ne ni da ke shege ka fasa. Ta fice daga gidan Halima na binta da kallo kafin taji Hawaye na bin idonta.


Har ga Allah bata iya fada ba. Amma tayi mamakin yadda ta gasawa Wasila maganganun nan.

Wasila ta koma gida tana saka yadda zata bullowa lamarin don gaskiya bata jin zata yarda Halima ta shigo mata a matsayin kishiya sai dai a san yadda za ayi

Ga mamakin ta sai taga Alh Aminu ya soma gyaran gidan dama part uku ne gidan nashi sai taga ana gyaran part din da suke da kuma daya daga sauran part biyun. “Ashe dai da gaske kake sabon Ango? Ta fadawa Alh Aminu cikin gatse?

“Au wai kin zaci abun a mafarkin ki zai faru? Soma lissafi nan da kwana Ashirin da takwas zaki jiyo guda.

“Kai haba dai guda ? Sai dai ko najiyo shiru ta bani labari don kasan an dade ana ruwa kasa na hadiya.

“To hakan Hajjaju makkatul mukarramina, Ya fada Yana shekewa da Dariya. Wayar shi tayi Kara ya fito da ita inda yayi arba da sunan Halima na yawo Wanda ya sakawa Darling..

“Yar halak Taki ambato kingan ta nan amarya sha guda itace ke kirana ya nunawa Hajiya Wasila wayar kafin ya dauka yana saka handsfree muryar ta ta fito sosai yana fadin, “Allah ya taimakeki da girman kujerar ki ranki ya dade fatan kina lafiya? “Aminu ina fatan matarka ta baka sakon da na bata ta baka? Ya dubi Wasila yake tambayar ta da ido .

“Haba darling dina yanzu har tsakanin mu sai kin sako min kawar ki saboda Allah don dai ki nuna min ita din kawar kice?

“A dane mukayi kawance da matar ka Amma yanzu kallon hanjin juna muke . Ko a da can din nayi kawance ne da ita saboda na kyautata mata zato ban zaci kwakwalwar kifi gareta ba . Sai yanzu da aka yi yunwa sai kuma na gane babu abinda kwanyar ta ta sani saboda ta dankare da tiren talla ba ta sha inuwar silin ba. Haka kuma bata je islamiya ba . To ka fada mata ta fita hanya ta ni ba jaka bace irin ta. Kuma ka sanar da ita yadda auren mu ya faro don tazo har gida tana min hauka. To ka gaya mata ba wai dadani kayi da kasa ba bare ka tuma naci ne yasa ka kasa kauda idon ka akaina tunda ai ban boye maka yadda nake kallon ka ba. To idan ka isa ne zaka yi mata magana ta fita hanya ta . Ka kuma fada mata idan ta kuma dawowa tayi min irin abinda tayi yau zan dauki mataki ne kawai don ina kallon ta a matsayin Yaya babba…

“Kiyi hakuri darling dina don Allah wallahi ban san tazo tayi miki wannan abin ba. Kuma zaki yarda dani cewa na isa da gidana.

“Wannan matsalar kuce Aminu da zaka sauwake min ka kuma saukakawa matar ka haukan ta da take kokarin tashin aljanu da zai fi mana sauki.

“Ai ba zan iya bane Darling ko don baki san yadda sauran kwanakin nan nake kallon su da nisa ba? Kullum sai nayi mafarkin ki.

“To ka sanar da ita yadda kake ji na kawai watakil ta sauwake wa kanta.

“Ai tana sane ba sai na maimaita mata ke dai taimakan ni kar ki bar ranki yana baci amarya da farin ciki aka santa. Ta datse wayar ta barshi da aikwa wasila wata matsiyaciyar harara. “Kina tunanin abun nan na wasane Wasila? To ki hutar da kanki Akan Halima idan kuwa kince A a to Zan Baki hutu Wallahi Wanda zai hanaki saka min ido yayin Angonci na tunda kin San dai ko gida kikaje Ni ake bawa hakuri saboda sun San Ni kadai ne me iyawa ki fita idona ki Kuma fita idon Halima ta.

Takaici ya hana Hajiya Wasila tankawa don ba karamar mutuwa kalaman Halima suka saka mata ba don da ace a gabanta ne ta fada mata haka da sai dai a kwashi gawar wata daga cikin su don kalaman Alhaji Aminu basu dameta ba don ta san tsiyar da take kulla musu shiyasa tayi kamar bata San yanayi ba. Inda ya shiga sakin maganganu wayar shi tayi kara ya figo ta a fusace yayi kuma arba da lambar lauje. Ya daga yana huci, “Ya aka yi ne uban makirci ?

“Wane Bala’i ne kake kokarin ballowa Aminu? Laujen ya tambaye shi. “Da akayi me Kuma?
Ya tari Laujen.

“Wacece kake kokarin Aure Aminu? To maza maza kazo tun baka ballo bahar maliya ba.

Lauje ya katse wayar ya barshi da fadin hello ! hello !!!

Ya dubi wayar tamkar zai hango Laujen ta ciki, dole ya mike da sauri ya suri makullin mota ya fice Hajiya Wasila na mishi rakiya da wani banzan kallo ya shiga mota tamkar zai tashi sama ya fice ya nufi hanyar fita gari zuwa gidan Lauje.

<< Hawaye 12Hawaye 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×