Gama sallar walha da tayi ta bude Alkur'ani tana karatu inda Husna ke markade sulaiman na wanke wanke shiyasa Basu ji kugin motar shi ba sai da ya shigo daidai da Husna ta gama markaden sukayi mishi sannu da Zuwa . Ya fito da fakitin ibon sweet ya Mika musu kowa leda guda guda kafin ya tambayi sulaiman ina mamar su?
"Karatu take Amma bari na sanar Mata taron ya nufi dakin Yana fada Mata inda ta Rufe Al kur'anin ta fito cikin hijabin sallar ta.
Ya zare gilashin idon shi yana jefa mata idanuwa
Suka yi ido hudu. . .