Skip to content
Part 15 of 50 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Gama sallar walha da tayi ta bude Alkur’ani tana karatu inda Husna ke markade sulaiman na wanke wanke shiyasa Basu ji kugin motar shi ba sai da ya shigo daidai da Husna ta gama markaden sukayi mishi sannu da Zuwa . Ya fito da fakitin ibon sweet ya Mika musu kowa leda guda guda kafin ya tambayi sulaiman ina mamar su?

“Karatu take Amma bari na sanar Mata taron ya nufi dakin Yana fada Mata inda ta Rufe Al kur’anin ta fito cikin hijabin sallar ta.

Ya zare gilashin idon shi yana jefa mata idanuwa

Suka yi ido hudu inda taji wata matsiyaciyar faduwar gaba tayi maza ta furta.

“A uzu bi kalimatullahi tamat min sharri ma khalak,”

Ta aje mishi kujera tana gaishe shi. “Fatan kuna lafiya? “Lafiya Lau alhamdulillah.

“To madallah ya wurin su hajiya? Suna tafiya ina su Muhsin da Amal? Kowa fa lafiya. “Dama wata Alfarma nazo nema wurin ki Allah yasa zakiyi min ita?

Ta dube shi inda gabanta ya kuma faduwa Amma ta dora Adduar har ma tana bin ta da Hasbunallahu wa Ni imal wakeel…

“Kinyi shiru Halima? “Ina jinka Allah yasa wadda zan iya ce

“Tafiya ce ta kamani kan harkar fata ta shine nake son kiyi min rakiya don zan dauki lokaci kusan three months zanyi shine nake so mu tafi tare…

“Idan an daura Auren kenan ko kuwa babu igiyar aure zan bika Ina ne ma inda zanyi maka rakiyar?

“Yardar ki kawai nake nema Halima koma ina ne ai ba zan siyar dake ba ko?

“Da siyar dani din kayi ba zanga bakin ka ba irin ka kalleni kace na bika wata kasa alhalin ga matar ka wadda tafi kowa cancantar hakan. To ko Auren mu aka daura ai ba zan bika ba indai ya zamo akwai shiga hakkin matar ka.”

“In don ta Wsila ne, Halima kar kiji komai babu inda banje da ita ba indai fita waje ne har ta gaji don haka zanje na samu Hajiya na nemi izinin ta.

“Babu ruwan ka da Hajiya ta kuma ban aike ka ba. Idan kallon da kake min kenan to ba Haka Nan nake ba. Ai nayi zaton akwai kunya ma ka kalleni kace Zan bika wani wuri har tsayin wata uku Kuma ba Aure aka daura Mana ba. Saboda ka Raina mu Ni da Hajiyar shine har zaka je ka sameta ka fada mata haka?

“Aminu na dade da ji ajikina ba zaka zamo min alheri ba. To na Roke ka da ka janye don Allah daga maganar Aure na tunda kallon da kake min ba na mutumci bane kana kallo na a wata me zaman kanta? To Nagode da hakan ta fada Hawaye na biyo gurbin idonta.

“Ubangiji gara da ka kauda Muazu ba iga wannan kayan takaicin ba.

“Halima ko na bar Auren ki ai ba zaki cire min begen ki ba inba kusanta ta kika yi ba.

“Zan Baki duk abinda kike bukata Ni dai bukata ta kiyi min Rakiyar Nan tunda kin dai matsa da na bar batun Auren ki to na Bari Amma ki kusance Ni nayi Miki alkawarin komai kike so Zan Baki shi.

“Aminu tashi kaje Allah ya Isa tsakani na dakai Wallahi idan baka bar gidan Nan ba yanzu ne zakayi nadamar sani na a Rayuwar ka.

Ya Mike don ganin yadda ta Mike a fusace. Ya kusa fita ne ya juyo Yake fada mata zai dawo yaji shawarar da ta yanke.

Kuka take kamar Ranta zai fita. “Allah Kaine Allah Ubangiji ka bani karfin gwiwar da Zan jure zafin kaddarar ka. Allah kayi min Sakayya Akan wannan mutum da baya nufina da ALHERI. Allah ka yi min katangar karfe tsakani na dashi. Tayi kukan ta har ta godewa Ubangiji.

Husna da Sulaiman da suka shigo suka ganta tana kuka suka zagaye ta suna faman tambayar ta dole ta shara musu karyar cewa kanta ke mata ciwo.

Washegari sai ga Mai Kano wanda yazo ya isketa kwance riris ciwon damuwa ya kayar da ita.

Ya zube Agaban ta Yana Kare Mata kallo bayan Ramar da ya barta da ita ta Kara wata akai yaji tausayin ta matuka Gaya. “Mama maganar Nan ce dai ta Baba Aminu? Ta Mike zaune tana kwarara jikinta Wai don kar ta saka shi damuwa.

“Wallahi itace Mai Kano abubuwa sunyi min zafi . Lamarin gaba kura ce baya siyaki.

“Mama ki shirya kawai mu wuce can akwai gidan da na Kama zai ishemu muyi Rayuwar mu.

“Mai Kano ba zai yuwu ba saboda hajiya zata ga na watsar da maganar ta duk da mutumin Nan Yana min wani kallo tamkar wata magajiyar karuwai har yake bude Baki ya fada min wata magana ta banza wannan. Abu ya kona min Rai. Sai HAWAYE. “Mama ki rabu da Hajiya tunda na kula Hajiya ba fahimta zata yi ba.

“Ka yi hakuri Mai Kano akwai lokacin da zaka yi hakan na kuma bika. Amma ba yanzu ba bari mu wanye da Hajiya lafiya.

Kwana biyu Hajiya ta zo take tambayar Halima wai me ke faruwa tsakanin ta da Alhaji Aminu taji shi shiru?

“Hajiya mutumin nan fa mayaudari ne wallahi don Allah ku kyale shi tunda har an kai yana duban idona yana karanto min maganar banza.

“Kar ki yi mishi sharri Halima. Ke dince ban sani ba? Ai dama kin nuna baki yin mutumin nan to kar kiyi mishi sharri tunda kinyi kutu kutun da kika kori mutumin nan nima na gama saka baki na akan kiyi Aure.

“Hajiya ki gafarce Ni wallahi banyi mishi sharri ba sai dan ni kaina ya shayar dani mamaki har nayi fatan ace akan kunnenki ya furta min hakan.

“Ai ko bai furta akan kunne na ba kin kala mishi sharri akan kunne na shikenan kuma idan ya zo, zan mayar mishi da sadakin shi dama makullin motar da kika kawo min na bashi yana hannu na duka zan hada mishi kayan shi kinga har motar kinga ta leko ta koma…

“Wai Hajiya dama ba a mayar mishi da motar ba?

“Ai yanzu ya zama dole a mayar mishi da kayan shi tunda abin har ya Kai da kala sharri. Hajiya ya Mike ta fice a fusace. Halima ta bita da kallo.

Washegari Mai Kano yayi shirin komawa inda dama kudin hidimar karatu ne da Mubarak ya fada mishi suna bukata Kuma suna Jin nauyin tambayar Halima shine yayi musu ba zata ya biyo ta Zaria ya Basu kafin ya wuto katsina.

Halima tayi ta saka mishi Albarka.

“Mama da kinji abubuwa zasu dameki don Allah ki kirani nazo mu tafi mu bar garin nan, shiyasa fa Ubangiji yayi Duniya da fadi in kaji matsatsi ka matsa.

Ita da kanta Halima Tana bukatar matsawa daga garin katsina ko don tayi nesa da alh Aminu to amma ba zai yuwu ta tafi a yanzu ba hajiya na kallon abinda ba shine ba .

Da haka Mai Kano ya koma Legos inda Kuma ta shiga fargabar Alhaji Aminu don tunda ya fara nuna mata bakin halin shi akan yadda yake so da ita ta shiga fargabar komai zai iya faruwa. Bata tsinke da lamarin ba sai da Alhaji Aminu ya shiga zarya gidan yana fada mata shi din karfen kafan ta ne kuma komai zaiyi mata idan har ta yarda da abinda yake so zai daga martabar ta motoci da gwalagwalai. Kai babbar mace ma Yake da burin maida ita.

To Bari muji daga Halimar ko zata yarda ta zamo babbar macen ko don Hajiya ta yarda bata da laifi?

<< Hawaye 14Hawaye 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×