Skip to content
Part 17 of 47 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Suka dubi juna shi da Halima. Shi Yana mata kallon mayata da kwalama yayin da ita kuma take mishi kallon makunshin cuta. Kwalba uwar Yan sharri ko kin fashe da sauran sharri fitilar zalunci ko Babu Mai kina Kai safe ! Halima ta Raya a Ranta

Yayin da Hajiya ke ta Ina ta ka saka da shi tayi ta kawo mishi abubuwa bayan ta dire mishi ruwa tayi ta kawo mishi abubuwan tabawa.

Ruwa kawai ya Sha ya dubi hajiya Yana fadin Ashe Halima Tana gida? Hajiya tace “Uhum Nan tazo kusan sati Hudu kenan. “Hajiya Ni ban San abinda nayiwa Halima ba ta uzzura min d lallai sai na hakura da Auren ta har dai na yarda nayi Mata yadda take so hajiya ko don ta samu Zama lafiya.

Hajiya ta kwadawa Halima harara yayin da Halima ke mamakin makircin Alh Aminu.

“Amma Ni ai Bata fada min Haka ba sai ta fada min wani zancen banza? To ai shikenan tunda Haka ta zaba. Hajiya ta fada a fusace kafin ta tashi ta SHIGA daki ta fito da kudaden tare da makullin motar tana zubewa a gaban shi.

“In babu Kira ai Babu abinda zaici gawayi Kuma idan amarya Bata hau doki ba Babu Mai aza Mata Kaya. “Ga kudin ka da makullin motar ka da Ina da wata Yar da zanyi maka huce haushi Aminu da nayi maka ko don Halima ta Gane ko a cikin tandu akwai gabas ba Kuma ita kadai ce mace ba wasu Matan ma in ta shiga cikin su ko kyallin ta ba za a gano ba.

Ya Soma kada kanshi Alamar A a. “Ba Zan karbi komai ba hajiya duk abinda na bayar na bashi baya har abada da ace ana bude zuciya da na budewa Halima taga irin yadda zuciya ta ta karbeta ta Bata mazauni. Don Haka son Halima yafi karfin komai agareni da abinda na mallaka don Haka hajiya a bawa Halima motar har kudin na bar Mata da kunya ma na karba…….

“Bana bukatar komai daga gareka Aminu. Wanda na karba ma a baya Rashin sani ne yasa na karba Amma yanzu da akayi walkiya ta haska bana bukata.cewar Halima da take mace cikin mamakin Alh Aminu.

Hajiya ta bita da kallon takaici . Shi Kuma Jin abinda Halima ta fada yasa ya dubi hajiya.

“Hajiya na bar Miki komai tunda Bata bukata. Ki dauki kudin kiyi amfani dasu motar Kuma a Rika Kai ki unguwa. Ai kuwa sai ga hajiya na ta sheko godiya ya Mike Yana yiwa hajiyar bankwana inda yake jifar Halima da murmushin kinzo hannu.

Hajiya ta Rako shi har wurin motar shi ya tafi Yana barin hajiya da barin jiki. Ta shigo tana saukewa Halima Lodi. “Ni dama tuni na gano yaron sharri kawai kike son yi mishi. Tuni dama Kika nuna adawar ki da Auren shi har naso na yarda da abinda Kika fada to sai ki gaji ki hutas yace ya hakura dake tunda ba autar Mata bace ke. Aure kuwa kada Allah ya Baki ikon yin shi har a busa kahon tashin alkiyama . Tunda Kuma kinyi sanadin da ya fasa Auren ki ai sai ki tattare yanaki yanaki ki koma gidan mu azu kici gaba da zaman Ya’ya da Sana a.

Duk yadda taso ta fahimtar da hajiyar Amma d gangan hajiya Taki fahimtar ta Dole ta hada kayan ta Dana su Husna tazo ta fice bayan ta Roki hajiyar da ta yafe Mata bacin Ran da ta saka ta.

“Na yafe dama ke nake hangowa yadda gaban ki zata gyaru ba Ni ba. Da Haka dai Halima ta fice zuwa gida cikin matsananciyar damuwa.

A Ranar da ta koma ne Mai Kano ya kirata Jin muryar ta ya Gane tana cikin damuwa.

“Mama kina cikin damuwa jiki na ya na Gaya min hakan.

“Kar ka damu Mai Kano ba sosai ba maganar Nan dai ce ta Alh Aminu yayi min ba zata ne kawai shine damuwata.

“Mama ki Amince min kawai nazo mu taho Nan ko hankalin ki zai kwanta. “Kar ka damu Mai Kano komai zai wuce in Allah ya yarda.

Haka suka Rabu Yana damuwa da damuwar mahaifiyar shi. Ta kimtsa gidan kasancewar ya Jima babu kimtsi. Har zuwa dare inda Bata huta da gyare gyare ba .

Sulaiman da Husna sunyi barci bayan ta gama sallar Daren da takeyi duk dare kasancewar Babu wutar nepa yasa ta kunna fitilar wayar ta tana Jan carbi tana Kai kukan ta ga Ubangiji kawai sai ganin mutane tayi akanta.

Ta firgita matuka kasancewar ta kulle gidan Kuma batajiyo motsin shigowa ba.

Kafin tace komai taji tsinin bindiga a goshin ta tare da kashegin tana yin motsi ko magana zata bakunci LAHIRA. Dole ta hadiye ta bisu da idanu kafin Daya daga cikin su ya manna Mata wani Abu Mai Kama da gum a Baki tare da Rufe fuskar ta da Bakin yanki.

Shikenan ! Sai dai tsintar kanta tayi a mota ana ta sharara gudu da ita. Babu abinda take face ambaton sunan Ubangiji da neman agajin sa . Yayin da agefe guda Kuma take tausayin yaranta husna da sulaiman da aka baro a gida su kadai. Suma ta Roki Ubangiji ya SHIGA lamarin su Kar ya barsu da iyawar su.

Tafiya Mai nisan gaske kafin taji ana Danna horn har aka bude gate motar da Danna aciki
Aka bude inda take a baya aka fito da ita tare da yaye Mata Bakin yankin fuskar ta inda tayi arba da wani gida me shimfida da daula tamkar a kasar waje inda aka Bata umurnin bin wata siriryar hanya ta Kuma bi cikin tsoro da sallamawa

Sannu a hankali take bin inda aka nuna Mata har zuwa wata kofa da sai da ta SHIGA ta Gane falone Mai girman gaske haske tarwai a ko ina tamkar Rana.

Babu abinda zuciyar ta keyi face duka tamkar zata faso kirjin ta Tayo waje. Idonta ya sauka kan mutumin dake zaune Akan kujera kafar shi daya Kan Daya.

Tamkar nunmfashin ta zai dauke saboda ganin Alhaji Aminu yana Mata murmushin barka da zuwa.

<< Hawaye 16Hawaye 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×