"Su kuwa wadannan fa? Haj Wasila ta tambaye shi tana duban Husna da sulaiman a lalace.
"Ai kin shaida su ko? Shima ya tambaye ta. "Kamar Ya'yan wata ke ma da suna? Yayi murmushi Yana fadin"Bari na tuna Miki idan mantawa kikayi. Ya 'yan marigayi mu azu ne kamar baici ace kin manta su ba tunda suna Zuwa.
"Naji yanzu me akayi da ka kwaso min su suna zuba min ido tamkar iyalan kamtaka? ( Tana nufin mayu)
"An nemi mahaifiyar su ne an Rasa shine na dauko su na kawo Nan.
Ta kyalkyale da Dariya har tana tafa. . .