Skip to content
Part 19 of 48 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

“Su kuwa wadannan fa? Haj Wasila ta tambaye shi tana duban Husna da sulaiman a lalace.

“Ai kin shaida su ko? Shima ya tambaye ta. “Kamar Ya’yan wata ke ma da suna? Yayi murmushi Yana fadin
“Bari na tuna Miki idan mantawa kikayi. Ya ‘yan marigayi mu azu ne kamar baici ace kin manta su ba tunda suna Zuwa.

“Naji yanzu me akayi da ka kwaso min su suna zuba min ido tamkar iyalan kamtaka? ( Tana nufin mayu)

“An nemi mahaifiyar su ne an Rasa shine na dauko su na kawo Nan.

Ta kyalkyale da Dariya har tana tafa hannu

“Yo ya akayi Kuma a ka haihu a maratayi? Ina zancen Amrcin?

Ya hade fuska Yana kallon ta. “Kar ki kawo min zancen banza anan wasila. Ta kame bakinta da hannunta ta Rike Wai tayi shiru Amma Kuma Dariya take sai dai Bata Bari sautin ya fito ba.

Alh Aminu ya Mike Yana kwalawa Mai Aikin Kira

“Asabe? Ina asabe take? Ta taho da sauri tana fadin gani Alh

“Yauwa don Allah Asabe ga Amana Zan Baki ta yaran Nan ki kula min da su cin su da Shan su har zuwa tsaftar jikin su Zan fita an jima Zan kawo musu Kaya yanzu kuje ki Basu abinci. Asabe tace ta karbi Amana don haka ta wuce da yaran

Kaya masu kyau da tsada ya siyo musu hatta da sabulun wankan su me tsada ne ga cima me kyau tuni yaran suka saki jikin su ganin su muhsin da Amal suna jansu a jiki.

Muhsin ya kammala karatun shi har Yana Shirin wucewa bautar kasa a edo. Yayin da Amal take a Jami ar ummaru Musa yar Adua yayin da Husna ke kokari zana jarabawar waec inda sulaiman ke aji Daya a secondary

Basu da matsalar komai sai dai haj wasila Bata shiga sabgar su bare ta sakar musu fuska shiyasa suke shayin ta. Idan Rashin mutuncin ta ya motsa tayi ta an taka musu Ashar sai dai hakan tana faruwa ne bayan idon Alh Aminu.

Randa tayi kuskuren zagin sulaiman akan idon shi taji bama bamai don sai da ya zageta tas !
Ta dubeshi tana mamakin zagin da yayi Mata.

“Duk da Rashin Auro uwar su da bakayi ba ban tsira daga kaidin Halima ba Ni nasan dama tunda ka jajibo yaran Nan nasan kishin uwar su ne zamuyi Ni da su.

“Inko Kika ce dasu yaran Nan Zakiyi kishi na Rantse Miki da wahala kawai Zakiyi don sune ke da nasara akanki

Jinin muhsin da Husna yayi bala in hadawa don in har ya dawo to Husna ce abokiyar firar shi
Yayin da Amal ma suke dasawa da Husna don yarinyar akwai wayo da hikima Yayin da sulaiman ya kasance miskili Wai kafi mahaukaci ban haushi magana ma Bata dameshi ba shiyasa Bai Faye hayaniya ba

Tuni muhsin ya wuce jihar Edo wurin bautar kasar shi inda Kuma Husna ta kammala scondry school har aka sama Mata gurbin karatu a ummaru Musa yar Adua suke tafiya tare da Amal duk da Amal din ta girmeta da kusan shekaru Hudu ko a makaranta ma ta girmeta a aji

Ranar da Mai Kano ya shigo katsina tsohon gidan su ya Fara zarcewa ya binciko kwalin wayar Halima sai da kyar kafin yayi nasarar samoshi ya wuto gidan hajiya inda take fada mishi har yanzu babu wani Labari akan Halima Amma Alh Aminu Yana Bakin kokarin shi.

Wani takaici ya turnike shi don har ga Allah tun Ranar da Alh Aminu ya zamo damuwar mahaifiyar su yaji ya tsani mutumin yanzu ma zuciyar shi na darsa mishi zargin mutumin shine dalilin da zai Kai kwalin wayar don ayi mishi tracking din wayar don har yau layin akashe yake baya samuwa.

Agurguje yayiwa hajiyar sallama ya wuce Bai ko tambayi su Husna ba don yayi zaton ko suna makaranta.

Isar shi Legos ya kaiwa magdo kwalin wayar inda ya shigar da wasu lambobi a computer Yana turawa har ya wani Zane me taswirar map ya bayyana ya Kuma SHIGA yiwa Mai Kano bayanin katsina da wata unguwa dake Dab da fita garin katsina inda keda yawaitar ciyayi da dogon karfen service na network din layin sadarwa na 9 mober kwatance dai Mai kyau Mai Kano Kuma ya fahimta inda magdo din ya fito mishi da takarda me dauke da taswirar map din Wanda computer ta fitar ta hanyar print ya bashi shi kuma ya sallame shi ya taho.

Tunda ya tsinci labarin batan mahaifiyar shi komai ya tsaya mishi inda ya bar yaran shi Akan harkokin shi na kayan karafa don yanzu shima tsaye Yake da kafafun sa

Ya zubawa takardar me zanen map din ido yana mamakin abinda yakai wayar mahaifiyar shi wani yanki a garin nasu

Yayi tunanin sanar da yayun shi su Mubarak sai Kuma yaga Kar ya saka su a damuwa me yuwa su samu tazgaro a karatun su don Haka sai ya kyale su Yana me ADDU AR Allah yasa kafin su farga ma mahaifiyar tasu ta bayyana

Kwana biyu kawai ya sake bugo hanya ya nufo katsina inda Kai tsaye ya wuce unguwar da alkalamin map din Nan yake nunawa sai gashi a unguwar sardauna Estes cikin wani daji me yawan ciyayi

Ya Soma zaga unguwar Yana kallon tsilli tsillin gidajen da mafi yawa a Rufe suke sai yaji Ina ma ace gidan farko da Yake dab dashi Nan ne zaiyi nasarar gano mahaifiyar shi?

Tun Sha Biyun Rana Yake yawatawa a unguwar har karfe Hudu na yamma ya kasa barin wurin inda yakejin zuciyar shi na Kara kawatar wurin ko babu komai Yana Jin lallai mahaifiyar shi na cikin yanki

Har Rana ta kusa faduwa baiji Yana son barin wurin ba duk da gajiya da son yaje ya bada farali

Nauyin salloli da Yake son zuwa ya sauke ne kawai yasa ya hakura yayi nufin komawa gida kafin gobe ya dawo ya dasa daga inda ya aje.

Wata katuwar mota ta silalo tamkar gudun macijiya ita ta dauki hankalin shi ya Kuma bita da idanu tana silalawa cikin sa a ko Rashin sa a zance? Karab idon shi ya hango mishi Alh Aminu ne matukin motar Yana tafe Yana karba waya Yana Dariya…..

Wata Aradu da ta saukowa Mai Kano a ka ita ta faskarar dashi a tsaye Yana yiwa motar Rakiya da idanu.

“Alh Aminu a unguwar da Yake kyautata zaton mahaifiyar sa na ciki? Idan har Bai bace lissafin shi ba Hudu da hudu idan aka Tara su takwas zasu bayar. Idan har Bai manta ba Alh Aminu shine damuwar mahaifiyar shi to ga misalin magdo yayi daidai da ganin wata Alama da zata alamta biyar da biyar goma kenan !

Sai kawai yaji kafafunshi sun bi bayan motar a sukwane zuwa wani gida dake lullube da furanni.

Lokacin da ya karaso kofar gidan tuni har me gadi ya bude kofar gate din motar ta silala Yana karasowa Kuma ana mayar da gate din ana Rufewa.

Nima kuma fa da na hada biyar da biyar goma suke Shirin Bani.

<< Hawaye 18Hawaye 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×