Mai Kano ya Soma dukan kyauren da karfi tamkar zai jijjige shi. A yadda yake ji matukar ba a bude ba ko ta sama sai ya haura.
Dukan da yakeyi kamar zai balle kofar ne yasa me gadin budewa a fusace Yana zare idanu da son ya keta Mai bugawa
Ya dubi Mai Kano. "Uban waye anan? Ya dubi me Kano Yana muzurai
"Wa kake nema ne? "Me gidan nake nema. "Baya Nan sai kaje sai ya dawo. Ya fada Yana kokarin maida kyauren ya Rufe inda me kanon yayi saurin tare shi ta hanyar tura gate din Yana kokarin. . .