Skip to content
Part 20 of 48 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Mai Kano ya Soma dukan kyauren da karfi tamkar zai jijjige shi. A yadda yake ji matukar ba a bude ba ko ta sama sai ya haura.

Dukan da yakeyi kamar zai balle kofar ne yasa me gadin budewa a fusace Yana zare idanu da son ya keta Mai bugawa

Ya dubi Mai Kano. “Uban waye anan? Ya dubi me Kano Yana muzurai

“Wa kake nema ne? “Me gidan nake nema. “Baya Nan sai kaje sai ya dawo. Ya fada Yana kokarin maida kyauren ya Rufe inda me kanon yayi saurin tare shi ta hanyar tura gate din Yana kokarin shiga cikin gidan inda me gadin ya fusata ya nemi daka Mai Kano.

“Kai Wai ubanwa ya daure ma kunkuru nake fada kana fada? “Wani Dan iska ne Wanda ya fiku tashanci Kai da uban da ya ajeka a Bakin kofa kana mishi gadi.

Ya kutsa kanshi da karfin tsiya ya shiga inda me gadin ya nemi cakumo shi inda shima Mai Kano ya fusata ya damki makoshin shi ya Rike yaki saki. Ya Raina Mai kanon Amma Bai zaci karfin shi ya Kai Haka ba.
Da dai ya Gane in baiyi sannu ba Mai Kano zai kashe shi don Bai Rike shi don ya saki ba don haka ya yi ta kwara Kara Yana neman agaji da sauri Alh Aminu ya fito Yana mamakin ganin Mai Kano Yana Rike da makoshin me gadin.

Da kyar ya kwaci me gadin Yana maida numfashi. Mai Kano ya dubi Alh Aminu fuska murtuk
“Ka fada mishi Kar ya Kuma SHIGA harka ta ba wurin shi nazo ba kaima da nazo wurin ka ba maula nazo ba.

“Yi hakuri Bai San ka bane. Ya fada Yana kamo hannun shi suka SHIGA cikin falon da Yake karbar Baki. Ya zauna Yana cin magani. Alhaji Aminu ya kawo mishi Ruwa Yana Zama don su gaisa Amma Mai Kano ya dauke kanshi bare ya gaishe shi.

“Daga Ina kake ne Mai Kano? Ya tambaye shi cikin dukan kirji. “Nan nazo karbar wayar mama ta ne ita kadai nazo amsa.

“Wace waya Kuma Mai Kano? Ya tambaya Yana Nuna kamar Bai San abinda ke Nan ba Amma a zahiri a Rikice yake

“Haba Baba da hausa fa nake maganar Nan wayar kawai nake so ka Fara bani kafin na dawo naji inda Zan sameta.

“Kana shaye shaye ne Mai Kano? Ya zaka Zo ka saka Ni Gaba kana tuhuma ta? Wace waya ce kake magana akai?

Ya Mike tsaye Yana kallon shi tamkar ya shake shi. “Idan ba zaka bani wayar ba ka bani kayin.

“Kaga zauna Mai kano muyi magana ka Gane? Ya zauna Yana hararar shi.

“Ka Gane ko? Na samu labarin batan mahaifiyar ku Halima Ina Nan ina kokarin ganin yadda Za ayi “Kana kokai? Ya tambaya Yana kallon shi. “Kwarai kuwa Kuma in Sha Allah zata bayyana.

“Ni nafi bukatar wayar Baba ita Kuma in na tashi neman ta ai nasan inda Zan nemeta..

Ya Mike da Shirin ficewa inda Alh Aminu ya bishi da kallo..

“Zan samu layin ko kuwa sai kayi shawara? Ni fa ban San abinda kake magana akai ba Mai Kano..

“To Bari na tafi idan na dawo zanyi maka bayanin abinda nake nufi. Ya fice Yana leken gidan da fatan hango wani Abu da ya danganci mahaifiyar shi Halima Amma Bai ga komai Dole ya fice inda ya wurgawa me gadin wani mugun kallo inda Me gadin yayi mishi kallon sauka lafiya

Fitar me kanon ya bawa Alh Aminu damar Kiran lauje

“Uban Yan sharri Daya daga cikin yaran matar Nan ya na neman Ballo min Ruwa Dole kayi min maganin yaron Nan Wallahi yazo min Yana neman wayar uwar sa ta Ina ya San wayar tana wuri na?

To gani Nan Zuwa don Wallahi ya kada min ganye kadan ya rage ya zurma Ni . Ya Mike Yana leka dakin da Halima take ya hango ta kwance tana bacci baccin da ake sakar Mata in za ayi Mata Masha ar

Ya karasa gareta Yana shafa fuskar ta kafin ya kashe fitilar dakin.

<< Hawaye 19Hawaye 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×