Skip to content
Part 24 of 48 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Napep ya direshi a unguwar sardauna Estes ya sallami mai napep din ya kewaya bayan gidan Alhaji Aminu fetal Babu yawaitar mutane ya fito da igiya Yana warware wa Yana daure wani Danko a take ya zuba mishi fetur ya Cinna mishi wuta ya Kuma jefa a wayoyin wutar lantarki dake sada wutar zuwa gidan a take wayoyin suka dauki wutar gashi Kuma akwai wutar nepa.

Galan din da sauran fetur din ma Yake ciki sai ya cillashi saman Rufin kwanon gidan inda wuta Kuma ta tashi ganga ganga.

Yana gefe Yana kallon yadda Rufin kwanon ya ke cin wuta

Kan kace me? Gidan ya dauki wuta sai turirin hayaki ke tashi. Me gadin ya an Kare da hayakin da ke fita ya Soma neman taimako ta hanyar kwarara ihu. Mai Kano ya kewayo har ya shige gidan ba tare da ya sani ba
Kai tsaye ya tausa kanshi cikin gidan inda ya Soma laluben dakunan gidan.

Halima dake kwance tana bacci tamkar gawa Rufin dakin ta da yafi cin wutar har ya Soma zaftarowa cikin dakin inda wani yanki ya fado mata a kafarta ta farka a firgice.

Ta Mike tana nufar kofar fita inda sukayi kicibus da Mai Kano Wanda yayi Ram da hannunta ya yo waje da ita suka fice yayin gidan ya Soma daukar mutane masu kawo dauki.

Mai Kano ya tsayar da napep suka SHIGA ya ce a wuce dasu Tasha inda suka SHIGA motar Legos

Alh Aminu yana gaban lauje Yana fada mishi yadda sukayi da Mai Kano

“Lauje yaron Nan ya Zama Dole jinin shi ya zamo Madara ga Zubaina da dodon kod’i.

“Dama ai na fada maka shine karfen kafar ka kamar yadda ka zamowa uwar shi.

“Ya fada min ya San komai kuma ba wayar ta kadai yake tuhuma ba har da inda Uwar shi take

Karshe ma yace hukuma zai sako idan ban fito mishi da Uwar sa ba.

“Mutumina Ashe baka Gane abinda nake nufi da karfen kafa ba? Wancan yaron duk yadda ka dauke shi ya wuce Nan. Bana zaton zaka iya dashi don Ina me tabbatar maka da tsaye Yake Bai jingina da komai ba Kuma zuciyar shi bata da tsoro bare ya firgita.

“Zanci uban shi kuwa don yadda nayi nasara Akan Uwar shi da uban shi shi din banza ?

“Baka fahimci karfen kafar da nake nufi ba Aminu har yanzu? Ina nufin shine Wanda zai gano abinda ka shukawa iyayen shi ya kake zaton zaku Kare da shi? Jinin shi yafi naka karfi. Yafi ka naci Akan fada. Ya fika Rigima komai ya wuce ka shine nake mamakin yadda akayi baka fahimci hakan ba.

“Kira min Zubaina in Bata Dan iska tun kafin ya jawo min aiki. A take lauje ya hada garwashi ya tada hayaki kafin Zubaina ta bayyana a yau Kuma da kuka ta bayyana Mai makon dariya da ta saba bayyana tanayi.

Lauje ya tare ta da tambaya. “Me Kuma ya faru kike kuka gimbiyar dodon kod’i?

“Mutumin Nan baiji kashedin da kayi mishi bane na bama son ya hada jini da iyalan wancan mutumin da muka Sha jinin shi?.

Lauje ya dubi Alh Aminu da kallon tambayar me ya faru? Lauje ya dubi kusurwar dakin inda muryar Zubaina ke fita Alamar ta Nan ta bayyana

“Me ya faru ne gimbiya?

“Matar da ya Kai gidan shi ai matar Wanda muka Sha jinin shi ce Kuma a yanzu tana da shigar ciki Dole sai ya hada jini da sune ? Lauye ya dubi Alh Aminu da kallon ka ballo Ruwa.

Zubaina taci gaba da Rera kuka tana fadin ba zasu yarda ba sai sun dauki fansa.

“Yanzu kije yaron can Mai Kano ki tabbatar Bai Kara kwana Duniya ba.

“Kana son na mutu ne kake hada Ni dashi? Shi wanene? Lauje ya tambaya

“Shi Mai kanon Mana. Lauje ya Kuma duban Alh Aminu Yana mishi kallon kaji abinda na fada maka?
Yanzu me zaku iya yi mishi ku Raba Ni dashi?.

“Ina fada maka yafi karfin mu kana cewa muyi wani Abu kana son mu mutu ne? Yafi karfin mu bama zamu kusance shi ba mu bar maganar shi ma yanzu dai indai kana nema Mana zaman lafiya kana Kuma nemawa kanka zaman lafiya ka je ka dauki matar can a zubar da cikin can ba Kar a Bari ya Kara kwana ajikin ta don in ya Kai gobe mun SHIGA UKU mun lalace.

“Za ayi hakan gimbiya Allah ya huci zuciyar ku. Ta Rikide ta koma hayaki ta fice tana jaddada fadin lallai lallai Kar cikin Halima ya wuce gobe in ya wuce gobe akwai wutar da zata tashi in Kuma ta tashi su duka zasu kone har Alh Aminu.

Zufa ta karyowa Alh Aminu cikin dukan kirji ya ke fadin. Lauje Dole kayi wani Abu Akan yaron can Wallahi…

Kafin lauje yace wani Abu wayar Alh Aminu ta dauki tsuwwa ya zaro ta Yana dubawa inda yaga sunan me gadin gidan shi inda ya dauka yake tambayar

“Me Kuma akayi ne goloko?

“Mai gida wuta ce ta Kama a gidan komai ya kone.

Ya Mike da sauri Yana dura Ashar tare da katse Kiran.

Lauje ya dubeshi Yana fadin “Me Kuma ya faru?

“Wai gida na ne wuta ta tashi.

<< Hawaye 23Hawaye 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×