Skip to content
Part 3 of 54 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Katafaren falon ya lashe duk wata kawar da duniya ke yayi tamkar fadar shugaban kasa. Haske tarwai ya haske ko’ina wanda ba za ka banbance Dare ko Rana ba. Sai dai wani abun haushe wani boyayyen gida ne da ba kowa yasan dashi ba koma ace gidane da ba gaskiya tasa aka kera shi ba. Babu kowa acikin sa sai shi kadai Maigidan sai kuma wani katon Maigadi. Yana zaune a falon Yana waya wadda muryar ke fita ta cikin wayar tamkar a gaban shi yake. Wani mutum ne Mai kyawun sura Amma ta fuskar hali da dabia baiyi dacen samun ko daya da za a daga a duba ba. Amma fa kyakkyawa ne na karshe. Shekarun shi arba in da biyu kanshi me dauke da suma irin ta fulani bakakirin sai saje wanda ya kara fito da kyawun shi. Irin mijin nan da kowace mace ke burin mallaka musamman ma da ya hada kyalli biyun da matan ke kulafuci a wannan makauniyar duniyar wato kyau da kudi.

Muryar shi a zafafe yake magana.

“Lauje na dai gabatar da fyaden nan da Zubaina ta zaba min, sai dai duk rashin imani na lauje na tausayawa yarinyar ka fadawa Zubaina kar ta kuma bani umarnin sake yiwa wata yarinya fyade gara tace jini take so Zan fi bata hadin kai gaskiya don na kwana ina mafarkin yarinyar nan…

Daga cikin wayar wanda aka kira lauje ya gaggabe da wata mahaukaciyar Dariya. “Kamar kuwa ka duba ka gani ko dai Zubaina ta fara magana da kai kai tsaye ne?

“Ban Gane ba? Wani abu kuma Zubainar take so yanzu? “Kwarai kuwa, jinin mutum take so ka kawo mata na wani makusancin ka . Ya Mike a rikice hannunshi na yamutsa sumar kanshi Alamar damuwa da wannan Rikicin

“Wa Kuma take so na kawo Mata ? In dai ba matata ko yaranan biyu take so ba ko waye Zan Bata Zan kawo Mata in dai ba wasila bace itace Rayuwa ta . In dai Kuma ba yarana muhsin da Amal bane ko waye Zan kawo maka shi lauje ka Bata jinin shi Ni Kuma ta bani abinda nake so wato DUNIYA…

Ya yi saurin katse wayar saboda shigowar mai gadin ya dubeshi.

“Ya aka yi ne Buhari? “Bakone yazo yana neman ka kuma yace kunyi zaku hadu shine dalilin da ban dakashi ba…

“Babu wani bako da muka yi dashi zamu hadu amma ka tabbatar shi kadai ne kuma ka cajeshi sosai in dai babu komai tare dashi ka barshi ya shigo.

Mai gadin ya dawo ya samu Bello inda ya barshi ya soma lalube shi har dai ya tabbatar babu komai a tare dashi kafin yayi mishi jagora har falon Alhaji Aminu

Alhaji Aminu ya bashi hannu suka gaisa Yana kallon shi inda ya gane kowaye, mutumin nan ne da ya gani ranar da ya mayar da yarinyar da yayiwa fyade a take ya gane ubanta ne don kamar tasu bata boyu ba…

“Ban gane ka ba Malam kuma kace munyi da kai zamu hadu?

“Hakane. Sati Hudu da ya wuce na nemi ya’ ta na rasa kafin naga motar can GMT ta kawo min yarinyar cikin wani hali ta zubar shine na biyo bayan ta na kuma ga nan gidan tazo. Shine nazo naji wanda ke da wannan Aikin…

“To yanzu kenan Ni kake tuhuma da wannan laifin kenan? “Kwarai kuwa don kuwa kallo daya da nayiwa fuskar ka yasa na yarda da hakan don inda bani da tabbacin kai din ne ai ba zan tunkare ka da wannan maganar Kai tsaye ba.

Alhaji Aminu ya nufi wata kofa ya Shiga mintina kadan ya fito da rafofin kudi na Yan Naira Dubu dubu ya zube agaban shi .

“Dauki wannan ka tafi malam idan kuma abinda aka yiwa yarka kake so na siya na biyaka duk na shirya. Ya koma dakin nan da ya shiga ya sake fitowa da wasu kudin wanda suka fi na farko yawa ya sake zube mishi a gaban shi.

“Gashi Nan dauki ka tafi. Bello ya dubi kudin irin duban da ake wa Kashi ko wani abun kyankyami

“Bana bukatar kudin ka Alhaji, Kuma kamar yadda ka fahimci cewa abinda aka yiwa ya ta nake so a biyani .

Tabbas hakane Anna ba kudi nake so ba hukunci nake so a yiwa irin ku don kuwa ta silar abinda kayiwa ya ta ta rasa Ranta. Mutuwar ta kuma yasa mahaifiyar ta kuma ta hadiye zuciyar ta ta mutu don haka Wallahi ba zan bar jinin Safiyya ya tafi wofi ba don haka ka saurari kira daga kotu.

Ya Mike Yana Shirin ficewa. “Ji Nan bawan Allah, Ya fada Yana dafa kafadar shi. Ya juyo idonshi jajir Yana kallon shi

“Ka dauki kudin Nan ka tafi bakin ka alaikum. Kana zaton Kai ka yi isar da zaka tsaya takara ko wurin kwatar yanci da ni? To Bari kaji duk wani Alkali dake garin Nan nawane ka dauki kudin Nan ka tafi ko sa fidda ka daga fatara ko tsiyar da kake ciki in Kuma kaki to jeka inga Alkalin da zai kwatar maka yanci a garin Nan.

“In Sha Allah in dai gaskiya itace gaba da karya zaka karyata kanka. Idan karya zata shekara karya to wallahi gaskiya tana makwafinta…

“Hahahaha Alhaji Aminu ya gaggabe mishi da Dariya . To jeka ina jiranka. Da sauri kuwa ya fice inda Alhaji Aminu ya biyo bayan shi Yana fadawa Buhari idan mutumin Nan ya dawo ya barshi ya shigo kanshi tsaye idan Kuma baya Nan ko Yana gidan iyalanshi a kirashi.

<< Hawaye 2Hawaye 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×