Skip to content
Part 30 of 50 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Husna taji saukar maganar haj wasila tamkar saukar Aradu da sauri ta dubi haj wasila da son tabbatar wa inda haj wasila ta wurga Mata harara don ita kanta ba son Auren muhsin da Safina ta ke ba sai don ganin yadda yake neman shigewa yarinyar can Husna abinda take Jin har muddin Rayuwa ba zata taba yarda ba duk Matan Duniya ya Rasa matar Aure sai diyar Halima ita ko Karen hauka ya cijeta da zata Bari ya dauko Mata ahalin Halima?

Ta kuwa ci gaba da zazzaga masifa tana fadin Auren Safina ya Zama Dole don ba zata yarda ya dauko Mata kwai Tara tsinana ba.

Alh Aminu ya Mike Yana fadin. “To ai gaki ga shi Nan ku gyarota duk yadda kukayi yayi dai dai

Ya wuce ya barsu Nan tana zuba mishi masifa Wai ai yasan shi Safina take jira Taki kowa saboda shi shine zaice baya sonta to kada Allah yasa ya sota idan ta shigo gidan shi zai so ta.

“Ni fa mami ban taba cewa Ina son ta ba ita ce ke haukan ta Kuma duk Baki da labarin mazan da tayi tarayya dasu? To Ni nasan ko wacece ita don Haka Mami abar maganar Nan Ni dai bana son ta.

“Zaka so ta ne Amma Wallahi kayi karya ka bani kunya tunda uban ka ya daure maka kugu Ni kubar Ni ku gani idan akwai abinda zai garareni tashi kaje abinka tun ban sharara maka Mari ba. Ya Mike ya barta da kumfar Baki.

Husna ta shige daki tana fasa kuka yau da me zataji Yaya muhsin da Auren Safina?

Amal ta dubeta tana kuka tamkar wadda akayiwa mutuwa.

“Me ya faru Husna? Sai ta kukan ta take inda Amal ta SHIGA Rarrashi har tayi shiru ta Kuma fada Mata abinda tajiyo mamin na fada Akan Auren Yaya muhsin da Safina.

“Kar wannan ya dameki Ni na San Yaya muhsin ba son Safina Yake ba ba kuma zai taba Auren ta don Haka zuba idanu kawai kiyi kallo.

“Har fa mami tace ita zatayi komai da kanta Anya Anty Amal Mami ba ta gano muna soyayya da Yaya muhsin ba?

“Ta gano Mana . Waye zai dube ku ya kasa fassara irin abinda ke zukatan ku musamman ma ke da son Yaya muhsin ya fito har ta cikin idanun ki?.

“Ni yanzu yaya zanyi Anty? “Ki Roki Allah ya yayi Miki zabin abinda Yake shine ALHERI ko ba Haka Kika fada min ba Nima? Ina me tabbatar Miki Husna yadda nake son Gayen can Wallahi Baki kamo ko kwata ta ba a soyayyar da nake mishi Kuma Kika nuna min abinda na yarda shine gaskiya wato barwa Allah komai .

Husna ta share HAWAYE tana fadin “Gaskiya Anty indai da gaske Mami take wallahi Zan koma gidan hajiya ne kawai don bana Jin Zan iya hakurin Rasa Yaya muhsin son shi Bai Kama Ni don ya saki ba.

Karab sai a kunnen muhsin da ya biyo bayan Husna saboda yaga irin dukan da maganar mamin ta haifar Mata. Ya sunkuya dai dai fuskar ta Yana zuba Mata ido

“Husna Nima son ki Bai kamani don ya saki ba. Husna Rasa ki Yana nufin Rasa Rayuwa. Kar ki damu da abinda Mami ta fada ko da ta Auro Safina to ina me tabbatar Miki da kanta ta Auro wa ba Ni idan Ni za ayiwa Aure to a Aura min ke aga farin ciki na Baki da kishiya a zuciya ta ba Kuma zanyi Miki ita ba.

Kadan ya Hana dadin maganar shi ya sumar da Husna ta Rufe fuskar ta don kunya.

HAWAYE ya biyo idon Amal tana fadin. “Allah yadda ka hada zukatan bayin nan naka Nima ka hada namu zukatan da bawan da ka jarabeni Akan shi.

Muhsin ya juyo Yana hararar Amal. “Kice Allah ya Kama alhakin mu da Kika dauka? Ta zabga tagumi ba ta tanka shi ba.

“Allah kema ya duba ki Anty. Cewar Husna.

Ta amsa da Ameen ya Rabb

Lauje ya Kira Alh Aminu Yana tambayar shi Wai ya kuwa cikka sharadin Zubaina?

“Wallahi lauye wani tarnaki ne na zuwan Mai Kano ya dauke hankali na Amma yau din Nan Zan cika shi Amma maganar sallar da tace na Daina tuni na Bari shima fyaden da za ayiwa makauniyar yanzu Zan sa a Nemo min ita duk inda za a samota.

“To kayi hanzari don Zubaina tace min bakayi ba Kar ka Bari ku Kuma samun sabani da ita don karon ba zaiyi maka kyau ba.

Suns gama wayar ya Kira zarto Yana fada mishi makauniya Yake so ya samo mishi.

Zarto ya sheke da Dariya Yana Fadin. “Kayan ka ya tsinke gindin kaba Alh indai makauniya kake so ina da ita a hannu.

“Kamar Yaya kana da ita a hannu? Ya tambayi zarton

“Ai Alh akwai kishiyar babata da Bakin kishin ta yasa ta yi mahaifiyata Asiri har ta bar gidan Duniya daga karshe mugun abunta ya dawo Mata har ta makance yanzu Haka Bata gani Kuma ko da ba zaka biya Ni ba na Rantse maka da kabarin uwa ta sai na kawo maka ita Koda zaka yanke shegiya kasha jininta Dama Ina neman hanyar da Zan kunzuga mata bakin ciki kamar yadda tayi min na Rasa mahaifiyata Mai kauna ta.

“Baka da mutunci fa zarton matar baban naka.

“Akan matar Nan ko ina da mutunci Yasin Zan zubar da shege in koyi yadda ake ta addancin don Haka shirya kawai Alhaji yanzun Nan Zan kawo maka ita kayi yadda kake so da ita.

Allah kayi Mana sutura kalubalen ku masu nuna wa Ya’yan kishiya bakin hali baku San yadda gobe zata Zo ba gadai zarto can zai kawo kishiyar Babar shi ko Yaya take karewa?

<< Hawaye 29Hawaye 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×